KUNYA ADON MACE 11~15

Feedoh_* *_yanmata_*✍🏻

*_page_* 1⃣1⃣ *_to_*1⃣5⃣

Zaune take tanata shafan wayanta tana murmushi, takai 20mnts tsaye amma batasan tana wurinba, tsaki tayi ta fizge wayan, d'agowa tayi da masifa tace hanifa miye haka, ina ruwanki da wayana, hanifa tayi tsaki tace kedai aysaah saikin gyara, tun yaushe nake wurinnan amma bakisan nazo ba gaba d'aya hankalinki yana kan photo, ina amfanin haka, Allah idan bazaki gyara ba saina gayama ammi, jin an ambaci ammi tace haba my bestie miye kuma harsai kingaya ma ammi, kinasan asirina ya Tonu, murmushi hanifa tayi ta samu wuri ta zauna, dafa ta tayi, tace aysaah ina da shawaran da zanbaki, gyara zama aysaah tayi tace inajinki bestie, tace why not kisameshi ki gayamashi kina sanshi, zaro ido aysaah tayi tace infad'a mashi fa kikace d'aga kai hanifa tayi tace I mean it, girgiza kai aysaah tayi tace kada Allah yakawo randa zance inasan namiji shin kinmance karin maganan hausawa da suke cewa *KUNYA* *ADON* *MACE* yanzu nasameshi nace inasanshi taya zai d'aukeni banda kunya kenan, zancigaba da dakon sonshi har sai randa da kanshi yace yana sona, amma nikam I can't Idan ma ammi nah taji saita yi fushi dani, "tab'e baki hanifa tayi tace shikenan dama shawara ce nabaki, tunda kink'i d'auka muje kawai,,,,

           "Tsaye take kitchen tana d'auraye kayan datayi girki dasu, wani k'amshi taji wanda bazata iya mantawa ba, aranta tace Ya salman harnafara mafarkin turarenka, takowa akayi akazo bayanta, jin k'amshin yak'a k'aruwa yasa ta juya, ganin wanda yake tsaye yana mata murmushi yasa ta Saki baki, idanuwanta ta murza kana ta bud'e ganin ba mafarki baneba, yasa taje da gudu ta fad'a jikinshi shiko ya rungumeta,  cikin siririyan muryanta tace Ya Salman kaine? Murmushi yayi yace nine my baby doll, shagwab'a tafarayi mashi, ni gaskia nayi fushi, shine kak'i gaya muna yaushe zaka dawo, salman yace sowee my baby doll, sonake nayi surprise d'inku shiyasa, amma on mah kneels bazan k'araba, zatayi magana Ya d'aura hannunshi kan lab'b'anta yace shhhhhhh don't say anything, murmushi tayi yaja hannunta sukayi d'akin ammi,,,,
                    ********
"Suna shiga d'akin ammi aysaah tafara ihu, duk tabi ta cika gidan, tafiya tayi ta fad'a kan ammi, ammi tace my babe karki karyani, zumb'uro baki aysaah tayi tace ammi nah duka nawa nake, dariya salman yayi yace kunfi kusa, ke aysaah shiyasa kuke fad'a da mummynzarah saboda ihunki, zumb'uro baki tayi tace ammi kinajinshi, ammi tace Salman ka kiyayeni kadawo kenan zakasaman baby gaba, duk yanda tayi missn d'inka amma daga dawowanka zakasa tarame, murmushi yayi yace ayi hak'uri ammi nd mummy's pet, dariya ammi tayi sukaci gaba da hira, aysaah tace ya Salman ina tsarabana, Salman yace tsarabanki na nan my baby doll, hakadai sukaci gaba da fira, Salman nabasu labarin rayuwan skul na dariya suyi dariya na tausayawa su tausaya, basu tashiba saida aka kira magrib kana kowa Ya mik'e dan gabatar da farali,,,,,

             "Sun had'u daining suna cin abinci, mummy ta duba bataga Salman ba, mummynzarah tace zarah tashi ki kira yayanku yazo yaci abinci, Kafin ta tashi salman yace mummynah gani nan, murmushi tayi tace naga banganka baneba, wuri yasamu yazauna, da kanta mummynzarah ke serving d'in salman, saidata zuba mashi wadatacce kana ta koma ta zauna, salman yace tnx so much my mummy, murmushi tayi tace ur welcum my son, "suna gama cin abinci salman yace nifa zantafi na kwanta bacci nakeci mummynzarah tace ay yakamata, dayake daddy yayi tafiya, aysaah tayi narai narai da fuska tace bruh tsarabana fa, mummynzarah tace saikizo ki kwata, murmushi yayi Ya shafa kanta yace afuwan my baby gobe zanbaki kinji, d'aga kai tayi alaman to, harara mummynzarah ta wurga mata, jawota ammi tayi jikinta tace kyalesu my babe su suka sani dariya yayi yawuce d'akinshi...

"Yana tafiya itama ta kwashi wayoyinta tama ammi saida safe, ammi tace Allah yakaimu my baby u make sure kinyi adua kinji, d'aga kanta tayi ta wuce ko kallon inda mummynzarah take batayiba, dan tasan suna had'a ido zata wurga mata harara, "tana hayewa sama tayi shirin kwanciya kit d'inta tajawo ta d'auko hoton tana dubawa, murmushi takeyi tace inama zakasan irin sanda nake maka, da katausayaman inama kazama uban yayana danafi kowa murna da haka, saiga hawaye sun wanke mata fuska share hawayen tayi ta maida hoton ta kwanta tayi lamo har bacci ya d'auketa,

Nasan masu karatu sun matsu suji waye wannan da aysaah ta mutu kanshi, dan da Alama shibaima san tanayiba, toh nima dai haryanzu nakasa samo amsar amma kudai cigaba da bina zakuji waye wannan saurayin....

*HAPPY* *SALLAH* *IN* *ADVANCE* *MY* *BEAUTIFUL* *PEOPLE*❤

Phirdauceejeebo.blogspot.com

© *Feedoh* *Deedoh*✍🏻✍🏻

Comments

Popular posts from this blog

RASHIN GATA 176-180

RASHIN GATA 1-5

DIJAH 241~245