KUNYA ADON MACE 161~165

*KUNYA ADON MACE*


*_Feedoh yanmata_*✍🏻



*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*
® *(NWA)*

*_page_*1⃣6⃣1⃣ *_to_*1⃣6⃣5⃣

*BAYAN WATA UKU*
Kwanciyan hankali da zaman lafiya ke tsakani salman da aysaahhh...

kullum cikin tattalin junansu suke, kowa burinshi ya kyauta tama d'an uwanshi..

Duk wanda ya ga aysaah saita burgeshi saboda irin kyan da tayi ga fari saikace ka tab'a jini ya fito....

Zaune take k'asan kafet tana gyarama salman k'umba. Kallonta yayi yace preety kinsan miyafaru jiya danaje kd?

Girgiza kai tayi, tace sai ka fad'a...

Salman yace wai mummyn mufeedah ke cewa cikinki yakai wata biyu yanzu? Kallonshi aysaah tayi tace mikace mata to?

Salman yace cewa nayi baki da ciki..

Girgiza kai tayi tace Allah ya salman inasan naganni da ciki nima...

Dariya yayi yace sai mungama cin amarcinmu yarinya duka fa 3month kenan da auren mu...

kafin ta bashi amsa wayanta yayi ringin. Mik'o mata yayi tana d'agawa tace bestiee nayi fushi Allah..

kiyi hak'uri bestiee na ina nan zuwa, dama zance maki gobe za'ayi dating bikina da imran. Wani ihu aysaah ta saki saida salman yaji tsoro..

Kashe wayan tayi ta tashi ta fad'a jikin salman tana dariya...

D'agota yayi yace yanmata yadai irin wannan ihu haka harkin tsoratani..

"D'agowa tayi tana dariya tace ya salman bikin bestie za'a saka gobe ita da imran. dariya salman yayi yace iyyeh kice imran ya d'aga tuta aysaah tace kaidai bari. Ay yasha wahalanta Allah yasa rabonshi ce...

kallon aysaah salman yayi yace ki shirya zamuje gaida su ammi, ihu tafarayi duk ta  cika gidan, tashi tayi ta nufa d'aki...

Dariyan mugunta yayi yace yarinya tunda kinason kije aysai naja maki rai...

cikin shirinta tafito ta saka purple super riga da sket tayi kyau sosai. Tana zuwa tace d'an saurayi ya naganka zaune baka shirya ba? Salman yace yan mata aysai anjima idan anyi azahar zamu. Bahaka taso ba amma dan dole ta hak'ura...

D'aki ta tardashi yana latsa computer. Dafashi tayi tace ya salman anfayi sallah kuma naga kaima kayi pls tashi kashirya...

Bai d'ago ba yace kinga aiki nakeyi bari ayi la'asar tym d'in nagama..

Fita tayi d'akin tana gunguni dariya yayi ya cigaba da abinda yakeyi...

            ★★★★★★★★★★
Parlor ya tarda ta tayi tagumi, hannun ya zare mata yace yanmata nah yadai kikai tagumi?

A shagwab'ance tace bakaine ba kak'i shiryawa ba...

Murmushi yayi yace ayna shirya yanzu bari nayo sallah..

Tsalle tayi tana murna peck ta mashi, fita yayi yana dariya...

"Tunda salman ya fita sallar la'asar baidawo ba kad'an kad'an aysaah ta kalli agogo...

Wajen 8:00 pm taga baishigo ba wayanshi ta kira da mamaki ta ganta bisa gadon ta, hawaye ta share ta shiga toilet ta d'oro alwallar isha...

Tana gama sallah ta cire kayanta tasaka kayan bacci...

Salmam bai shigo gida ba sai wajen 10:00pm..

Yana shigowa ya wuce kitchen ya dafa masu indomie dan yasan yau aysaah sai yayi dagaske zata sauko daga fushin datayi....

Yana gamawa ya wuce d'akinshi yayi wanka...

Yana fitowa ya kulle ko ina kana ya d'auki abincin yayi d'akin aysaaah dashi...

Sallama yayi ya shiga d'akin, ciki ciki ta amsa sallamar. Aje plate d'in yayi ya dawo bisa gado wajenta....

Salman yace yanmata nayi laifi ko? Kiyi hak'uri pls. Bata ko juyo ba bare ta amsa shi..

D'agota yayi yaga tana kuka, shikanshi yasan bai kyauta ba kuma tabashi tausai. Share mata hawaye yayi yace natuba baby doll kiyi hak'uri...

Hawaye ta goge tace ya salman laifin mi namaka haka? Idan laifi na maka kamata yayi kagayaman. rungumeta yayi yace wlhi bakiman laifin komi ba, ninema na maki laifi amma nagane ban kyauta ba kiyi haku'uri kinji my babe...

Hannunta ya kamo ya sauko da ita, yakai abinci bakinta ta goce da kyar salman yasamu ta karb'a tanaci yana bata labari harsai da yaga ta saki ranta..

Suna gama cin abinci salman ya kwashe kayan ya nufi kitchen dasu, da wowa yayi ya kama kunnenshi yace baby doll kiyi hak'uri bazan k'ara ba. Allah gobe zan kaiki wajen ammi d'inki da safe...

Fad'awa kanshi tayi tana dariya, rungumeta yayi sosai yana k'arajin santa na shigarshi...





Phirdauceejeebo.blogspot.com



*IG: yar_ficika*



© *Feedoh Deedoh*✍🏻✍🏻

Comments

Popular posts from this blog

RASHIN GATA 176-180

RASHIN GATA 1-5

DIJAH 241~245