KUNYA ADON MACE 81~85

*KUNYA ADON MACE*

*_Feedoh yanmata_*✍🏻

*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*
   ® *(NWA)*

*_page_*8⃣1⃣ *_to_*8⃣5⃣

Yana fitowa ya ci karo da ita duk'e, duk'awa yayi yace lil sis garin ya akayi haka? Itadai ta kasa cewa komai sai kuka takeyi, d'agota yayi yace haba baby doll miye na kuka daga kawai tsotsai ya sa kin yarda tray d'in pls stop cry, hawayen ya shiga share mata "hannunta ya kama yayi cikin d'akinshi da ita, zaunar da ita yayi shima ya zauna gefenta, yace baby doll miye kike kuka kinsan bansan kukanki oya share hawayenki zanyi surprising d'inki, hawayen da suka gangaro mata ta share amma zuciyanta bai daina bugawa ba, "kallon ta yayi yace aysaah namaki laifi amma ni a wurina ba laifi bane ba kawai inasan nayi surprising d'inki ne, itadai bata ce komai ba... Sunan ta ya kira aysaah d'agowa tayi ta kalleshi, "salman yace yau zan gabatar maki da wadda zan aura a razane ta d'ago, d'aga kanshi yayi yace nasan abun zai baki mamaki amma ba abun mamaki baneba, "lokacin da naje kd Allah ya had'ani da wata yarinya mai suna sahr......kwashe komai yayi ya gayama aysaah babu abinda ya b'oye mata, "in banda zufa babu abinda aysaah keyi amma shi baima lura ba, waya ya jawo zaikira sahr murya dashe tace ya salman banjin dad'i yanzu bari wani tym d'in mun gaisa, d'aga mata kai yayi alamar toh da sauri ta bar d'akin duhu ta fara gani gabanta a haka tabi bango har takai d'akinta, tana shiga ta maida k'ofa ta rufe tafara rera kuka kamar *rookiey kaxs idan taja fad'a jiddah ja'o tak'i tare mata kuma taci duka*😂
             **********
"Waya ta jawo tayi dialing number bestie naga an rubuta ringing biyu aka d'aga muryan aysaah ko fita batayi sosai tace hello bestie pls kizo yanzu gida ina san ganinki, bataji amsar da zata bata ba ta kashe wayanta.

    "Mintuna k'alilan taji knocking k'ofanta tashi ta bud'e haneefa ce ta shigo d'akin da sallama, amsa mata tayi "binta haneefa tayi da kallon tambaya hannun haneefa ta ja sukaje bisa gado suka zauna, shiru sukayi can haneefa tace bestie kin kirani kin k'iceman komai sai faman kuka kikeyi, "cikin sheshek'an kuka tace bestie na rasa ya salman *kunya ta sa na rasa masoyi na* haneefa tace nifa bangane kan magananki ba gara kiman bayani, salman yana da wadda yakeso sunanta sahr yanzu haka maganan aure sukeyi da ita "in banda innalillah wa'inna ilaihir raji'un babu abinda haneefa ke fad'a, aysaah ya akayi haka wakuma ya gaya maki ko shine ya fad'a maki? Tace yau naje kaima shi  abinci naji yana waya har kayana abincin suka zube, infact yaman bayanin komai da kanshi kuma ya tabbatar man da irin sanda yake mata, ita kanta haneefa kuka takeyi saboda ita kad'ai tasan irin sanda aysaah takema salman, "bestie ina cikin hali ga shi papa yaban 3month after exams d'inmu da 2weeks idan ban fitar da miji ba zai bani yaron abokinshi bestie ki taimakeni ya zanyi su duka kuka suke sosai.....

Kuka sukai mai isarsu kana haneefa ta share ma aysaah hawaye tace bestie kidaina kuka yanzu ba time d'in kuka baneba adua ita zaki cigaba dayi saboda babu abinda zai gagari Allah dan haka stop cry nd keep praying kuma kidaina cewa " *kunya ta cuceki ta rabaki da masoyinki kefa da kanki kika nunaman darajan kunya ga d'iya mace saboda tabbas kunya ita ce adon mace* kuma tunda kika rik'e kunyarki in shaa Allah zakiga ribanta nan gaba, amma ina da shawara bansani ba ko zaki karb'eta aysaah tace inajinki, zama ta gyara tace why not ki fidda asad a matsayin mijinki dan nasan tabbas haryanzu yana sanki, "bazan iyaba saboda idan namashi haka banmashi adalci ba lokacin da ya soni na k'ishi sai yanzu da na rasa mafita zan dawo mashi Allah ban mashi adalci ba saikuma ta fashe da kuka, da kyar haneefa ta samu tayi shiru...

"Haneefa tace a yanda na karanto sonki cikin idon asad ko aure kikayi kika fito zai aure ki bare kuma ya san komai dake faruwa kedai idan kina sanshi kimashi magana, shikuma salman kisa a ranki dama ba mijinki bane ba, kicigaba da d'aukanshi a matsayin wanda kuka fito ciki d'aya kamar yanda yake d'aukanki, itadai in banda kuka ba abinda takeyi da kyar haneefa ta samu tayi shiru ta dinga bata magana hartasamu ta d'an ci abinci, sai marece  haneefa ta wuce gida........


Phirdauceejeebo.blogspot.com


*IG:yar_ficika*

© *Feedoh Deedoh*✍🏻✍🏻

Comments

Popular posts from this blog

RASHIN GATA 176-180

RASHIN GATA 1-5

DIJAH 241~245