KUNYA ADON MACE 156~160

*KUNYA ADON MACE*


*_Feedoh yanmata_*✍🏻

*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*
  ® *(NWA)*

*_page_*1⃣5⃣6⃣ *_to_*1⃣6⃣0⃣

K'arfe hud'u na koma d'akin aysaah dan gano ma masu karatu yanda aysaah da salman suka k'are daren jiya..😂😂

Kwance take bisa gado tana kuka "matsowa yayi kusa da ita pls aysaah ki daina kuka Allah bazan k'ara yimaki da zafi ba..

Harara ta wurga mashi wama zai k'ara yarda da kai indai haka ake aure nidai ka maidani wajen ammi nah...

Shi maganan ma dariya ta bashi amma ba halin yi, matsowa yayi kusa da ita ya dafa mata kai zafi sosai yaji ta bashi tausai, bige mashi hannu tayi...

"Tashi yayi yaje toilet ya had'a mata ruwan zafi ya saka dettol ciki, d'akin yadawo dan tai maka mata...

salman yace tashi aysaah ki wanka zakiji k'arfin jikinki. Hannunta ya kamo ta goce..

Tashi tayi da sauri saikuma ta fasa k'ara "d'aukanta yayi kamar wata yar baby yayi toilet da ita..

Da taimakon salman aysaah tayi wanka d'auko ta yayi ya maidota d'aki "bedsheet d'in gadon ya cire saboda ya b'aci da jini ya shinfid'a wani kana ya aza aysaah bisa gado...

Kayan bacci ya d'auko ya saka mata ya bata magani ta sha kana ya kwantar da ita...

Tashi yayi shima ya shiga toilet yayi wanka..

Bayan sunyi sallar asuba "salman ya d'aga hannu yana ma Allah godia da yabashi kamilar mace..

Yagama adu'o'i ya juyo yaga aysaah kwance tana bacci..

Tausayinta ya kamashi dan shi kanshi jiya yasan yaba aysaah wahala...

cire mata hijab d'in yayi ya d'auketa ya maida bisa gado. Yana rungume da ita har bacci yayi gaba dashi cikin nishad'i...

Sha biyu daidai salman ya zare jikinshi daga jikin aysaah. D'akinshi ya nufa toilet ya fad'a yayi wanka...

Cikin shirin k'ananan kaya ya dawo d'akin aysaah..

Haryanzu bacci take "samun wuri yayi ya zauna ya k'ura mata ido yana murmushi...

A hankali aysaah ta fara bud'e idonta tana salati "kallon salman tayi dake ta faman washe mata baki. Murgud'a mashi baki tayi ta juya baya..

Kwantowa yayi bisa bayanta "yace haba baby doll nifa mijinki ne bai kamata kina fushi dani ba akan abinda Allah ya halarta man "kuma namaki alk'awarin bazan k'ara yimaki da zafi ba..

Tausayin salman ya kamata juyowa tayi ta shafi kuncin shi tana murmushi. Rugumeta yayi yace kindaina fushi dani ko? D'aga mashi kai tayi, peck ya mata yace tnx my baby...

Hannu ta mik'a mashi kamata yayi ta tashi ta shiga toilet....
                ★★★★★★★★★
Tana fitowa daga wanka ta iske salman ya aje mata kaya dariya tayi taje gaban mirror..

Light makeup tayi ta mulke jikinta da turaruka masu tsada da k'amshi...

Kayan da salman ya aje mata ta d'auka ta saka k'ana nan kaya ne rigan iyakarta cibi sai wandon baikai gwuiwa ba...

Tana sakawa tadawo gaban madubi ta kalli kanta ita kanta tasan tayi kyau ga gashinta da ta raba hud'u ta saka ribom sai ta fito baby doll d'in sak😂😂

Parlor ta iske salman yana ganinta yace wow duk'ar da kanta tayi tana dariya..

Duk'awa tayi k'asa ta gaishe amsawa yayi ya kamota ya zaunar da ita kusa dashi yana murmushi..

Kallonta yayi yace babynah kinyi kyau aysahh tace tnx bruh "yanzu amminki ta aiko muna da abinci ga wannan ma tace abaki yar guntuwar takardace ya ba aysahh..

Duba letter tayi tana karantawa tana murmushi "lek'owa salman yayi ta b'oye, fizge ta yayi ya tashi ya ruga binshi tayi yana gudu yana karantawa. Dole ta zauna saboda zafin da takeji...

yana gama karantawa ya wurga mata yana dariya...

Turo baki tayi shine ka karanta man sirri? Kama kunnenshi yayi yace on my kneels d'iyan ammi baxan k'ara ba...

Kusa da ita ya zagayo ya zauna hannunta ya kama yace ammi fa na nuna sankai "kijifa abinda tace wai ga abinci nan basai kin wahalan girkawa ba kuma tayi missn d'inki. Ke kad'ai tayi mssn banda ni kenan...

Dariya aysaah tayi tace aykasan tsakanin mama da dota, dun gurinta yayi yana dariya...

Hannunta ya kama suka tafi daining table da kanshi ya dinga ba aysaah abinci saida yaga ta kusa amai kana ya kyaleta. Shima ci yafarayi yanaci suna fira..

Suna gamawa aysaah ta kwashe kayan ta nufa kitchen saida ta wanke su kana ta dawo parlor...

Tana zuwa salman ya rufe mata fuska da kyalle yaja hannunta suka nufa haraban gidan...

Bud'e mata fuska yayi a hankali ta dinga bud'e fuskanta "kallonshi tayi tana murmushi...

Makulli ya mik'amata aysaah tace na miye? Mota ya nuna mata..

Zare ido tayi saikuma ta ruga wajen motan tana dariya..

Juyowa tayi tace ya salman da gaske wannan mota tace? Marcedes AMG  E43 ce fa nake gani, my fav car..

Takowa yayi yazo kusa da ita sak'ala hannunshi yayi a k'ungunta yace yes motarki ce aysaah, "duk'awa tayi k'asa tace na gode ya salman Allah yabani ikon yimaka biyayya har k'arshen rayuwata...

D'agota yayi ya rungume yace kinfi haka, nike da godia da kika rik'eman mutunciki da darajanki dole nayi duk abinda zai faranta ranki, kamar yanda kika faranta raina jiya...

Duk'ar da kanta tayi tana dariya "sun sunarta ya farayi yana mata kiss ta ko ina. Nuni tamashi da inda suke dariya yayi yace ayba kowa mukad'aine aysaah tace idan mukayi bak'ifa? Murmushi yayi ya sungumeta yayi cikin gida da ita.....



Phirdauceejeebo.blogspot.com


*IG: yar_ficika*




© *Feedoh Deedoh*✍🏻✍🏻

Comments

Popular posts from this blog

RASHIN GATA 176-180

RASHIN GATA 1-5

DIJAH 241~245