KUNYA ADON MACE 86~90

*KUNYA ADON MACE*

*_Feedoh yanmata_*✍🏻

*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*
    ® *(NWA)*

*_page_* 8⃣6⃣ *_to_*9⃣0⃣

Yinin ranan aysaah bata sauko k'asa ba itama kuma ammi bata nemeta ba dan gara ta barta ta huta, da zazzab'i mai zafi ta kwana da kyar ta iya tashi tayi sallan asuba inda tagama sallan nan tafara shek'a amai, "ammi ce zaune tayi ta gumi kamar a tsinkureta tashi tayi da sauri tayi hanyar d'akin aysaah tana murd'a k'ofan cikin ikon Allah taji ta bud'e shiga tayi d'akin tana sallama amma shiru, "can ta hangota k'asa cikin amai da sauri ammi ta isa wajenta duk'awa tayi tana kiran sunanta amma bata iya d'aga kanta, "sungumarta ammi tayi ta nufa toilet da ita wanke mata jikinta tayi tas kana ta nannad'ota cikin towel kamar wata k'araman yarinya bisa gado ta aje ta nemo doguwan riga ta saka mata saida ta gyara wurin tas kana ta kira papa a waya ta sanar mashi halin da aysaaah ke ciki....
            *********
Da sallama papa ya shigo mummynzarah na biye dashi, amsa masu ammi tayi shigowa sukayi ciki papa yace mike faruwa nan ammi ta kwashe komai ta gaya mashi, waya ya jawo ya kira salman, salman na d'auka papa yace my boy ka kira family doctor aysaah ba lafiya, amsawa salman yayi da toh ajiye waya papa yayi ya ja dogon numfashi, daga nan babu wanda ya k'ara cewa k'ala "salman ne ya shigo tare da doctor tashi papa yayi ya gaisa da doctor shikuma salman ya nufa bisa gado yana tambayan ammi mike damunta, kasa bashi amsa ammi tayi saboda hankalinta yana kan aysaah dake fidda numfashi kad'an kad'an "k'arasowa doctor yayi gaban gadon dubata yayi da yan gwaje gwaje kana ya d'aura mata k'arin ruwa magunguna ya rubuta, juyowa yayi ya kalli papa yace alh fever ne da headache ke damunta amma ga wannan magungunan a siyo in shaa Allah zataji sauk'i nan ba da dad'ewa ba tunda nasa mata k'arin ruwa, "amsan takardan salman yayi ya fita bankwana doctor yamasu papa kana yafita.....

"Salman ne ya dawo da magunguna hannunshi mik'ama ammi yayi ta amsa ta aje, ya juya zaifita takira sunanshi dawowa yayi ya zauna kallonshi tayi tace inasan magana dakai salman yace toh ammi, ammi tace dama ba wani abu bane ba illah kan matsalan aysaah...........nan ammi ta kwashe komai ta gaya mashi da lokacin da papa ya d'ibar ma aysaah kuma abinda nake zargi shine salman aysaah na san wani wanda inaga shi baisani ba kuma bata gaya mashi ba kuma naji dad'in da bata gaya mashi ba saboda *kunya itace adon mace* yanzu abinda nakeso dakai shine idan ta samu sauk'i ka lallab'eta ta gaya maka wa takeso saboda nasan kai zata iya gaya maka, nikuma idan harta fad'a wanda takeso in shaa Allah saina nemo matashi saboda farin cikin aysaah shine kwanciyan hankali na, numfasawa yayi yace in shaa Allah ammi zanyi yanda kikeso kodan na dawo da walwalar k'anwata da kuma ke a cikin gidannan, ammi tace tashi kaje nagode Allah yamaku albarka amsawa yayi da amin ya fita.....

"Masha Allah aysaah ta warware sarai saidai haryanzu ba walwala tare da ita gashi suna shirin fara exams dan monday zasu fara, salman yayi yayi ta fad'a mashi wanda takeso tace ba kowa da zaran ya matsa mata saita sa mashi kuka dole ammi tace ya kyaleta, kwatakwata walwala da wasan da ta sabayi da k'annenta ta daina kowa na gidan ya shiga k'unci idan ka fidda mummynzarah da bata damu da halin da aysaah ke ciki ba, "ammi ce zaune tana tambayan aysaah ta gaya mata damuwarta aysaah tace ammi karatun exams ne shiyasa kuka ganni haka da ammi ta matsa mata saita sama ammi kuka dandole ammi ta kyaleta.....

Tunda suka fara exams komi ya k'ara rikicema aysaah dan gani take kwanakin da papa ya bata matsowa sukeyi, hawaye suka gangaro mata hannu ta d'aga sama tace Allah ka kawoman mafita shikenan na rasa salman shima asad ina gab da rasashi, tashi tayi ta nufa d'akin ammi tana kuka zaunar da ita ammi tayi dan yanzu ta riga da ta saba da halin aysaah da anyi abu kad'an sai kuka, ammi tace yanzu kuma miyafaru aysaah cikin kuka tace ammi yau kusan sati kenan ina try number asad da yan gidansu tak'i shiga ammi yanzu ya zanyi naga  asad d'agota ammi tayi tace bangane mikike nufi ba? Kina nufin baki samu wayoyinsu d'aga kanta tayi alamar eh, waya ammi ta jawo ta dinga dialing numbers d'insu amma kowace kashe hardata maaah tagumi ammi tayi tace karki damu in shaa Allah lafiya kuma kina nan asad zaizo da kanshi aysaah tace ammi aybaisan mundawo sabon gidannan ba dan haka gobe idan nafita zanbiya tsohon gidan inba maigadi address d'innan duk idan yazo sai yabashi address d'in, ammi tace hakanma yayi daidai.......




Phirdauceejeebo.blogspot.com

*IG:yar_ficika*

© *Feedoh Deedoh*✍🏻✍🏻

Comments

Popular posts from this blog

RASHIN GATA 176-180

RASHIN GATA 1-5

DIJAH 241~245