KUNYA ADON MACE 111~115

*KUNYA ADON MACE*

*_Feedoh yanmata_*✍🏻

*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*
© *(NWA)*

*_page_* 1⃣1⃣1⃣ *_to_*1⃣1⃣5⃣

Zaune take haraban asibitin tana latsa waya doctor ne yazo round yana zuwa wajen gadon aysaah ya ga batanan, ammi da tafito daga toilet ya kalleta yace hajia ina patient d'ina murmushi tayi tace ay tuni tafita haraban asibitin wai bazata k'ara zama ba tunda ta warware dan haka saika sallameta dariya yayi sosai yace karta damu hajia yau zanyi discharging d'inta..

Ammi ce ta kirata a waya, shigowa tayi tana ihun da ta sabayi a gida bata kula da wanda ke d'akin ba ta k'araso da gudu ta fad'a kan ammi d'agota ammi tayi taja hancinta tace naji dad'in ganin ki haka d'iyata Allah ya k'ara maki lafia "kamar daga sama taji ance amin juyawa tayi ta kalleshi tace ammi nah bakiceman doctor na ciki murmushi yayi yace idon ki ya rufe baki ganni ba fad'awa tayi jikin ammi tana dariya, doctor yace toh my patient yau zan sallameki dan naga kin samu sauk'i harkina yawo ciki  asibiti.....
              ★★★★★★★★★
"Dariya aysaah tayi tace ah ah fa kawai naje ganin yanda asibitin take, "takarda ya mik'oma ammi yace gashinan na sallamar d'iyarki dariya ammi tayi tace na gode doctor da irin kulawan da kaba my one nd only dota murmushi yayi yace bakomai ammi aysaah ay k'anwa tace nima kallon aysaah yayi yace rigimammar ammi sainazo ganinki ko shigewa tayi cikin jikin ammi tana dariya, shima dariyan yakeyi.....
        ◆◆◆◆◆◆◆◆◆◆◆◆◆◆◆◆
Waya ammi ta kira papa ta gaya mashi an sallamesu "papa ne da salman sukazo d'aukansu tunda salman ya shigo aysaah ta daina fara'a shikuma sai janta yake da wasa amma bata kulashi, "kallon ammi yayi cikin damuwa yace amminmu kinga dai babynki tunda ta warke tadaina kulani pls ammi idan laifi na mata kice tayi hak'uri dafashi ammi tayi tace karkadamu my boy ba kamata komai ba kasan bata da isasan lafiya amma zaku koma normal kasan kaida ita ba'ajin kanku....

*```BAYAN KWANA BIYU```*
Aysaah ta warke sosai amma tunda suka dawo ta fita harkan salman shikuma abun na damunshi, yau ne su mummyn ablah zasu koma salman ne ya shigo d'akin aysaah da sallama amsa mashi tayi amma bata d'ago ta kalleshi ba "zama yayi kusa da ita yace baby doll zanje kd maida su mummy amma 2days zanyi indawo shiru tayi bata ce komai ba tashi yayi ranshi b'ace ya fita yakai bakin k'ofa aysaaah tace Allah ya kiyaye ka gaida sahr juyowa yayi ya kalleta amma inda yake bata kalla ba. Yana fita itama ta fita zuwa tayi tai bankwana  dasu ablah kana ta dawo d'aki...

"Ammi ce ta shigo d'akin aysaah na ganinta ta tashi taje ta rungumeta magani ammi ta bata tasha. Kiran sunanta tayi wanda dataji ammi ta kirata to maganan na da muhimmanci amsawa tayi da naam ammi tace magana nakeso nayi dake dan haka kiban hankalinki. "Waye kikeso? D'agowa tayi da sauri tace ammi ni? Ammi tace eh ke girgiza kai tayi tace ba wanda nakeso fa ammi murmushi ammi tayi tace kuma k'arya bata maki kyau ba tabbas nayi zargin akwai wanda kika kamu da sanshi amma shi baisani ba kuma ke *KUNYA* ta hanaki ki fad'a mashi sai gashi zargina ya zama gaskia saboda randa kika farfad'o kin fad'i wasu maganganu wanda ya nuna akwai wanda kikeso. "Tashi ammi tayi ta k'araso kusa da ita tace aysaah idan baki fad'aman damuwanki ba wa zaki fad'amawa dalilin damuwa yasa kika shiga halin da kike yanzu dan Allah ki daure ki fad'aman waye kikeso nikuma namaki alk'awarin bakishi indai yana da halin kwarai, "aysaah tace ammi nifa ba wanda nakeso saidai idan zafin ciwo ne, "Ninasan wanda aysaah keso ammi gaba d'aya suka kalli k'ofan haneefa ce tsaye ta had'e hannuwa k'arasowa tayi tace ammi nasan wa aysaah ke so kuma yau zan gaya makishi kodan ta fita halin da take ciki.....

Aysaah da sauri ta d'ago ta kalli haneefa tace haba bestie karmuyi haka dake pls, Allah ammi karki saurareta k'arya takeyi ni ba wanda nakeso, "dafata haneefa tayi tace bestie kiyi hak'uri dole na fad'ama ammi waye kikeso saboda nasa tana da magani matsalanki, nagaji da ganinki cikin damuwa aysaah dole tasa zan karya alk'awarin dana d'aukar maki kodan ganin d'orewan lafiyanki, "kallon ammi tayi tace ammi dama bawani aysaah ke so ba illa.......


*Hannuna ya kasa idawa kuman hak'uri my people gobe zakuji komai. lurv u all my sweeries*





Phirdauceejeebo.blogspot.com





*IG: yar_ficika*


© *Feedoh Deedoh*✍🏻✍🏻

Comments

Popular posts from this blog

RASHIN GATA 176-180

RASHIN GATA 1-5

DIJAH 241~245