KUNYA ADON MACE 181~185

*KUNYA ADON MACE*

*_Feedoh yanmata_*✍🏻

*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*
® *(NWA)*

*_page_*1⃣8⃣1⃣ *_to_*1⃣8⃣5⃣

   Zaune muke a parlor nida Daddy, ita kuma Maamah na kitchen. Kuka muka fara ji a d'akin Ablah, da gudu muka isa d'akin muka tarar da ita kwance tana hawaye, Daddy ne ya d'agota ayayin da Maama ta shigo d'akin."
       Kallonta Daddy yayi yace, "Ablah mike damunki?" Kasa magana tayi sai kuka da takeyi, ga numfashinta na fita ba daidai ba. Maamah tace, "yanzu ba lokacin tambaya bane ba, mu d'auketa muyi asibiti da ita."

     Mota na d'auko su Maama suka sakata ciki, asibiti muka nufa da ita. Muna shiga asibitin nurses suka karb'eta sukayi ciki da ita.
       Kusan minti talatin saiga Doctor ya fito daga d'akinta. Kallon Papa yayi yace, "ina san ganinku. Gaba d'aya" atare muka nufa d'akin doctor, da sallama muka shiga. Amsawa yayi yamana izinin zama, saida yagama yan rubuce rubucen shi kana ya kalli Daddy da murmushi yace, "Alh dama tana da Athma ne?" Girgiza kai Daddy yayi yace, "gaskia bata da Athma."
    Doctor yace, "toh gaskia Athma ce ke damunta, amma yanzu da sauk'i mun yi mata allura kuma tasamu bacci." Godia Daddy yayi yace, "doctor zamu iya ganinta?" Doctor yace, "eh" nan muka tashi muka nufa d'akin da Ablah take. Kwance take tana bacci amma numfashinta ya koma normal.

     Zumbur Maamah ta mik'e tsaye, kallonta Daddy yayi yace, "lafiya?"
   "Wallahi nabar gas kunne" ta amsa.
    Da sauri na mik'e Papa yace, "garin ya haka?" Kallon Papa nayi nace, "yanzu ba tym d'in tambaya bane ba bari naje gidan." Maamah tace, "jirani Asad muje tare" girgiza kai nayi nace, "Maamah bari naje in shaa Allah ba abinda zai faru."
        Ina isa layin gidan mu na fara ganin hayak'i, amma nakasa yarda gidanmu ne. Saida na isa "tabbas gidan mu ne" abinda nake fad'a kenan, mutane nagani tsaye harma an kashe wutan.  
     Aljihuna na laluba na d'auko waya dan na kira Daddy amma da mamaki banjita ba, tunawa nayi dana barta gida, dole na juya asibiti dan na gayama su Daddy. Ina shiga d'akin Maamah ta mik'e tana tambaya na "Asad miyafaru?" Kasa magana nayi saida Daddy yaman magana. Kallonsu nayi nace, "gidan ya k'one komai na gidan yazama toka." Salati Daddy keyi, saida ya natsu kana yace, "muje na gani."

   Bayan kwana biyu aka sallami Ablah. Kallon Daddy Maamah tayi tace, "yanzu ina zamu?" Murmushi Daddy yayi yace, "ai tuni na sama mana gida, har ma an saka kaya." Murmushi Maaama tayi tace, "shikenan."

    Tun da muka koma gida nake neman hanyar da zata had'ani daku bansamu ba, gashi gabad'aya wayoyinmu sun k'one.
        Su Daddy na tarda parlor shida Maamah, na zauna. Kallo na Daddy yayi yace, "yadai akwai magana bakink" Murmushi nayi nace "eh daddy dama ina san naje Nigeria ne saboda su Aysaah nasan zasu nememu." Daddy yace, "nima nayi tunanin haka dan haka sai kayi arranging komai zuwa jibi saika tafi"
     Godiya nama Daddy na mik'e cikin murna. Da murna na, na iso Nigeria, ina sauka airport na d'auki drop na gaya mashi inda zai kaini, abin mamakin muna isa bakin gate na tambayi mai gadi yace man gaskia shi bak'one. Nace dan Allah ya taimaka yaman magana da masu gidan. Jim kad'an wani saurayi ya fito cikin sakin fuska muka gaisa, na mashi bayani, ceman yayi gaskia kun tashi, dan Babanshi ne ya siya gidan. Nace mashi ko yasan inda kuka koma? Yace gaskia baisani ba, kuma tsohon maigadin bai dad'e da daina aiki ba.
      Haka na dinga yawon neman ku a gari amma bansamu ba, dole na hak'ura na koma Cairo cikin bak'in ciki.

   Kullum cikin hanyar bincike muke ko zamu ganku, amma shiru har na hak'ura. Wata rana naje na samu Daddy akan inason ya barni na dawo Nigeria da zama ko Allah yasa na ganku, Daddy yace zai amince amma sai nayi aure, nace, "daddy nikam banda wadda nakeso amma idan kana da wadda tamaka ka had'ani da ita." Murmsuhi Daddy yayi yace, "ina da ita zan had'aka da d'iyar abokina kuma tana da hankali sosai."

   Ba'a d'auki wani lokaci ba akayi bikinmu da Hanan, bayan biki muka dawo Nigeria da zama. Kullum cikin yawon neman ku nakeyi amma Allah baisa na ganku ba sai yau sanadiyar little."

Babu wanda baiji tausayin Asad ba, ita ko Aysaah harda kuka tayi.. Papa yace, "Alhamdulillah dama haka Allah ya tsara abinshi kuma gashi daga k'arshe mun sake had'uwa."
    Waya Asad ya jawo ya kira Daddy ringing biyu Daddy ya d'auka. Da murna Asad ke gaya mashi ya gasu Papa, murna sosai Daddy yayi yace abawa Papa, gaisawa sukayi sosai da murnan k'ara ganin juna, Daddy yace, "Alhaji muna nan zuwa next week muganku." Papa yace, "kubarshi sai Allah ya sauki Aysaah lafiya sai kuzo."

   Sai dare su Asad suka bar gida, "Salman ne ya kalli Aysah yace, "Madam mutafi ko?" Ammi tace, "ina? Ai tazo kenan yaro saita kuma haihu cikinta ya shiga wata tara ba inda zata, dan haka ka kwaso mata kayanta" tashi Salman yayi yana gunguni, Haka yafita.

  Washe gari suna zaune parlor sai ganin sukayi ana shigo da kaya. Salman ne ya shigo da sallama, amsawa sukayi  wuri ya samu ya zauna gaidasu yayi, Ammi tace, "malam yadai? Naga kaya haka da yawa." Murmushi yayi yace, "ai Ammi mun dawo kenan sai randa kika maida man matata." Yana kai wa nan ya mik'e ya fita, dariya Mummyn Zarah tayi tace, "ai ga irinta nan kin hana yaro matar shi" tab'e baki Ammi tayi tace, "saidai yadawo amma Aysaah sai ta haihu ko tana komawa."



Phirdauceejeebo.blogspot.com

*IG: yar_ficika*


© *Feedoh Deedoh*✍🏻✍🏻

Comments

Popular posts from this blog

RASHIN GATA 176-180

RASHIN GATA 1-5

DIJAH 241~245