KUNYA ADON MACE 136~140

*KUNYA ADON MACE*


*_Feedoh yanmata_*✍🏻


*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*
  ® *(NWA)*


*_page_*1⃣3⃣6⃣ *_to_*1⃣4⃣0⃣

Ya salman a hankali ta kirashi kamar mai jin bacci, wani iri yaji "shima amsawa yayi a hankali kana yadawo ya zauna kusa da ita "shiru sukayi bamai ma wani magana....

Kallonta salman yayi yace yadai yanmata kin kirani kinkuma yi shiru?

Kanta k'asa tana wasa da yatsunta tace ya salman sahr fa?

Wani iri yaji dan yanzu baisan akira mashi sahr "daurewa yayi yace ta na nan...

Aysaah tace mu biyu zaka aura ne? Maganan dariya ta bashi dan yasan kishi ne ke damun aysaah...

Salman yace "eh" haka nake tunanin had'aku ku biyu da sauri ta d'ago saikuma taga ya tsareta da kallo k'asa tayi da kanta tana share hawaye...

Murmushi salman yayi ya d'ago fuskanta "ganin tana kuka ya b'ata rai yace miye na kuka? Ke abun kuka baimaki wuya ko?

"Share hawayenta tayi nida ita wazaka fara aura?

Tashi yayi tsaye yace aysaah zan fara aura "shiru tayi bata k'ara cewa komai ba har tsawon minti goma...

Takowa yayi yazo kusa da ita kallonta yayi yana murnushi yace kwantar da hankalinki my baby ke kad'ai zan aura in shaa Allah ke kad'aice gidan salman

D'agowa tayi tana murmushi har saida kumatunta suka lotsa "dariya yayi yace ashe dai yarinyar tana da kishi "pillow ta d'auko ta wurgo mashi ta shi yayi da gudu ya fita yana dariya...
                 ★★★★★★★★★
"Soyayya mai k'arfi ta shiga tsakanin salman da aysaah kullum a gida suna tare idan ammi ta ishesu da masifa sai sukoma suna waya "dan ammi tace salman ya b'ata mata d'iya da rashin kunya kullum suna mak'ale da juna...

An saka ranan auren aysaah da salman da tagama law school da 2weeks...

Salman da mummyn zarah sunso ayi bikin kafin ta gama amma ammi tace bata san wannan ba sai d'iyarta ta gama tunda saura 2month ta gama idan kuma bazasu iya jira ba ya nemi wata "kuji ammi da karfin hali tasan fa yanda aysaah ta mutu kan salman amma take haka dama yafasa muga yazatayi lolzz 😂😂 "dan dole mummynzarah ta lallashi salman suka hak'ura..

"Papa ne ya kira daddyn salman yace baya san komai daga gareshi zaima salman komai tunda dama salman d'anshi ne" daddyn salman yayi godia sosai...

Aysaah ce zaune gaban salman tana kuka shidai ya kasa lallashinta sai ido daya bita dashi "aysaah tace ya salman yanzu haka za'ayi bikina ya asad bai nan? Ya salman inasan ganin ya asad kafin bikinmu..

Hawaye ya share mata yace kinsan bansan ganinki kina kuka ko? "D'aga kanta tayi alamar eh" salman yace toh share hawayenki...

Kallonta yayi yace aysaah ina bakin k'ok'arina wajen gano asad amma haryanzu ba labari kiyi hak'uri mu cigaba da adua in shaa Allah asad zai bayyana ina ji ajikina...

"kwance take jikin ammi suna fira wayanta tafara ringin tana d'auka taga ansaka *final choice* kallon ammi tayi saitaga ammi ba
ita take kallo ba..

Tashi tayi zatabar d'akin ammi tace ina zaki aysaah tace ammi haneefa ce ke kirana a waya mayb ta zo ne...

Saida takai bakin k'ofa ammi tace haneefa ce final choice d'in "dariya tayi tabar d'akin da gudu..

Ita kanta ammin abun dariya yabata wai aysaah ce yau ke mata k'arya da haneefa "bayan tasan haneefa bestie aka mata seving...

parlon bak'i ta tardashi dayake dama can suke fira "sallama tayi, amsa mata yayi ya ware hannunshi da gudu ta k'arasa rungumeta yayi yace i miss u my babe
murya can k'asa tace miss u more my man...

kamo hannunta salman yayi suka zauna "kallonta yayi yace amarya bakya laifi dariya tayi tace bandai yi ba amma nayi mummynzarah aysai ta zaneni "dariya yayi sosai...

"Wani d'an akwati ya bud'e ya zaro wani zobe, hannunta ya kama ya saka mata shi ba k'aramin kyau ya mata ba "peck yama hannun kana ya saketa...

Kallonshi tayi tace tnx ya salman bata ida ba ya d'ora hannunshi bisa bakinta yace na hanaki yiman godia ko amma baki bari marairaicewa tayi tace na daina..

Fira sukeyi sosai "hannunta ta kalla taga 11:00pm kallonshi tayi tace ya salman dare yayi fa " a marairaice yace Allah bangaji da ganinki ba "murmushi tayi tace kayi hak'uri saura kwana kad'an na koma gdanka..

Salman yace nidai ban yarda ba. "peck ta mashi a kumatu ta tashi ta ruga tana dariya. Shim dariyan yayi yarasa miyasa komai na aysaah da ban yake da na sauran mata komai tayi burgeshi takeyi...



Phirdauceejeebo.blogspot.com


*IG: yar_ficika*



© *Feedoh Deedoh*✍🏻✍🏻

Comments

Popular posts from this blog

RASHIN GATA 176-180

RASHIN GATA 1-5

DIJAH 241~245