KUNYA ADON MACE 141~145

*KUNYA ADON MACE*

*_Feedoh yanmata_*✍🏻


*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*
   ® *(NWA)*


*_page_*1⃣4⃣1⃣ *_to_*1⃣4⃣5⃣

Alhamdulillah hausawa sunce duk abinda aka sama lokaci zaizo k'arshe. Yau aysaah ta zama cikakkiyar lawyer inda dubban mutane suke tayata murnan kammala karatunta lafiya...

Kyaututuka aysaah ta amshe abun tun yana burgeta hartakai tana mamaki irin kyaututukan data samu..

Tsaye yake ya hard'e hannunshi bakin mota yana kallonsu ita da sauran students suna ta d'aukan pix. Takowa yayi yazo kusa da su yace kuzo na maku to juyowa tayo taga salman ne "fad'awa tayi jikinshi tana dariya rungumeta yayi "sauran students suka fara dariya suna ihu...

Haka dai salman ya dinga yi masu pix sai marece sosai kana suka taho "gida suka aje haneefa kana suka d'auki hanyar gida suna tafe suna firan soyayya....

Kallonta salman yayi yace yarinya na ni miye zan bada gift? Murmushi tayi tace kanasan na fad'a maka d'aga kanshi yayi yace eh mana...

Aysaah tace toh karkad'e kunnenka, shiko yakama kunne ya karkad'e "dariya ta dingayi mashi. Kallon shi tayi tace ya salman abinda nakeso kawai kasoni har k'arshen rayuwata kayi hak'uri da duk shirme na watarana zan daina shine babban gifts d'in da zakaban..

Jawota yayi jikinshi yace kisa aranki ke kad'ai ke da zuciyan salman sai yanda kikayi da ita " kuma ba shirme kikeyi ba yarinta ce kuma ni yarintarki burgeni takeyi dan haka karki ji komai  *zan maki hallaci fiye da yanda naufal yaima hudah zan soki fiye da yanda moh yaso nafeesa zan k'auna ce ki fiye da yanda hamza ya nunama dijah k'auna*..

Rungumeshi aysaah tayi k'am tana dariya. A haka har suka iso gida...

```BAYAN SATI D'AYA```
salman ne ya kalli su aysaah yace haneefa dami dami zakuyi? Haneefa tace bridal shower sai kamu sai dinner kawai...

Atm d'inshi ya basu yace gashinan kuciri abinda zai isheku amsa haneefa tayi "kallon aysaah yayi yace yadai yarinya na ba wata matsala ko? Dariya tayi tace babu...

Aysaah da haneefa ne ke yawon rabon iv duk gidajen k'awayensu saida sukaje "dan haneefa tayi parking ta dawo gidansu aysaaah sai anga ma biki..

Mai gyaran jiki ammi ta  d'aukoma aysaah daga mai duguri ita zata mata gyaran jiki ta mata lallai kuma bata zuwa ko ina...

Salman ne ya dinga kiran aysaah a waya yana san ganinta dan yau kwananshi ukku bai ganta ba "k'in d'auka tayi dan tasan halin masifan ammi...

Part d'in ammi ya nufa parlor suka had'u dashi kallonshi tayi ta d'aure fuska tace yadai malam? Sosa k'eya yayi yace dama gaidaki zanyi ammi tace toh nagode jeka "har ya juya yace ammi aysaah fa? ammi tace neman mi kake mata? Dama inasan ganinta ne ammi tace toh ba yanzu ba dan yanzu gyaran jiki ake mata "fita yayi yana gunguni abin dariya yaba ammi..

Yau aka kawo lefen aysaah akwati sha biyu sai key d'in mota duk wanda yaga lefen aysaah sai ya burgeshi..

Yan kd ma sun taho gida ya cika kamar yau ne ranan bikin...

Aysaah da mufeedah da haneefa ne suka kulle kansu k'uryan d'akin ammi suna fira...

Aysaah ta kalli mufeedah tace sis ance sahr k'awarki ce bani labari dariya mufeedah tayi tace aike sis randa ya salman yaceman sahr yakeso har zazzab'i nayi dan na tausaya maki...

Dariya haneefa tayi tace sis ay randa bestie ta gane ya salman nasan wata karkiso kiga hauka nan suka dingayi ma aysaah dariya harta k'ule saida sukayi mai isarsu kana suka yi shiru...

Mufeedah tace ay ta dawo wai yayi hak'uri "wlhi she cant do without him waye waye aykam yamata spark yace shi yana da mata kuma aysaah da yake bata labari yarinya mai hankali da tarbiya. Kuma karta k'ara kitanshi idan kuma ta cigaba da kiranshi zaiyi maganinta. Kai in tak'aice maku magana ta daina yiman magana saboda ya salman..

aysaah tace ayni fushi yake dani wai ammi ta hanashi ganina kuma da amincewa ta, yakasa gane nikaina yanda nakeji na rashin ganinshi amma kanshi yasani "kallonta sukayi suka bushe da dariya mufeedah tace aysaah Allah da gaskian ammi salman ya b'ataki "d'aka mata duka tayi tace ina ruwanku aydai miji nane....



Phirdauceejeebo.blogspot.com




*IG: yar_ficika*



© *Feedoh Deedoh*✍🏻✍🏻

Comments

Popular posts from this blog

RASHIN GATA 176-180

RASHIN GATA 1-5

DIJAH 241~245