KUNYA ADON MACE 166~170

*KUNYA ADON MACE*

*_Feedoh yanmata_*✍🏻


*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*
  ® *(NWA)*

*_page_*1⃣6⃣6⃣ *_to_*1⃣7⃣0⃣

Tunda aysaah tayi sallan asuba bata koma bacci ba. Aiki kawai takeyi, dariya salman yayi yaja blanket ya cigaba da bacci...

7:00am aysaah tadawo d'aki, yaye blanket d'in salman tayi. Shafa kanshi tafarayi a hankali tana hura mashi iska a fuska...

Ahankali ya fara bud'e idon shi, zaune yaganta tana ta faman murmushi. Aysaah tace ya salman wake up haka nan pls, kasan fa inda zamu. Jawota yayi ta fad'o jikinshi ya rungumeta, mutsulniya tafara tanasan kwace kanta amma ta kasa..

A kunne ya rad'a mata, yarinya ba yanzu zamu tafi ba sai nagama bacci na, infact saikin ban hak'k'ina inkuma kika k'iya nafasa tafiyan. Zaro ido tayi, dariyan mugunta yayi yace i mean it....

Gunguni aysaah tafarayi, shiko salman dariya kawai yake mata. Ahaka yabiya buk'atanshi. "Yana gamawa ya fad'a toilet danyin wanka, itama tashi tayi ta nufa d'akinta ta fad'a toilet...

Sha d'aya ta fito cikin shirinta cikin bak'ar kimono, daining table ta iske shi yana ganinta ya taso yayi huging nata peck ya mata a kunci, babe kinyi kyau sosai fa anya zamu fitar nan kuwa? Marairaicewa tayi pls ya salman kayi hak'uri Allah nasa ran ganin ammi nah. Hancinta ya lakuta yace wasa nake maki zan kaiki kiga amminki yau, dariya tayi ta mak'alk'aleshi...

Suna gama cin abinci ta kwashe kayan ta nufa kitchen dasu. Salman ne ya fito yana d'aura agogo ga hannu, amsa tayi ta d'aura mashi kallonta yayi yace nagode matata. Murmushi aysaah tayi tace is part of my duty dearieee..

Tafe suke suna fira cikin so da k'auna, sahad store suka tsaya danyin tsaraba. Kaya suka kwasa kamar basu san darajan kud'i ba, suna gamawa suka kai aka masu bill salman ya biya, aka kwasa kayan aka saka a mota...

Kwance take jikinshi kamar mage, sai shagwab'a take mashi kallonta yayi yace baby doll karkisa na kasa driving d'innan fa. Dariya tayi tace sai na amsa, daidai sun iso gaban gida. Horn yayi mai gadi ya lek'o ganin salman yasa ya wangale gate. Cinna kan motarshi yayi mai gadi ne ya biyoshi yana mashi barka da zuwa...

Baiko ida parking ba aysaah ta bud'e murfin motan ta fita, ta nufa cikin gida da gudu tana kwalama ammi kira. Girgiza kai salman yayi yana daria, gaisawa sukayi da baba mai gadi salman ya mashi kyautar da ya saba kana ya d'auko jikar aysaah ya nufa ciki da ita....

Parlor ta tarda su fad'awa kan ammi tayi tana dariya, d'agota ammi tayi tace aysaah kece saikuma ta rungumeta tana hawaye itama aysaah hawaye takeyi, tsaye yake ya hard'e hannuwa yana kallon ikon Allah. Papa yace toh yanzu miye kuma kuke kuka? Mummynzarah tace salan tace my boy yana mata laifi ko? Dariya ammi tayi tace mudai bamuce ba...

Xama salman yayi tare da gaida su mummynzarah amsawa sukayi cikin sakin fuska, itama aysaah gaida su tayi nan aka shiga tsokanan aysaah "mik'amata bag d'inta salman yayi. Aysah tace ammi inasu zarah? Ammi tace sunje kd jiya zumb'ure baki aysaah tayi shine basuzo mukaje tare ba, hararanta salman yayi yace waye zai barki kije? Hararshi ammi tayi tace marar kunya kai zaka barta dariya akayi gaba d'aya. Baba mai gadi ne yafara shigo da kayan da sukayi tsaraba. Nan papa ya dinga shimasu albarka... Tare da k'arayi masu fad'a akan su zauna lafiya da junansu..

Ammi tace my babe tashi mutafi d'aki kinji, dariya mummynzarah tayi tace baza'ayi gabanmu ba kenan, ammi tace eh saboda bamuson kuji sirrinmu..

Mummynzarah taji dad'in ganin aysaah cikin jin dad'i, saida kunya tasa ta kasa nunawa..

"Suna shiga d'aki ammi ta kalli aysaah ita kanta taji dad'in ganinta cikin kwanciyan hankali, ammi tace aysaah badai wata matsala tsakanin ku ko? Murmushi aysaah tayi tace babu ammi yana k'ok'arin kyautataman. Ammi tace Alhamdulillah, "yanzu cikinki watanshi nawa? kanta ta sadda k'asa tace ammi haryanzu banda ciki , d'agota ammi tayi tace karki damu baby nah in shaa Allahu "Allah zai baki kinji, karna sake naga kin tada hankalinki. in shaa Allah ammi zanyi yanda kikace...shafa kanta ammi tayi tace gud gal Allah ya maki albarka, amin ta amsa...

Sai dare su aysaah sukabar gida cike da kewar iyayenta.
                   ★★★★★★★★
Tunda aka fara bikin haneefa aysaah bata zauna ba, kullum ta fita sai dare take dawowa...

Salman ne keta faman yima aysaah rigima, "nifa aysaah nagaji tunda aka fara bikin nan bakida tym d'ina kullum kina kan hanya, shafa sumarshi tayi tace haba ya salman ay haneefa tafi k'arfin komai wajenmu kaga fa bikinmu gida tadawo gaba d'aya inkayi hak'uri ay gobe ake gama bikin, rungumota yayi yace shikenan princess Allah yabasu zaman lafiya ki d'auki 100k kibata gudumuwa ta. Rungumeshi aysaah tayi tana mashi godia...

Angama bikin haneefa lafiya, ankai amarya minna kuka haneefa tayi sosai da aysaah zata dawo ita kanta harta iso abuja tana kuka...

Salman ne ya shigo da sallamarshi rungumeta yayi ta baya, yace ur welcum habeebty, tnx aysaah tace. Juyota yayi yaga tana kuka murmushi yayi yace dama nasan za'ayi haka, murmushi tayi tace Allah ya salmab duk dauriya na saida haneefa tasani kuka. Hannunshi ya d'ora bisa bakinta yace aydama dole sai kunyi kuka bare yanzu kunyi nisa da juna, kafin  ta k'ara magana ya sungumeta yayi ciki da ita tana tsalle tsalle amma ta kasa kwace kanta.

Aysaah tace pls ya salman ka kyaleni Allah nagaji, dariya yayi yace Allah yarinya baki isa ba. "Bayan da ta iya dole ta kyaleshi...




phirdauceejeebo.blogspot.com



*IG: yar_ficika*




© *Feedoh Deedoh*✍🏻✍🏻

Comments

Popular posts from this blog

RASHIN GATA 176-180

RASHIN GATA 1-5

DIJAH 241~245