KUNYA ADON MACE 71~75

*KUNYA ADON MACE*

*_Feedoh yanmata_*✍🏻

*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*
® *(NWA*)

*_page_*7⃣1⃣ *_to_*7⃣5⃣

Tana shiga d'aki ta maida k'ofa ta rufe fad'awa tayi kan gado ta saka sabon kuka kamar wadda aka cirema rai, ammi tazo ta dinga bugun k'ofa da kyar ta tashi ta bud'e mata, shigowa ammi tayi cikin d'akin, hannunta ta kamo ta zaunar da ita itama zama tayi, kiran sunan ta tayi d'agowa tayi ta kalleta, ammi tace aysaah kiban hankalinki magana nakeso nayi dake, "d'aga mata kai tayi tana share hawaye, aysaah sunanta ammi ta kira, amsawa tayi da naam, tace haba aysaah miye sa kike haka shin kinfisan kullum kina d'agaman hankali ne? Kinsan babu abinda na tsana naga damuwarki amma ke kullum saikin d'agaman hankali tafiyan asad baya nufin kun rabu ba kenan zaidawo, kuma kinsan bazai k'i bin umurnin mahaifansa ba saboda ke dan haka wake up  kidaina kuka kidaina sa damuwa cikin zuciyanki idan kinasan mu shirya, "fad'awa tayi kan ammi tace kiyi hak'uri ammi nah in shaa Allah nadaina kuka bazan sake d'aga maki hankali ba, murmushi ammi tayi tace gud gal Allah yamaki albarka amsawa tayi da amin, tashi ammi tayi tabar d'akin....
               ***********
Tana bud'e kit d'in english gold ne tagani sark'a da d'an kunne sai zobe shima da ban tana d'auko wa ta ga wata takarda tana budewa taga wata yar k'aramar ta karda ta fad'o da writing note "d'auka tayi ta duba ga abinda tagani, *assalam pretty nasan zaki mamakin ganin abinda kika gani so ba abin mamaki bane ba saboda komi nasamu na kine, wannan english gold d'in nakine keda ablah na saima wa naso nabaku a tare amma Allah bai nufa ba tunda zanbar gari shiyasa nabaki nd takardun da kika gani na gida nane dake maitama nayi shawara da su maaah sunce na barmaki dan haka na barmaki dunia da lahira, nd pls kidaina saka damuwa kisani ni asad ina tare dake ko da yaushe nd ki tabbatar kafin nazo ganinki komai ya daidaita ke da salman...... Ki huta lafiya* rungume takardan tayi tana kuka sosai, tashi tayi ta kwashi kayan ta nufa k'asa dasu parlor taci karo da su ammi harda papa gabansu ta zube kit d'in saidai ta b'oye letter d'in. Bayani ta masu babu wanda baiyi mamaki ba daga k'arshe papa ya karb'i takardun gidan yana shima asad da albarka...

"Washe gari tana tashi ta shirya atamfa ta saka red doguwan riga gaskia d'inkin ya mata kyau dayake stone work ne sark'an da asad yabata ne ta d'auko ta saka kallon kanta tayi a mirror ita kanta tasan sark'an yamata kyau, rolling tayi da red scarves kana ta d'aura agogonta mai tambarin apple ta d'aura a tsintsiyar hannunta, jikarta da takalmin ta duk na prada ne feshe jikinta tayi da turare, kana ta fita daining area ta iske iyayenta harda papa fad'awa kan ammi tayi tana shagwab'a d'agota ammi tayi tace masha Allah yarinya na kinyi kyau mummyn zarah ta kalli salman tace kaji yanda ake kod'a wannan mummunar dariya salman yayi yace naji, papa yace anya kuwa zaku iya rik'e alk'awarin asada kuwa? Ammi tace yawwa papa tell dem dai dariya mummyn zarah tayi tace daga fad'an gaskia toh shikenan nida yarona mundaina magana 'haka dai suka dinga cin abinci suna fira cikin k'aunar juna gaskia zaman gidan yana burgewa kowa saboda kansu had'e yake baka tab'a gane d'an wannan inba kasani ba, aysaah na gamawa tabi iyayenta tamasu peck harda mummyn zarah, zata juya kenan salman ya rik'ota yace ina nawa murmushi tayi tamashi peck ta ruga da gudu, kallo ammi ta bita dashi cikin sha'awa da son d'iyar tata....

Tana shiga skul bata jima ba saiga haneefa, kallon ta haneefa tayi ta gano damuwa k'arara a fuskarta girgiza kai tayi dan tasan damuwar aysaah bata wuce salman, dafata tayi firgigit ta d'ago murmushi ta mata itako haneefa d'aure fuska tayi tace bestie bazaki daina sakama kanki damuwa ba ko? Allah kinji na rantse ko, zan gayama ya asad tun da dama kafin ya wuce saida ya zo yaban amanarki kuma namashi alk'awarin zan rik'e amana, amma tun ba'aje ko ina ba kinfara sab'a alk'awari da kika d'aukar mashi "jawota tayi tace kiyi hak'uri bestie nasan ina saku damuwa amma Allah ba yin kaina baneba kudai cigaba da tayani da adua amma wlhi bestie inasan salman fiye da tunaninku kuma gashi ya asad yace kafin ya dawo na tabbata salman yana sona amma gashi banda wata hanya, hawayen da suka gangaro mata ne haneefa ta goge ma tace aysaah adua dai ita zance ki cigaba saboda nasan watarana zakici riban adua nki in shaa Allah, kada ki nuna gajiyawarki wajen gayama Allah buk'atunki kinji ko, fad'awa jikinta tayi tana hawaye da kyar haneefa ta samu ta daina hawaye, a haka dai suka gama abinda suke a skul....





Phirdauceejeebo.blogspot.com

*IG: yar_ficika*




© *Feedoh Deedoh*✍🏻✍🏻

Comments

Popular posts from this blog

RASHIN GATA 176-180

RASHIN GATA 1-5

DIJAH 241~245