KUNYA ADON MACE 171~175

*KUNYA ADON MACE*

*_Feedoh yanmata_*✍🏻

*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*
® *(NWA)*


*_page_*1⃣7⃣1⃣ *_to_*1⃣7⃣5⃣



*BAYAN SHEKARA BIYU*
Aysaah ce tsaye gaban salman ta rik'e k'ugu ga k'aton cikin ta, d'agowa yayi ya kalleta ya kwashe da dariya. Salman yace yadai maman babys kika kama man k'ugu kamar mai shirin dambe "tab'e baki tayi kaga tashi ka kaini silver birth shawarman can nakesan ci..

Zaro ido salman yayi yace yanzu fa kika gamacin bugger. Aysaah tace Allah shawarman silver birth nakeso idan kuma ba zaka kaini ba kagayaman kawai. Dariya salman yayi yace ni na isa jirani na d'auko key d'in mota mutafi...

Suna kan hanya salman ya kalli aysaah, yace baby doll d'azu ammi ta kirani wai tunda cikinki ya shiga 8month na maidaki gida ki haihu. Kallonshi tayi mikace mata to? Ban bata amsa ba cz gaskia bansan kikoma gida nafisan ki haihu gidanki. Murmushi aysaah ta cigaba dayi, kallonta yayi ya bakice komai ba? Ya salman mi kakeso nace duk yanda kukayi daidai ne ay. Daidai sun isa gate d'in silver birth...

Suna shiga salman yaje yayi mata oder, kana yadawo wajenta ya zauna. basu fi minti talatin da zuwa ba aka kawo masu..

"Kallonta salman yayi yace madam tashi mutafi. Aysahh tace ina? Ay anan zanci, zaro ido yayi eh nan zanci. Dandole ya mik'amata...

Saida tagamaci ta kalli Salman tace bruh lets go. Dariya yayi ya mik'e, jitayi an rik'eta ta baya ana mammy! mammy!! Mammy!!! "juyowa tayi dan taga wanda ya rik'eta. Wata yar k'aramar yarinya ce wadda baza tafi shekara hud'u ba ta mak'alk'aleta. Tabbas yarinyar ta burge Aysaah, duk'awa tayi ta shafi kuncin yarinyar, tace wia iz ur mom? Kallonta babyn tayi tace i don't...

Rik'e hannun yarinyar tayi kamar ta santa, kallonta salman yayi yace yadai hajia nah sakarta mutafi mana. Murmushi tayi ta girgiza kai ya za'ayi mutafi mubarta mutsaya muga zuwan mammy d'inta..

"Wata yar kyakyawar mace ce wadda batafi sa'an Aysaah ba tak'araso wajen, sallama tamasu amsawa Aysaah tayi, saukowa yarinyar tayi daga jikin aysaah ta ruga wajen matar nan tana mammy ina kika shiga? D'aga ta sama tayi tace little ke zan tambaya daga naje na maki oder saiki b'ace..

Matuk'a sun burge Aysaaah, kallon mammy little tayi tace mammy meet my anty tana da kirki. Dariya tayi ta mik'ama Aysaah hannu tace my name is hanan, murmushi aysaah tayi tace nice meeting u. Hanan tace same...

Aysaah tace pls miye real name d'in little? Hanan tace *AYSAAH* wani juyowa salman yayi ya kalli yarinyar da aka kira aysaah. Itako Aysaah mutuwan tsaye tayi, hanan tace yadai antyn little? Murmushi tayi tace notin..

kallon ta Salman yayi ya mik'ama little hannu, da gudu ta sauka taje wajenshi rungumeta yayi sosai, ya kalli hanan yace sunan antyn hanan kenan Aysaah, ita kanta hanan abun yabata mamaki. murmushi kawai tayi tace shiyasa sukaji suna son juna. Dariya salman yayi...

      Nan fa suka fara fira, harda exchanging contact. Aysaah ce ta shafi kuncin little tace my baby ina nan zanzo d'aukarki kiman weekend "kallon hanan tayi tace hpe za'abani? Murmushi tayi tace saikin zo amma zakiyi fama da daddynta kafin ya yarda cz baisan yayi nesa da ita. Aysaah tace in shaa Allah zai yarda nan sukayi bankwana kowa ya tafi...

```BAYAN KWANA BIYU```
Aysaah ce ta fito cikin shirin ta na doguwar riga dayake yanzu kayanta duk dogaye ne saboda ciki, zama tayi kusa da salman tace my man nafa shirya tashi ka kaini naga my little Allah yarinyar tashiga raina da yawa fa. Kuncinta ya shafa yace nasani tashi mutafi.

Address d'in suka bi har suka isa gidan da ke area 11, gaban gidan suka tsaya sukayi horn. Gate man ne yazo ya bud'e masu shiga sukayi cikin gidan,,,

     "little ce ke wasa da ball, ganin mota ya tsaya tabi motan da kallo "Aysaah na fitowa little tatafi da gudu tana anty "ware hannu aysaah tayi da gudu little ta k'arasa wajen aysaah Rungumeta aysaaah tayi sosai,,

D'agota Aysaah tayi tace i miss u so much my baby, murmushi little tayi tace miss u more my anty. Shidai salman binsu yayi da kallo yana dariya "Anty naba daddynah labarinki yace yanasan yaga anty nah Aysaah tace my little dadynki zai ganni yau amma ga uncle can jeki gaidashi. Da gudu ta fad'a jikin salman tana uncle am sowee banganka baneba murmushi yayi ya shafa kanta yace dama ya za'ayi kiganni kina tare da antynki...

Dariya little tayi ta k'ara sunne kanta jikin salaman,,,

hannun Aysaah little taja suka shiga cikin gida tana kwalama mammy kira, Fitowa mammy tayi tace yadai? Bata k'arasa ba taga Aysaah tsaye rungume juna sukayi suna murnan ganin juna ..

Hanan tace maman twinse ina uncle salman? Dariya tayi tace yana mota Hanan tace kika barshi waje? Oya little jeki ce uncle d'inki ya shigo...

Salman ne ya shigo da sallama yana rik'e da hannun little wuri ya samu ya zauna. Gaisawa sukayi da hanan, masu aiki ne sukw cika gaban su Aysaah da kayan ciye ciye kala kala "Hanan tace kun ko ci sa'a daddyn little yana nan bari namashi magana...

Dawowa tayi parlorn tace gashinan zuwa. Fira sukeyi sosai shikuwa salman hankalinshi yana wajen little dake ta mashi surutu...

Da sallama ya shigo parlorn amsawa salman yayi, "d'aga kan da aysaah zatayi suka had'a ido daidai shima salman ya kalleshi, a tare suka mik'e tsaye Aysaah ke nunashi da yasa "nikaina *Deedoh* saida biro na ta fad'i.......





phirdauceejeebo.blogspot.com




*IG: yar_ficika*




© *Feedoh Deedoh*✍🏻✍🏻

Comments

Popular posts from this blog

RASHIN GATA 176-180

RASHIN GATA 1-5

DIJAH 241~245