KUNYA ADON MACE 116~120

*KUNYA ADON MACE*

*_Feedoh yanmata_*✍🏻

*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*

*_page_*1⃣1⃣6⃣ *_to_*1⃣2⃣0⃣

Ammi ba wani aysaah ke so ba illah salman, da sauri ammi ta d'ago salman? Eh ammi salman duk halin da aysaah ta shiga na son salman ne ammi aysaah ta fara san salman tun batasan miye so ba tun randa aysaah ta gane tana san salman tayi kuka kamar ta cire ranta............haneefa ta kwashe komai ta gaya ma ammi ba abinda ta rage mata, "d'agowa ammi tayi ta kalli aysaah dake faman kuka dafa kafad'anta tayi tace tabbas kin cika yar halak kuma nayi alfahari da samunki a matsayin d'iya so da yawa ina tunanin dama ni na haifeki nasan zan yi alfahari dake, fad'awa tayi kan ammi tace ammi yanzu ma zaki alfahari dani kumani banda wata mama bayan ke, "d'agota ammi tayi ta share mata hawaye tace nagode Allah da kika rik'e kunyarki saboda *KUNYA ADON MACE CE* nakumaji dad'i yanda baki bari salman yagane shi kikeso ba, salman da kanshi zaizo yace yana sanki, haneefa kema nagode kin cika k'awar arzik'i Allah ya maku albarka, tashi ammi tayi tabar d'akin fad'awa aysaah tayi kan gado tana dariya hannefa tafara zolayanta d'iyar ammi kuka ya k'are daga yau.....
             ★★★★★★★★★★
Alh kaduna nakeso naje gobe amma idan nasamu yanda nakeso goben zandawo ammi ce ke fad'ama papa kallonta yayi cikin mamaki yace kaduna kuma ina cewa yau yan kaduna suka tafi mi zakijeyi? Mumnyzarah tace ah ah alh kabarta taje mayb akwai abun da zai kaita mai muhimmanci shikenan Allah ya kiyaye hanya, amin suka amsa "ammi tace yawwa kafin aysaah ta tashi natafi amma dan Allah mummyzarah kartayi wasa da maganinta nd idan tace ina naje kuce naje minna saboda bansan tasan inda zani, shikenan ammi in shaa Allah za'ayi yanda kikeso......

◆◆◆◆◆◆◆◆◆◆◆◆◆◆◆◆◆◆◆◆◆◆◆◆◆◆◆
Tunda ammi tayi sallar asuba bata koma ba shiryawa tayi k'arfe takwas ta fito daga d'akinta daining area ta samu su mummynzarah gaidasu tayi kana tasamu wuri ta zauna abinci sukeci suna fira saida ta gama tsaf ta kalli mummynzarah tace toh mummynzarah ga amanar d'iyata nan na yau kawai dan Allah ko tsawa kar amata papa yace bazan bari amata ba ammin aysaah godiya tayi ta tashi har wurin mota suka rakata, juyowa tayi tace idan babynah ta tashi taci abinci tasha magani kuma idan ta tambaya inda naje ace naje minna yau zandawo, in shaa Allahu, xanyi yanda kikeso godiya tayi tashiga mota driver yaja sai kd fatan Allah yaba ammi sa'an abinda taje nema amin.....

"Cikin shigan k'ananan kaya ta fito parlor taci karo da mummynzarah gaida ta tayi takuma amsa cikin sakin fuska tare da tambayan ya k'arfin jiki da sauki tace "tashi tayi ta nufa d'akin ammi aysaah zonan yauce ranan farko da mummynxarah taji ta ambaci sunanta dawowa tayi ta zauna kallonta mummynzarah tayi tace amminki taje minna amma yau zata dawo, kwalla tafarayi shine bata tadani muka tafi tare ba kallonta mummynzarah tayi tace bakida lafiya shiyasa itama taso tafiya dake amma ciwonki yahana amma yau zata dawo, yanzu tashi kije kici abinci kisha magani "dan dole aysaah ta tashi idan ta tsaya gardama yanda takema ammi tasan bazataji da dad'i ba.....
★★★★★★★★★★★★★★★★★
```12:30pm```
sha biyu da rabi su ammi suka isa horn akayi maigadi ya wangale masu mota shiga sukayi haraban gidan suka samu wuri sukayi parking, "fita tayi ta nufa cikin gida da sallama mummyn mufeedah na ganinta ta taso da sauri ta tari yar uwarta tana tambayanta lafiya? Murmushi ammi tayi tace lafiya lau anty hamdala mummyn mufeedah tayi, "saida ammi taci ta k'oshi kana ta kalli mummyn mufeedah da daddy tace anty alfarma naxo nema wajenku anty tace wace iri ce yar uwata fad'aman indai batafi k'arfinmu ba zamuyi maki "zama ta gyara tace anty kunsan dai aysaah ba tada lafiya ko? Eh sukace a tare toh ba komai baneba ciwon aysaah illa............. Ta kwashe komai ta gaya masu tasowa tayi tazo kusa dasu ta durk'usa tana hawaye tace anty dan Allah inasan salman ya auri aysaah wlhi anty bansan ganin aysaah cikin damuwa "d'agota anty tayi ta share mata hawaye gyaran murya daddy yayi yace haba nafeesa ay kuke da hukunci da salman wlhi duk yanda kukayi dashi duk d'ayane nikaina na mashi kwad'ayin aysaah saboda kyawawan halayarta. Anty tace haba autan mama kinsan duk abinda kikeso shi nakeso dan haka salman baida wata mata bayan aysaah rungumeta ammi tayi tana godiya. Daddy ne ya d'auki waya yakira salman yazo yanzu sunasan ganinshi....

"Salman ne ya shigo da sallama ganin ammi zaune yasa ya saki baki tashi tayi ta kamoshi tana dariya my boy toh rufe bakin dariya shima yayi zama yayi ya gaidasu, daddy ya kalleshi yace mamanku dama kesan magana da kai shine tazo, kallon ammi yayi "tashi ammi tayi tazo kusa dashi tace alfarma nake nema rufe mata baki yayi yace ammi kifad'i abinda kike buk'ata nikuma zanzama mai biyayya a gareki, "kauda kai tayi tace so nake ka auri aysaaah da sauri ya d'ago yace ammi aysaah? Eh ita nakeso ka aura marairaicewa yayi yace Allah ammi bata sona kigafa yanda ta canjaman kwana biyu dafashi ammi tayi tace aykai zaka koya mata sanka my boy, "kallon iyayenshi yayi yace toh mummy daddy sahr fa? Daddy yace nayi bincike kan yarinyar iyayenta ba dattawan arxik'i baneba dama yau nakesan namaka magana akanta "shikanshi yasan abinda mahaifinshi ya fad'a gaskia ne iyayenta ba dattawan arzak'i baneba dan yanzu haka bat 9ja wai tatafi london weekend kuma ita kad'ai, "kallon ammi yayi yace shikenan amminmu zanyi yanda kukeso, rungumeshi ammi tayi tana shimai albarka......

"D'aki ya shiga ya rasa abinda yake mashi dad'i waya ya d'auka ya kira sahr amma da mamaki wani namiji ya d'auka salman yace waye? Saurayinta ne abinda aka bashi amsa kenan, kuma hutu tazoman karka k'ara kiranta kabari har sai tadawo. Kashe wayan salman yayi ya tura mata sak'o akan shi kam bazai iya aurenta ba tunda dama halin da take ciki kenan da mamakinshi yaga reply d'inta da ok.... Kwance yake yana tunanin aysaah komi nata yadawo mashi a memory duk abinda ya tuna saiyayi dariya "tabbas babu wadda ta dace da tazama matata sai aysaaah toh miyasa banyi wannan tunanin ba sai yanzu aysaah fa batasanka kaga yanda ta canja maka hawaye suka gangaro mashi wata zuciyan tace karkadamu kaifa namiji ne kaizaka koya mata sanka.....

Sabon layinshi ya d'auko yamata sms kamar haka, ```salam aysaaah nasan bakisan waye ba toh mijinki ne in shaa Allah wanda yadad'e yana dakon sonki ki saurareni gobe da misalin 8:00pm zan bayyana maki kaina. Lurv u so much my future wife,``` sending ya mata "tashi yayi ya nufa d'akin mummy ammi yagani da mummy kallon ammi yayi yace ammi gobe zanje ga matata dan karwani ya rugani ba ammi ba koni *yarficika* yaban dariya, ammi tace karkadamu tare zamu tafi gobe, baka gaya muna ya kayi da sahr ba ya b'ata fuska yayi yace gaskia ba matar aure baceba yanzu haka tana india wai vocation kuma dana kirata wani namiji ya d'auka yanaman warning dana mata text akan bazan  iya auren ta ba tunda haka halinta yake reply taman da ok.. Ammi tace Allah shi kyauta. Dan haka ammi na amince da zab'inku aysaah tazama matata, rungumeshu ammi tayi tana shimashi albarka....







Phirdauceejeebo.blogspot.com




*IG: yar_ficika*


© *Feedoh Deedoh*✍🏻✍🏻

Comments

Popular posts from this blog

RASHIN GATA 176-180

RASHIN GATA 1-5

DIJAH 241~245