KUNYA ADON MACE 96~100

*KUNYA ADON MACE*

*_Feedoh yanmata_*✍🏻

*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*
    ® *(NWA)*

*_page_*9⃣6⃣ *_to_*1⃣0⃣0⃣

Duk'awa ammi tayi tace pls aysaah ki tashi dan Allah karki mutu kibarni saikuma ta saka kuka, da sauri papa da mummynzarah sukayo kan aysaah d'aga masu hannu ammi tayi tace karku k'araso wajen nan dama aybaku son kuga tana rayuwa duka aysaah nawa take da za'ace dole saitayi aure yanzu toh gashinan ta barmaku duniyar sai ku zuba ruwa k'asa kusha kuma wlhi idan aysaah ta mutu nagama zaman gidannan, "mummynzarah burin ki ya cika kinyi sanadiyar raba d'iyarki da kika haifa da cikinki da  duniya saiku ciga ba da rayuwanku kuda wanda kukeso. Dukkansu jikinsu yayi sanyi "tashi tayi ta je ta kira driver da taimakon driver suka saka aysaah mota suka nufa hanyar asibiti papa ne ya kalli mummynzarah datayi tagumi yace gaskia nafisa ta fad'a mana kuma kalamanki kan yarinyar nan yayi tsauri bansan mita maki ba kin tsaneta kefa kika haifeta yanzu ba dan Allah yasa ta samu marik'iya mai tsoron Allah ba yakika gani yakamata ki farka kija d'iyarki jikinki ki bata kulawa kamar sauran yaranki yanzu an wuce wannan zamanin k'auyancin nasan bazata sake da ke ba kamar yadda take sakewa da nafisa amma ki dinga bata kulawa koyane, "numfashi taja tace yanzu ba lokacin wannan maganan baneba tashi mu bisu asibitin.....
               ********
Suna isa asibitin da sauri ammi tafita taje ta samu nurses ta masu magana gadon tura marassa lafiya aka d'ora aysaah turata akeyi ammi na biye na sharan hawaye, ana zuwa k'ofan wani d'aki aka tsaida ammi shiga akayi da aysaah ciki "su papa ne suka k'araso asibitin reception suka iske ammi tanata safa da marwa ga hawaye suna bin kuncinta, mummynzarah ce ta tako tazo kusa da ita dafa kafad'anta tayi tace ammi dan Allah kiyi hak'uri kidaina kuka tabbas nasan bana kyautawa abinda nakema aysaah amma wlhi bawai bansan ta baneba kawai ina kawaici ne akan tana d'iyata tafari kuma kina tsaye kanta baikamata nina dinga shiga harkanta ba kuma maganan danayi d'azu nasan ban kyauta ba saboda irin tarbiyan da kika ba ma aysaah koni dana haifeta iyakar abinda zanmata kenan dan Allah kiyi hak'uri ki yafeman, "d'ago idanuwanta tayi da suka rine suka zama ja saboda kuka tace shikenan mummynzarah ya wuce na yafe maki Allah ya yafemana baki d'aya itakuma Allah yabata lafiya nan suka rungume juna suna kuka saida papa ya masu nuni da asibiti suke....

*BAYAN AWA SHIDA*
Awan aysaah shida cur cikin d'akin marassa lafiya amma bawani bayani tun ammi na daurewa harta fara kuka da kyar aka samu tayi shiru, "likitoci uku ke kan aysaah dan ceto ranta amma abun yaci tura, alwallah ammi ta tashi tayi tayi nafila tafara nemar ma aysaah sauk'i....

Wani saurayi ne yafito mai kimanin shekara talatin adunia hand glop d'in hannunshi ya cire "wata nurse ya tambaya yace ina iyayen patient d'innan nuna ammi tayi, karasowa likita yayi ya mik'ama papa hannu yace alh kardai ace d'iyarka ce papa yace wlhi d'iyata ce girgiza kai doctor yayi yace toh Alh ina san ganinku office d'ina. Tashi sukayi suka bishi office d'inshi da sallama suka shiga amsa masu yayi kana yace su zauna....
             *********
Bayan sun zauna suka sake gaisawa rubuce rubuce doctor yayi kana ya d'ago kallon papa yayi yace alh wacece mahaifiyar yarinyar ammi ya nuna doctor ya kalleta da kyau yace hajia garin ya akayi d'iyarki takamu da ciwon zuciya haka mai tsanani a razane ammi ta d'ago tace ciwon zuciya? Doctor yace eh d'iyarki ta kamu da ciwon zuciya sakamakon akwai abinda takeso bata samu ba kokuma tana gab da rasa abun kuma gaskia idan harta rasa abinda takeso kuma ta cigaba da saka damuwa a cikin ranta to zafa ta iya rasa rayuwarta dan yanzu haka da kyar muka samu muka daidaita bugun zuciyan ta kuma aman jinin ya tsaya tunda nake amsar patient bantab'a cin karo da na irin d'iyarki ba "in banda kuka ba abinda ammi keyi shiko alh gumi yake sharewa ita kanta mummynzarah saida tayi kuka doctor yace Alh ku kwantar da hankalinku zata samu sauk'i in shaa Allah tunda yanzu mungano kan matsalan, amma gaskia idan ta cigaba da saka damuwa a zuciyanta toh fa nan ba da dad'ewa ba zata iya rasa rayuwarta saboda zuciyanta ta raunana. Papa yace in shaa Allah bama zata rasa ba zamuyi iyakar k'ok'arinmu doctor yace yawwa, alh yace zamu iya zuwa muganta dr yace eh saidai kar ayi hayaniya saboda halin datake yanzu batasan hayaniya. "Godiya sikama doctor suka tashi suka fita....





Phirdauceejeebo.blogspot.com

*IG: yar_ficika*




© *Feedoh Deedoh*✍🏻✍🏻

Comments

Popular posts from this blog

RASHIN GATA 176-180

RASHIN GATA 1-5

DIJAH 241~245