KUNYA ADON MACE 26~30

*KUNYA* *ADON* *MACE*

*_Feedoh_* *_yanmata_*✍🏻

*_page_* 2⃣6⃣ *_to_*3⃣0⃣

Alh sadeeq shine mahaifinsu asalin shi  d'an k'auyen katsina ne bugaje anan yayi makarantarshi firame da secondary bayan yagama yatafi ABU zariya ya karanta civil engineering bayan yagama karatunshi yadawo gida anan iyayenshi suka aura mashi safiyya wadda d'iyace ga liman d'in garin, daga nan yasamu aiki a abuja ya tattara iyalanshi Yakoma Abuja da ita shekara shidda Allah bai bata haihuwa ba abun yadameta sosai shiko bai damu ba saboda yasan yin Allah ne asibiti sunje kuma antabbatar masu lafiyansu lau su duka, ita tamatsamashi ya k'ara aure amma yak'i amincewa har fad'a sukayi, "daga k'arshe dai ya amince yana wata kwangila  a kaduna Allah ya had'ashi da nafisa, suka daidaita kansu nan aka sha biki itama ta tare gidanta Abuja itama shiru shiru bako b'atan wata har aka shekara yafara zargin kanshi da shine bai haihuwa Ana cikin haka Allah yaba safiyya ciki zokaga murna wajen iyalan alh sadeeq hardai nafisa saikace ita keda cikin saboda irin zaman lafiyan da sukeyi zaka rantse da Allah ba kishiyoyi baneba wata Tara chur safiyya ta Haifi santaleliyar d'iyarta mace sankowa k'in Wanda ya rasa zokaga murna, "rannan suna yarinya taci sunan aysaah bayan suna gaba d'aya renon aysaah ya koma wajen nafisa komai nata wajenta yake idan kaganta wajen safiyya toh nono zatasha, bayan haihuwar aysaah da shekara hud'u Allah ya sake ba safiyya ciki ta Haifi zarah, ba'ayi arba'in ba itama nafisa tasamu nata rabon wata Tara tahaifi rahma daga nan haihuwar ta bud'e mata ta k'ara haihuwar sameer sai yar autarsu basma daga Nan babu wadda tasake haihuwa cikinsu, alh sadeeq yaba yaranshi tarbiya da ilimi daidai gwargwado "kasancewar aysaah yar fari yasa safiyya bata janta ajikinta idan ba amfad'a ma mutaneba basu cewa safiyya ita tahaifi aysaah "Aysaah ta sakama safiyya mummynzarah saboda tace bata kula da ita sai zarah take cema nafisa Ammi, dan tace nafisa ce mamarta    yanzu haka aysaah shekararta 18 tana karatu a nail university Abuja inda take karanta law tana year 1  sukuma zarah da rahma na js3 sameer na js1 basma na primary 4, "aysaah irin matannan ne da ake kira coca cola saboda shape d'inta gata fara ga dukiyar Fulani Allah yabata sometimes mutane na danganta kyan aysaah da Rani mukhreji idan aysaah tayi dariya zaka rantse da Allah rani ce maza nakawo mata hari a skul a kan hanya amma ko kallonsu batayi saboda anata cewar zuciyarta ta Riga ta mallakama dream guy d'inta, wanda ita kad'ai tasanshi......
              ************
*WAYE* *SALMAN* *?*
Salman d'an sister Ammi ce su biyu ne wajen iyayensu daga mamar salman sai ammi tun suna yara iyayensu suka rasu sunsha wahalar duniya, wajen kishiyar uwa har Allah yakawoma mamar Salman hajia binta miji tayi aure koda tayi aure bata bar nafisa ba da ita tatafi acan kaduna tayi makarantarta, watan hajia binta goma da aure Allah yabata haihuwa inda tahaifi santalelen d'anta ranan suna aka sakamashi salman, tun Salman yana jariri komi nashi ammi keyinshi kodaya ya girma shak'uwa mai k'arfi tashiga tsakaninsu baida abokiyar shawara sai ammi daganan hajia binta tasake haihuwa ta haifi d'iyarta mace aka saka mata mufeeda, "lokacin da ammi zatayi aure da kyar aka raba Salman da ita sunba kowa tausai har asibiti ya kwanta daga k'arshe dai aka tambayi mijinta yace bakomai amaidoshi shima aymai rik'e Salman ne mafarin dawowar Salman kenan gidansu aysaah...

                "Tun dawowar salman gidansu aysaah renonta Yakoma hannunshi komai yasamo baby doll saida ta girma tasan ba d'an gidansu baneba, amma shak'uwarsu kullum k'aruwa take lokacin da zaitafi England karatu da kyar aka rabasu, tunda yatafi tadawo shiru shiru abun har yafara damun ammi itako mummynzarah ba ruwanta harkanta takeyi da sauran yara, dakyar ammi tasamu aysaah tasake....
              *********
"Tunda salman yatafi karatu aysaah take fama da tunaninshi kullum saita kalli pics d'inshi take samun sauk'i tun batagane sanshi takeba harta gane sanshi take randa tagane tayi kuka babu wanda yasan tana san salman sai bestie d'inta haneefa, kuma ta d'aukarma kanta alk'awarin bazata tab'a gaya mashi ba saboda ita macece kuma ansan mace da kunya, zata dinga renon sanshi harsai randa da kanshi ya gaya mata idan kuma bai gaya mata ba saidai ta mutu da sanshi kuma baza tab'a aure ba "tunda aysaah tagane san salman take tayi alk'awarin k'ara kyautata mashi kuma pictures d'inshi su suka zama abun kallonta safe dare da rana, su kad'ai ke rage mata damuwa da kuma kewar masoyin nata.....

To masu karatu kunji wacece aysaah kuma kunji waje dream guy d'in nata....


Phirdauceejeebo.blogspot.com

*IG*: *yar_ficika*


® *Feedoh* *Deedoh*✍🏻✍🏻

Comments

Popular posts from this blog

RASHIN GATA 176-180

RASHIN GATA 1-5

DIJAH 241~245