KUNYA ADON MACE 131~135

*KUNYA ADON MACE*

*_Feedoh yanmata_*✍🏻

*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*
   ® *(NWA)*

*_page_* 1⃣3⃣1⃣ *_to_*1⃣3⃣5⃣

Tana shiga kitchen tafara had'a kayan break fast biebee ce ta taso da sauri tace uwar d'akina ke da kanki barshi nayi "murmushi aysaah tayi tace na hutar dake yau barshi zanyi komai kedai duk abinda na b'ata ki wanke kinji ko? Da sauri biebee tace toh uwar d'akina. Kafin kace wani abu gida ya d'auki k'amshin abincin aysaah..

" ```9:00am``` tagama komai jerasu tayi a daining table kana ta nufa d'akinta dantayi wanka, tana shiga taga haneefa na barci d'aka mata duka tayi a firgice haneefa ta tashi tana waige waige....

"Ganin aysaah na dariya abun ya k'uleta, tasowa tayi da sauri aysaah naganin ta taso ta fad'a toilet tanama haneefa dariyan mugunta.....

```10:00am```
K'arfe goma aysaah da haneefa suka sauko cikin shirinsu tsaf suna tafe suna fira duk wanda yaga yan matannan sai sun burgeshi saboda Allah yamasu kwarjini....

"a daining suka iske su ammi, da gudu aysaah taje ta fad'a kan ammi d'agota ammi tayi tace my babe kinyi kyau peck aysaah ta mata tace tnx ammi, "zo nan ammi tacema haneefa da sauri ta isa wajenta had'asu tayi ta rungume...

Saida suka gaida kowa kana suka faracin abinci "tunda suka zauna salman ke kallon aysaah itama shi take kallo tana murmushi, "babu wanda ya lura dasu sai ammi, "kallonta ammi tayi tace zakici abinci kokuma zaki tsaya shirme sunne kai tayi tana dariya...

Saida suka gama cin abinci papa yace gaskia biebee ta iya abinci a shagwab'ance aysaah tace papa nifa ce nayi ba biebee ba kasanfa biebee bata iya abinci mai dad'i ba, "dariya papa yayi yace ashe d'iyar ammi ce tayi "jawota ammi tayi jikinta tace kyalesu my babe sun san ke kikayi santi ne sukeyi...

"Kallon salman papa yayi yace my boy inasan magana dakai, "a natse salman yace "toh papa...

Gyaran murya papa yayi yace salman ka girma kuma kaga k'arfina yana k'ara k'arewa yakamata ka aje iyalai saboda ragamata hannunka zata koma "kuma nan gaba kai zaka d'auki nauyi na dana iyayenka dana k'annenka "dan haka na baka yan kwanaki ka fito da matar da kakeso ko wacece nikuma zan nema maka auren ta.....

"Tunda aka fara maganan kan salman k'asa yake ita kuma aysaah sai wasa take da yan yatsu...

D'agowa salman yayi yace papa dama ina da wadda nakeso kuma ammi ta santa...

Hararan shi ammi tayi tace ina nasanta idan kana mashi bayani kamashi...

"Salman yace papa dama ba wata nakeso ba illa aysaah "da sauri aysaah ta tashi ta bar wurin tana dariya...

"Da murna papa yace alhamdulillah magana ta k'are salman na baka aysaah duniya da lahira "ammi tace oh hukunci za'ayiman da d'iyata? "Dariya papa yayi yace ohh afuwan ammi nayi shishigi fa...

Mummynzarah tace ammi gamu da k'ok'on baranmu a taimaka abamu auren aysaah...

Ammi tace zanbaku amma wit one condition kada ku dinga matsama d'iyata "gabana ma kuna matsa mata bare na kaimaku ita yanzu "dariya mummynzarah tayi tace zamu kiyaye "kallon salman ammi tayi tace kaje ka nemi so wajen aysaah...

Salman yace ammi ay mun daidaita kanmu "papa yace shikenan Allah yasama abun albarka amsawa sukayi da amin "papa ya sallami salman "tashi salman yayi ya nufa d'akin aysaahhh....
                 ★★★★★★★★★
"Da sallama salman ya shiga d'akin aysaah amsawa tayi ta mashi izinin shiga...

Yana shigowa d'akin ya tarda aysaah zaune "duk'awa yayi ya kamo hannun aysaah yace haba my wife shine kika gudo?

Dariya tayi tace toh ya salman ya za'ayi na zauna dariya yayi ya lakuci hancinta "d'agowa tayi ta kalleshi tace ya kukayi da papa?

D'aure fuska yayi yace amminki ta hana "marairaice fuska tayi tace miyasa ammi zatayi hana? K'ara d'aure fuska yayi yace oho ki tambayeta...

Sanda kanta tayi k'asa tana hawaye d'ago ta yayi ya goge mata hawaye yace miye na saurin kuka kuma? Toh wasa fa nake maki "da sauri ta d'ago "yace eh kai mashi duka tayi, ta shi yayi yana dariya ya bar d'akin....

Phirdauceejeebo.blogspot.com

*IG: yar_ficika*


© *Feedoh Deedoh*✍🏻✍🏻

Comments

Popular posts from this blog

RASHIN GATA 176-180

RASHIN GATA 1-5

DIJAH 241~245