KUNYA ADON MACE 66~70

*KUNYA ADON MACE*

*_Feedoh yanmata_*✍🏻

® *NWA*

*_page_* 6⃣6⃣ *_to_*7⃣0⃣

Tana shiga gida parlor ta iske yan gidansu da gudu ta isa ta fad'a kan ammi tana murmushi tace ammi nah i miss u so much, d'agota ammi tayi tace my babe ayni nayi fushi dake, "a shagwab'ance tace kiyi hak'uri ammi nah, kallonta ammi tayi tace wasa nake maki my dota aybaki laifi, murmushi tayi tace ammi nah  nagode, shafa kanta tayi tace shhh karki damu my baby, peck  tama ammi tace datz y i lurv u, lurv u more juyawa tayi tace mummyn zarah ina wuni amsa mata tayi fuska sake abin ya bata mamaki dan tunda take bata tab'a ganin ta mata fara'a ba sai yau, katseta ammi tayi tace tashi kije d'aki kiyi wanka ki huta mik'ewa tayi tana tambayarsu ammi ina su zarah, mummyn zarah tace sunje saloon basma kuma sunfita da salman, murmushi aysaah tayi tace yau ya salman ya bani kenan dan sai auta ta naka sa mashi aljihu, dariya sukayi su duka.....

"Haka dai rayuwa ta cigaba da wakana, wajen aysaah kuma babu abinda takeso sai randa salman zai gaya mata yana santa kullum adu'anta kenan, shiko salman soyayya mai k'arfi ta shiga tsakaninshi da sahr dan yanzu bai wuce 2weeks bai je kd ba, kuma duk abinnan bai gayama aysaah yana da budurwa ba....
                ********
Asad ne zaune gaban iyayenshi yace daddy yanzu dole sai munkoma cairo da zama? Wlhi bansan nayi nesa da aysaah tana buk'atar taimkona pls daddy nidai ku barni nan zan dunga zo maku hutu, dafa kanshi yayi yace kayi hak'uri asad nikaina ba yanda zanyi ne kasuwanci na ya koma can kuma kaima na samo ma ka aiki can d'in kaga tafiya dakai ya zama dole kaje kafara shirye shire nan da 3dayz zamu wuce, zai k'ara magana maaah ta d'aga mashi hannu tace bansanka da yima mahaifanka musu ba kaje kayi abinda mahaifinka yace, kaga ablah itama jibi zata wuce kuma kasan bazata so ace anbarka 9ja ba tunda kasan yanda kuke kai da ita, tashi yayi yana hawaye yawuce d'aki.....

"Asad ne gaban ammi yana gaya mata yana hawaye, ita kanta ammi batasan wannan tafiyan saidai dole yabi umurnin mahaifanshi, daurewa ammi tayi tace haba asad miye toh na kuka cigaba fane kasamu kayi hak'uri indai aysaah ce baka da matsala zan lallasheta yanda zata fahimce ka, zai k'ara magana sukaji sallamar ta amsawa ammi tayi tana shigowa ta iske asad zaune murmushi ta mashi tace hi bruh shidai ya kasa d'agowa, kallon ammi tayi tace ammi yadai? Jawota ammi tayi tace my babe ki bud'e kunnenki ki saurari abinda zan gayamaki da kyau kinjini ko? D'aga kanta tayi alamar eh, ammi tace dama daddyn asad ne d'azu yacema asad ya shirya nan da 3days zasu wuce cairo kuma sun koma can da zama kenan, mik'ewa tayi tsaye tace noh ammi wasa ya asad ke maki saikuma ta  fashe da kuka, matsowa tayi gabanshi tace haba ya asad miyasa zakaman haka kasan yanzu kaine gatana saida kabari na saba dakai shine zakaman haka yanzu shikenan nikadai zan cigaba da rayuwa saikuma tafashe da kuka shima kukan yake, itadai ammi ta saka masu ido saida sukayi mai isarsu kana ammi ta lallashesu takuma fara yimasu nasiha harta samu suka sauko, "ranan sukuku aysaah ta wuni ko abinci ta kasaci......

*BAYAN KWANA UKKU*
        "Tsaye yake yana masu ammi bankwana salman zai kaishi airport dan olrdy su maaah sunwuce, can zai samesu airport, rugowa tayi da gudu ta fad'a jikinshi tana kuka, pls ya asad karkaman haka karka tafi kabarni kadaure ka cigaba da zama dani, d'agota yayi ya share mata hawaye yace haba my lilsis tafiyana baya na nufin mun rabu kenan ba ah ah zan dinga zuwa ganinki kuma zamu dinga waya kidaina kuka pls kinsan bansan kukan ki, share hawayenta tayi yace yawwa gud gal kokefa, ki tabbata kafin nazo ganinki kun daidaita da suruki nah saboda dana dawo aure zanmaki, sunne kai tayi tana dariya, hannunta ya kamo yazo gabansu ammi da ita, kallon mummynzarah yayi yace mummy nasan dama keda d'anki salman kuke takurama sis d'ina dan kunga amminmu bata magana, pls mummy ga amanarta nan na barmaku adaina mata fad'a dan Allah murmushi mummyn zarah tayi tace idan tayi abun fad'a zanmata, asad yace i trust my pretty bama zatayi ba, kallon salman yayi yace bruh ga amanata nan na barmaka ka kularman da k'anwa kamar yadda kake kula da kanka, bansan tayi maraicin yaya, dafashi salman yayi yace karka damu bruh zanyi yanda kakeso, "wani akwati ya d'auko daga cikin mota ya mik'a mata yace my sis karb'i, amsa tayi tana kallon akwatin, agogon hannunshi ya duba yaga jirginsu yakusa tashi, peck ya mata ya juya yamasu ammi bankwana ya fad'a mota, shima salman shiga yayi yama motan key suka wuce yana d'aga masu hannu, da gudu tayi cikin gida tana kuka mai tsuma rai.......



Phirdauceejeebo.blogspot.com

*IG*: *yar_ficika*

© *Feedoh Deedoh*✍🏻✍🏻

Comments

Popular posts from this blog

RASHIN GATA 176-180

RASHIN GATA 1-5

DIJAH 241~245