KUNYA ADON MACE 146~150

*KUNYA ADON MACE*

*_Feedoh yanmata_*✍🏻

*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*

*_page_*1⃣4⃣6⃣ *_to_*1⃣5⃣0⃣

Yau aka fara bikin aysaah da salman inda sukayi bridal shower amarya ta sha kyau harta gaji shi kanshi angon idan ka ganshi baka gane shi sabo da kyau, ga k'awayen amarya suma sun sha kyau inda sukayi ankon red polo sai sweatpant, duk wanda yaga amarya da ango sai sun burgeshi saboda kyau...

Sai dare aka tashi a gajiye suka dawo gida "tunda suka shigo salman ke kiran wayanta..

Tana d'agawa yace inasan ganinki bai jira mizatace ba yakashe waya...

Tagumi tayi haneefa ce taxo ta zare mata hannu ajiyan zuciya aysaah tayi ta kalli haneefa tace Allah bestie rigiman salman tana ban mamaki haneefa tace miyayi? Wai yanasan ganina kamar ba yanzu muka rabu ba "murmushi haneefa tayi tace toh saikije..

Zaro ido tayi tace so kike ammi ta balbaleni da masifa Allah bazanje ba nasan dai fushi ne idan yagaji ya daina. Tana gama magana taja blanket ta kwanta...

Tunda suka tashi suke ta faman shirye shiryen kamu 4:00 pm daidai aka fara tafiya saboda papa yace baisan suyi dare nan ma ancashe anyi watsi da naira "saidai ango na fushi da matarshi da sun had'a ido sai ya harareta ita abunma dariya yake bata...

" *FRIDAY*
Saadah bamblee ce kema amarya makeup gaskia fad'in kyan da amarya tayi b'ata lokacine nabar maku masu karatu ku auna da kanku "karfe 8:00pm aka fara tafiya dinner..

Amarya ce da angonta bisa high table idan kagansu sai sun burge ka saboda irin kyan da sukayi. "Wasu yan mata ne masu ji da kansu su biyar suka shigo hall d'in..

Haneefa ce da sauri taje ta rungumesu tana murna "rookie sadau dama zakuzo ayna d'auka bazaku zo ba "wadda aka kira da rookie sadau tace mizai hanamu zuwa kallon haneefa tayi tace meet my sisters ummu bassam, softie, husnah nd fadeelah rungumesu haneefa tayi tace sannunku "suko sai ya tsina sukeyi..

Rookie sadau tace banga rookiey kaxs ba da jeeddah ja'oh haneefa tace gasu can..

Karode bello ne yafara wasa bayan ya gama umar m sharif shima yayi nashi "can naga rookiey kaxs nd deeyerh sunyi d'amara da gyalensu suna rawa😂😂

biki yayi biki kowa yaci ya k'oshi dan softie harda take away🤔 sai 12 :00 aka tashi daga dinner kowa kagani zaka ganshi da bag mai d'auke da hoton amarya da ango....

```22/10/2016```
*Hausawa sunce Rana bata k'arya saidai uwar d'iya taji kunya.*
Yau asabar daidai da 22/10/2016 aka d'aura auren aysaah da salman akan sadaki naira dubu d'ari da hamsi inda dubban mutane suka shaida "harda shugaban k'asa ya halarci d'aurin auren. Ana gama d'aurin aure aka tafi hilton danyi reception...

Tunda aka cema aysaah an d'aura aure ta kulle kanta k'uryan ammi tana kuka "ba kukan komi take ba yanda yau aka d'aura aurenta amma asad baya nan..

Saida ammi tayi dagaske kana aysaah ta bud'e d'akin..

Ammi na shiga d'akin ta wuce toilet tahad'ama aysaah ruwan wanka "zuwa tayi ta kama hannunta ta kaita bakin toilet amma tak'i yarda su had'a ido..

Saida ta juyo tace kiyi wanka akwai wasu magunguna na zamane ki tabbata da kin xauna su nd idan kika fito ga wasu nan a cup d'innan suma kisha su tana kaiwa nan tafita batako juyo ba...

Tana shiga toilet ta cigaba da kuka saida tayi mai isarta kana ta fara wanka...

Tayi duk yanda ammi ta umurce ta tayi, tana fitowa daidai su haneefa da mufeedah suna shigowa, kaya ta aje bisa gado tace gashi nan inji ammi tace ki sasu kuma ki shirya da wuri dan yan d'aukar amarya suna kan hanya..

Suma suna fad'a suka fita dan kowace kuka takeyi...

Tana cikin shiryawa k'anwar mummynzarah ta shigo d'akin kallon aysaah tayi tace kingama shiryawan? D'aga mata kai tayi alamar "eh"..

Alkyabba ta mik'a mata ta saka kana ta kama hannunta suka fito...




Phirdauceejeebo.blogspot.com



*IG: yar_ficika*


© *Feedoh Deedoh*✍🏻✍🏻

Comments

Popular posts from this blog

RASHIN GATA 176-180

RASHIN GATA 1-5

DIJAH 241~245