KUNYA ADON MACE 46~50

*KUNYA* *ADON* *MACE*

*_Feedoh_* *_yanmata_*✍🏻

*_page_*4⃣6⃣ *_to_*5⃣0⃣

Zaune take parlor tayi d'ai d'ai tanacin popcorn sallama yayi tashi tayi da gudu ta rungumeshi saikuma ta sakeshi ta fashe da kuka ta nufa d'akinta da gudu hankalin Salman yatashi ganin baby doll d'inshi na kuka, d'akin ya bita kodayaje kwance ya isketa kan gado tana kuka, d'agota yayi ya share mata hawaye sunanta ya kira cikin muryanshi mai sanyi kamar ta *SAURAYINAH* lolzz d'agowa tayi ta kalleshi miyasaki kuka ko baki murnan dawowa ta ba idan baki murna ba inkoma dasauri ta d'ago tace ah ah bakai baneba tunda katafi baka kirani ba ka mance da ni kanata harkanka, murmushi yayi aysaah kenan saunawa kina ganin miskal d'ina amma baki d'aga ba nifa yakamata nayi fushi dake amma dayake kinsan ban iya fushi dake shiyasa banyi zumb'ure baki tayi ayni kaima laifi kaban hak'uri kumatunta yaja yace am sowee toh my baby doll murmushi tayi ta fad'a kanshi ya rungumeta, "kefa yanzu ba yarinya baceba kin girma yakamata ki rage shigema salman harkina rungumarshi kinsan ba muharraminki baneba keko muharraminki ne baikamata ba saboda kinsan addininmu baiso Allah yayi hani da haka dan haka shiyasa nake k'ara jan kunnenki daki daina shigema namiji koma waye bawai salman kad'aiba koma waye bakuma zarginku nakeba kawai saboda dukkaninku yanxu balagaggu ne maganganun ammi ne suka dawo mata da sauri ta janye jikinta murmushi yamata yace yanaji gidan shiru inasu mummynah da ammi nki, suntafi suna sukuma su zarah suna islamiyya, kafin yak'ara magana wayanshi tayi ringing ganin wadda takirashi yasashi murmushi tashi yayi yace baby doll big bruh fa yanajin yunwa dan haka anema mashi abinda zaici......
             ***********
Tana tashi da safe ta shirya mashi komi as usual kana ta shiryan cikin doguwar rigan material sallama tayima ammi ta nufa makaranta kusan tare suka shiga skul da haneefa suna ganin juna suka rungume juna aysaah tace bestie ya Salman fa yadawo jiya murmushi hanifa tayi tace ashe jiya munyi babban bak'o shine baki kirani nazo natayaki had'a mashi delicious ba murmushi tayi tace kinsanshi da surprise nima kawai ganinshi nayi "ehen bestie kinsan mi? Girgiza kai tayi wannan guy d'in asad yake kowa ashe ranan binmu yadingayi harya ga gidanmu, basai gashi ba cikin k'aguwa hanifa tace yakukayi dashi kafin tabata amsa lecturer ya shigo bari muganma lecture zan fad'amaki.....

       "Suna gama lectures d'insu suka nufa cafteria dan suci abinci saida sukagama kana haneefa tace bestie inajinki, kwashe komai aysaah tayi tagayama haneefa sannan tace wlhi haneefa baccin zuciyata na riga dana sadaukar da ita kan Salman nd kuma nama kaina alk'awarin idan ba Salman ba bazan tab'a aure ba dana saurari asad saboda shima namijine ajin farko saidai bazan iyaba itadai haneefa kallonta takeyi saida tagama kana tayi ajiyan zuciya tace duk naji magananki ki cigaba da adua Allah yamaki zab'i mafi alkairi amma kidaina cewa wai idan baki auri salman ba bazaki aure ba shifa ba'ama Allah dole saiya hanaki salman d'in kuma kinsan iyayenki bazasu samaki ido ki k'iyin aure ba, dan haka adua itace mafita wajenki....

"Sallama sukaji akansu gaba d'aya suka d'ago asad ne tsaye yanata masu murmushi "murmushi haneefa tamashi kana ta gaidashi amsawa yayi cikin sakin fuska  kallon aysaah yayi yace pretty can I sit? D'aga mashi kaitayi tnx yace yaja kujera ya zauna tashi haneefa tayi tace bestie kisameni hall kafin taji abinda zatace hartayi gaba, juyowa tayi tana kallonshi murmushi yamata itama tamaida mashi martani gaidashi tayi amsawa yayi cikin jin dad'i  kallonta yayi yace pretty Allah dai yasa ba b'ata maki rai nayi ba ranan danaje gidanku wlhi harna koma gida ina tuhumar kaina da sanya pretty kuka murmushi tayi tace ba ruwanka, asad yace ranan namaki magana baki ceman komai ba, d'agowa tayi cikin sanyin murya tace asad kayi hak'uri kabari sai gobe zangaya maka komai da dalilin da yasa nake kuka kaga yanzu tym d'in lecture ya kusa gobe muhad'u nan wajen 11:am "kallonta yayi cikin tausayawa yace Allah yakaimu tashi na rakaki, har gaban hall d'insu yakaita kana sukayi bankwana ta shig cikin lacture hall shikuma ya juya yatafi. Suna gama lecture haneefa ta kalleta tace ya kukayi dashi babu komai saidai gobe zamuyi magana dashi amsar data bata kenan suka wuce wajen mota dan tafiya gida.....





Phirdauceejeebo.blogspot.com

*IG* : *yar_ficika*





© *Feedoh* *Deedoh*✍🏻✍🏻

Comments

Popular posts from this blog

RASHIN GATA 176-180

RASHIN GATA 1-5

DIJAH 241~245