KUNYA ADON MACE 91~95

*KUNYA ADON MACE*

*_Feedoh yanmata_*✍🏻

*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*
    ® *(NWA)*

*_page_* 9⃣1⃣ *_to_*9⃣5⃣

Tunda su aysaah suka fara exams take fatan Allah ya kawo mata sauk'i kuma kullum saitayi try number asad da yan gidansu amma stll kashe a ke cemata, duk idan kaga aysaah saita baka tausai saboda yanda ta rame kamar ba ita ba tadaina walwala kullum cikin kuka take amma duk wannan halin data shiga bai hanata karatun exams ba, saboda burinta taga tafito da papers masu kyau ta cikama asad alk'awarinshi, "dan bazata manta ba kafin asad ya koma cairo watarana suna zaune yana k'ara yimata bayani akan karatunta kallonta yayi yace pretty d'agowa tayi da murmushi ta kalleshi shima murmushin ya mata yace kinsan me nakeso dake? Girgiza kai tayi alamar ah ah asad yace pretty kiyi karatu sosai saboda kifito da sakamako mai kyau kinsan irin karatunku yana da amfani ga alummar annabi badan komai nakesan course d'inki ba saidan ki taimaki wanda aka cuta kamar talaka xakiga masu kud'in mu zasu iya amfani da kud'insu su takashi tunda sunsan baida abinda zai kaisu kotu koma ya kaisu bazaiyi nasara ba shiyasa nakesan ki rik'e karatunki dan ki taimaki talaka dashi, d'ora hannuwanta tayi kan cinyarshi tace in shaa Allah bruh saina baka mamaki zanyi duk yanda kakeso dariya yayi yace nagode sosai my pretty nan suka ci gaba da firansu....
               **********
Zaune take tana karatu da yake gobe zasuyi last paper d'insu tana karatu tana kuka ammi ce ta shigo d'akin da sauri aysaah ta goge hawayenta wuri ammi ta samu tazauna tace ay yanzu bakijin magana tunda har zangaya maki magana ki tsallake kije aysaah kiyi abinda kikeso tunda ni ban isa dake ba, dasauri aysaah ta fad'a jikin ammi tace ammi kiyi hak'uri wlhi kin isa dani ke kad'ai nakeji  dad'inki duk gidannan da  Allah kiyafeman, d'agota ammi tayi tace kinasan na yafemaki? "Eh tace ammi tace toh saikinman Alk'awarin kindaina kuka hakanan kuma zaki dawo aysaahr ki kamar ta da aysaaah tace in shaa Allah ammi nah nadaina daga yau kuma zandawo aysaah ta d'iyar ammi nah rungumeta ammi tayi tace naji dad'i sosai my babe Allah yamaki albarka.....

Yau su aysaah sukayi last paper kowa yafito yana murna amma banda aysaah datayi tagumi tana hawaye pictures ake tayi, haneefa ce ta juya bata ga aysaah ba can ta hangota k'arasawa tayi wurinta ta cire mata hannun datayi tagumi dashi d'agowa tayi ta kalleta b'ata rai tayi tace kedai aysaah bakijin magana, dan  Allah yanzu miye na zuwa nan kiyi tagumi kowa saiya gane halin da kike ciki, yanzu tashi mushiga cikin mutane ayi pix d'in dake zatayi magana kenan haneefa tace shhhhhhh dan dole aysaah ta mik'e ta shiga mutane anata pix da ita amma da kaganta kasan tana cikin damuwa.......


         "Tunda su aysaah sukagama exams kullum cikin tunanin mafita takeyi amma bata samu ba, tana zaune d'aki salman ya shigo da sallama amsawa tayi wuri ya samu ya zauna kusa da ita kallonta yayi yace congrats sis Allah yasa kici amfanin karatun naki amsawa tayi da amin, "shiru ya gifta can salman yace aysaah nayi bincike kan su asad harcan cairo d'in amma gaskia bansamu wani imformation a kansu ba saidai kawai muciga ba da adua Allah ya bayyanar dasu, in banda hawaye ba abinda aysaah keyi tunda yafara magananshi, lallashinta da nasiha ya shiga yimata saida yaga tayi shiru, salman yace gobe in shaa Allah zanje kd saida gabanta ya fad'i cikin sanyin jiki tace Allah ya kiyaye hanya amsawa yayi da amin.......
                 **********
Tunda ta tashi gabanta ke fad'uwa ko abinci ta gazaci, wayanta ne yayi ringin tana dubawa taga sunan papa nan da nan gabanta yaciga ba da fad'uwa a sanyaye ta d'auki wayan banji mi aka ce ba, aysaah tace to papa tana aje wayan ta tashi tayi hanyar sauka k'asa "parlor ta iske su papa ammi da mummyn zarah wuri ta samu kusa da ammi ta zauna aysaah tace papa gani, "gyaran murya papa yayi yace aysaah yau alk'awarinmu dake ya cika amma banji kinceman komai ba kuma na tambayi amminki tace baki bata sak'o ba shine nace bari naji dafa gareki, "aysaah tace papa gaskia banda wanda nakeso saboda banyi tunanin fara soyayya ina karatu ba papa yace toh zab'ina zanbaki kenan? Girgiza kai tayi tace papa kayi hak'uri Allah bansan wanda zaka bani kubarni haka bazanyi aure ba, tsawa mummynzarah ta daka mata tace ubanwa zai kyaleki haka shasha sakarai wadda batasan mi takeyi ba toh dole ko kinaso ko bakiso ki auri wanda mahaifinki zai baki yarinya duk kin lalace, "ran ammi ya b'ace tace haba hajia mi yarinyar nan tamaki kika tsaneta haka kefa kika haifeta idan bakija d'iyarki a jiki ba kika bata k'auna da kulawa waye zai bata amma kinbi kin tsani yarinya ko rab'owa tayi wajenki saikin mata tsawa, kuma da kike cewa anbi an lalata yarinya nikenan na lalata ta Allah yaga zuciyana irin tarbiyan da na bata ban bata muguwar tarbiya ba amma nagode, aysaah tace ammi kiman rai dan Allah tashi ammi tayi ranta b'ace itama aysaah mik'ewa tayi tana mik'ewa jiri yafara d'ibanta ammi tafara kwalama kira kafin ammi ta juyo ta yanke jiki tafad'i da sauri ammi ta dawo duk'awa tayi ta fara jijiga aysaah amma aysaah tayi nisa saima jini dake fitowa daga bakinta........




Phirdauceejeebo.blogspot.com


*IG: yar_ficika*


© *Feedoh Deedoh*✍🏻✍🏻

Comments

Popular posts from this blog

RASHIN GATA 176-180

RASHIN GATA 1-5

DIJAH 241~245