KUNYA ADON MACE 61~65

*KUNYA* *ADON* *MACE*

*_Feedoh_* *_yanmata_*✍🏻

® *NWA*

*_page_* 6⃣1⃣ *_to_*6⃣5⃣

A daddafe takai safe saboda ko barcin kirki batayi ba hankalinta yana kan asad dan ta tabbata asad ba lafiya ba tunda harya kasa d'aga kal d'inta kuma bai kirata bac ba, tana tashi da safe ta fad'a wanka tana fitowa ta zira jallabiya tasaka turare ta d'auki key d'in mota, d'akin ammi ta shiga tana shiga ta tarda tana toilet bata iya tsayawa tafito writing note ta aje mata bisa gado ta juya ta fita, parking space ta wuce motarta ta shiga ta mata key horn ta danna mai gadi ya wangale mata gate yana mata kirarin da ya saba hannu kawai ta d'aga mashi tayi gaba, gudu ta dinga shararawa kamar zata tashi sama, Allah ne yakaita gidansu asad lafiya....

"Horn ta dingayi ba tsayawa da gudu mai gadi ya zo ya wangale mata gate, shiga tayi cikin gidan tana shiga batako tsaya kulle motanba ta fito tayi cikin gida da gudu....
              ***********
bako sallama ta fad'a parlor d'agowa ma tayi taga waye aysaah tagani tsaye tana dube dube tashi maaah tayi ta kamo hannunta ta zaunar da ita, kallonta maaah tayi tace my babe ya dai kika shigo bako sallama kalli yanda duk kika firgice sai a lokacin hankalinta ya d'an dawo, ajiyan zuciya tayi tace maaah ina kwana amsawa tayi cikin kulawa, kallonta tayi tace miyafaru naganki haka? Duk'ar da kanta tayi k'asa tace maaah nazo duba ya asaad ne tun jiya nake kiranshi bai d'aga ba kuma bai kira bac ba shine nace bari nazo naga lafiya, murmushi maah tayi dan tasan irin shak'uwar datake tsakanin asad da aysaah....

Kallonta maaah tayi tace haryanzu bai fito ba yana d'aki nasan bai tashi ba,,,,

Tashi tayi ta nufa hanyar d'akinshi tace yanzu kuwa zai tashi maaaah.....
            ***********
Binta maaah tayi da kallo tana murmushi, tana isa bakin k'ofan d'akin knocking tayi shiru murd'a murfin k'ofan tayi ta shiga d'akin da sallama amma shiru ba a amsa ba ga d'akin yayi duhu, light ta kunna dan da nan haske ya baibaye d'akin, saman gado ta hangoshi k'udundune da blanket, da sauri ta k'arasa bisa gadon yaye blanket d'in tayi tace ya asad, bud'e idon shi yayi ya kalleta amma yakasa magana hankalinta atashe tace ya asad mike damunka saikuma ta fad'a kanshi tana kuka, da kyar ya d'agata shima tashi yayi ya kalleta girgiza mata kai yakeyi alamun tadaina kuka, cikin sheshek'an kuka tace dama nasan baka da lafiya naji a jikina, dan Allah mike damunka a hankali yake magana yace my pretty kaina ne keman ciwo tun jiya, kasha magani tambayar da tamashi kenan girgiza kai yayi alamar ah ah, tashi tayi ta fita ta koma cikin gida wajen maaah.....

Tana zuwa inda ta bar maaah nan ta tardata zumb'ure baki tayi tace Allah maaah saina maida ya asad gidanmu tunda baki kula dashi, murmushi maaah tayi tace mikuma nayi yanzu, b'ata fuska tayi tace yanzu maaah ya asad bai lafiya yana ciwon kai shine baki sani ba haba maaah, "kallonta maaah tayi cikin kulawa dan tabbas batasan bai lafiya ba kuma bata kyauta ba da bata dubashi yau ba dan rabonta dashi tun jiya, maah tace ayman hak'uri nayi laifi, murumushi tayi tace baki laifi ay maaah...


      "Tashi maaah tayi ta nufa sashen asad itakuma aysaah tayi kitchen dan ta had'a mashi breakfast, "indomie ta dafa mashi saikuma tea mai kauri da ta had'a mashi, a tray ta jera su ta d'auka tayi hanyar d'akinshi dasu, da sallama ta shiga kallonta maaah tayi tana tsokanarta tace yayi aysaah yanzu haka asad kawai kikama girki, murmushi tayi tace ayshine bai lafiya, da taimakon maaah asad ya tashi yayi brush takuma had'a mashi ruwan wanka saida ya shirya tsaf kana aysaah ta dawo d'akin da kanta ta dinga bashi abincin yanaci suna rigima dan tace saiya cinye indomie kuma ya shanye tea d'in shikuma yace ya k'oshi maaah dai na gefe na masu dariya dan dole yayi yanda takeso aykam taji dad'i, yana gamawa ta kwashe kayan kana ta kirasu ammi da salman ta gaya masu...

"su ammi ne suka shigo da kayan marmari nik'i nik'i tashi maaah tayi ta taresu da murna "dan yanzu zumunci suke sosai, zama sukayi suka gaisa, maaah ta kalli mummynzarah tace ina d'anki salman murmushi mummynzarah tayi tace yana part d'in asad, maaah tace eh lallai shine yak'i zuwa ya gaidani ko, ammi tace yafazo "mummynzarah tace aymuna hak'uri maaah dariya sukayi gaba d'aya, kana suka tashi sukayi sashen asad, salman yana ganin maaah yafara kame kame dariya maah tayi tace ni rabu dani ayka nuna d'an uwanka yafi mamanka dariya yayi yace ayman afuwa duk na rud'e ne shiyasa, nan  sukama asad ya jiki, sai marece kana sukabar gidan,  itako madam aysaah gaba d'aya nan tadawo saboda tace maaah bata kula da asad yanda ya kamata, "kwananta hud'u asad ya warware kamar bashi ba, kana ta had'a kayanta tayi gida............



Phirdauceejeebo.blogspot.com


*IG*: *yar_ficika*



© *Feedoh* *Deedoh*✍🏻✍🏻

Comments

Popular posts from this blog

RASHIN GATA 176-180

RASHIN GATA 1-5

DIJAH 241~245