KUNYA ADON MACE 186~190

*KUNYA ADON MACE*

*_Feedoh yanmata_*✍🏻

*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*
® *(NAW)*

*LAST EPISODE*

*_page_*1⃣8⃣6⃣ *_to_*1⃣9⃣0⃣

*BAYAN SATI BIYU*
        Aysaah ce kwance bayan Ammi ji tayi cikinta yana ciwo Mik'ewa tayi zaune. Farkawa Ammi tayi ta ganta zaune Ammi tace, "my Baby lafiya?" Murmushi Aysaah tayi tace, "nothing Ammi". Ammi tace, "toh koma ki kwanta, kwanciya tayi ta rufe idonta kamar tana bacci, amma ba barci takeyi ba..
      Can taji cikinta ya k'ara murd'awa, Ammi ta fara kwalama kira da sauri Ammi ta farka tace, "Aysaah miye?" Kasa magana tayi sai cikinta da take gwadama Ammi, tashi Ammi tayi ta fita da sauri, shigowa sukayi ita dasu Mummynzarah da Salman. Kama Aysaah akayi aka sakata a mota, in banda salati ba abinda Aysaah keyi.."

        Suna isa asibiti aka shiga da Aysaah labour room. Ammi ce ke zagaye zagaye tana ta adua, yayin da Salman ke hawaye, Dafashi Papa yayi yace, "Haba Salman be a Man mana, akanmi zaka dinga kuka a yanzu Aysaah adur'amu take nema ba kuka ba, dan haka share hawayenka". Hawayen shi ya share.
      Kusan awa guda tunda aka shiga da Aysaah ba wani labari. Ammi ce ta kalli Papa tace, "gaskia nikam abin nan na bani tsoro ace haryanzu shiru." Murmushi Papa yayi yace, "karki ce haka kowa da yanda yake haihuwan shi kedai kawai mucigaba da yimata adua."
      Likita ne ya fito yana cire handgloves d'inshi, gaba d'aya suka mik'e sukace, "likita ta haihu?" binsu yayi da kallo yana murmushi, mik'ama Salman hannu yayi yace, "congrats my man matarka ta sauka lafiya kuma ta samu d'iya mace". Nan aka fara murna kowa da abinda yake cewa..

      Suna Shiga d'akin sukaga Aysaah kwance, ita kuma babyn na gadon jarirai, har rige rigen d'aukan baby'n akeyi tsakanin Ammi da Salman, ita kuwa Mummyn Zarah ta zama yar kallo. Papa ne ya karb'i d'iyar ya mata adu'a. mik'ama Salman yayi yace, "sai kai mata hud'uba" wajen gadon Aysaah Salman ya matsa peck ya mata a kunci yace, "nagode sosai my baby doll da kika haifaman mace mai kama dake, dan haka yanzu na baki zab'i ki fad'i sunan da kikeso a saka mata." Murmushi tayi tace, "nagode sosai matso na gaya maka." Matsawa yayi ta mashi rad'a murmushi yayi yace "angama hajia nah." Sudai iyayen binsu sukayi da kallo suna murmushi.

     Tun cikin daren aka fara fad'ama mutane Aysaah ta haihu.
      Washe gari Likita ya sallami Aysaah da yake ba wata matsala, koda suka isa gida cike suka tar dashi da mutane kowa na murna. Asad da Hanan ma sunzo. Tunda Little taga Baby shi kenan ta koma wajen Aysaah ko fita batayi.

      Haihuwa da kwana uku yan Cairo suka iso, kowa
yayi murnan ganin d'an uwanshi, gida ya cika yan Kaduna suma sunzo.

    Yau monday daidai da 07/11/2016 akayi suna, inda yarinya taci sunan Ammi, Nafeesa amma za'a dinga kiranta da *ASBAN*, Ammi taji dad'i sosai dan har kuka saida tayi kowa yayi murna da aka sama baby sunan Ammi.
      K'arfe hud'u na hango Aysaah taci ado cikin super red, d'inkin ya karb'eta, shiga ta dingayi cikin mutane ana gaisawa kowa da gifts d'in da yake bata.
yan NAGARTA na hango
sun shigo gidan sunan cikin shiga ta alfarma, Aysaah na hangosu taje tayi hugging d'insu, ciki tayi dasu tana nuna ma Ammi ga yan groups d'insu. Sha tara ta arzik'i k'ungiyar Albarka NAGARTA tayima Aysaah, taji dad'i sosai itama ta bisu da tukuici.
Sai dare aka gama taron su na, kowa ya koma gida cikin farin ciki.

   Aysaah ce zaune parlon Ammi tana cirema Asban pampers. Salman ne ya shigo parlon, Ammi na ganinshi ta d'aure fuska tace, "ranka yadad'e lafiya?" Duk'ar da kanshi k'asa yayi yace, "Ammi nazo ganin sune." Abin dariya yaba Ammi, tashi tayi tace, "na baka 20mnt tana kaiwa nan ta fita."
     Zama yayi yana gunguni, dariya abin yaba Aysaah amma ba halinyi. Kallonta yayi yace, "yarinya komawa gida zakiyi basai kingama wanka ba, dan wannan takuran ya isheni." Dariya tayi ta fad'a jikinshi, d'agowa Aysaah tayi tace, "Salman kullum ina alfahari dakai da ka zama uban 'ya'yana Allah ya k'ara had'a kanmu." Rungumeta yayi yace, "Aysaah a yanzu kinzama wani abu daga cikin jikina." D'aga hannu sama yayi yace, "Allah na rok'eka ka raya Aysaah da abinda zata haifa kabani abinda zan ciyar dasu na halak. Aysaah ta amsa da Amin, had'asu yayi ya rungume ita da Asban yana murmushi....

Anan zan aje biro na...

Godia ga Allah subahanu wata'ala da yabani ikon gama wannan littafin. Kura kuren dake cikinshi Allah ka yafeman...

Godia ta gareku bata da iyaka NAGARTA WRITERS ASSOCIATION, mungode sosai yanda kuke had'a kanmu, Allah yabar k'auna. luv y'all..."

Godia mai tarin yawa ga yan group d'inmu FEEDOH & BIEBIE  FANS, Allah yabar zumunci.."

Na sadaukar da littafin nan gareku, Aysha misau (big sis) da Zarah B~B nagode sosai da irin kulawarku akaina..

Wannan littafin goro ne ga duk masoyana wanda na sa ni da wanda bansani ba, na gode da irin soyayyarku gareni Feedoh loves u my sweetos

*JINJINA GARE KU*
Hauwa Jabo
Benaxir Omar
Lubabatu sani Mai Tafseer
Autar Hajia
Anty ybk
Munaysha
miss Hafcy
Sdy Jegal

*wanaan littafin tukuici ne gare ku*
MIEMIEBEE
Stylish Bch
Biebie Isa (Tawan)
Jiddah AKA Quee (Tweety)
Khadeeja Candy (Deedee)
Damary
Jiddah Ja'o
Ummu bassam (Mummyn admin)

*K'awayen kirki*
Husna Msharif
Queen bilqees
Miss softie
Fadeelah
FeenahS
Rookiey Kaxs
Lollita
Yesmeen tafeesu
Nafeesa Gambo
Zee Sifawa
Safiyya Binji
Aneesa Anush
Rama Mtn
zee Labo

*KUNA RAINA*
Zarah Sani Mai Cassette
Hauwa Bello
Maryam Ladan Shuni
Nimcy
Surayya Saeed
Its Riko
Sadeeya Yuguda

*Godiya ta gareku*
Anee lurv
Nafee Anka
Esha tsafe
Hafsat rano
Ya hajja (hajja ce)
Ummy agoss
Hajar
Anty Amina K'aura
Anty Carofee
sadeeya Marafa
Uwar Taslim

Da duk wanda ban kiraba, kuna raina..

Sai kunjini a littafi na gaba.

Any comments or correction, Here my digit
08037791855
Text only

Lurv u all my people❤

Comments

Popular posts from this blog

RASHIN GATA 176-180

RASHIN GATA 1-5

DIJAH 241~245