KUNYA ADON MACE 121~125

*KUNYA ADON MACE*

*_Feedoh yanmata_*✍🏻

*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*
  ® *(NWA)*

*_page_*1⃣2⃣1⃣ *_to_*1⃣2⃣5⃣

Wayanta taji tayi k'ara alamun sak'o ya shigo dubawa tayi da mamakinta taga new number da kamar bazata bud'eba wata zuciyan tace aysaah bud'e bakisan waye ba k'ilama asad ne, karanta sms d'in tayi tunani tafara waye wannan kuma? Kodai salman ne ah ah ba salman baneba saboda ya salman bai da wannan number toh waye wannan? Amsar da takasa samu kenan "kibari gobe zakiga kowaye tunda yace zai bayyana maki kanshi ah ah aysaah karki saurareshi kinga ammi ta maki alk'awarin salman zai kawo kanshi toh kibari koma waye gobe zaki ganshi duk zuciyanta ce ke gaya mata haka, "aje wayan tayi ta cigaba da harkokinta...

"Tunda ta tashi take jin wani farin ciki wanda bata tab'ajin irin shi ba duk wanda ke gidan yagane tana cikin farin ciki, mummynzarah ce ta kirata amsawa tayi kallonta tayi tace babyn ammi yadai naganki cikin farin ciki haka "fad'ad'a dariyanta tayi tace mummyn zarah saboda ammi na zata dawo yau ne shiyasa, murmushi mummynxarah tayi tace toh tashi ki gyara mata d'akinta amsawa tayi da toh ta tashi....

"Karfe biyar ammi ta iso aysaah najin horn ta tashi da gudu taje ta taro ammi, rungumeta ammi tayi d'agowa aysaah tayi tana kuka amminah shine kika tafi kika barni kuma baki bari mukayi bankwana ba "share mata hawaye ammi tayi tace haba babynah kinfa girma yanzu kidaina kukan banza keda zanma aure soon rufe fuskanta tayi tana dariya "hannunta ammi taja sukayi cikin gida tanata ma ammi shagwab'a parlor suka iske mummynzarah da fara'a ta tari ammi mummynzarah tace ammi daga dawowanki anfara maki shagwab'anko murmushi ammi tayi tace kinsan tayi missn d'in mamanta dariya mummynzarah tayi tace toh sannu da dawowa ay yanzu zaku cigaba daga inda kuka tsaya murmushi ammi tayi tace mummy kinfa sa muna ido dariya tayi tace na bari. "bayan ammi taci abinci ta huta aysaah ta bata sms d'in da aka mata ta karanta cz bata b'oyema ammi komai, murmushi ammi tayi saboda tasan waye, Allah yakaimu *8:00pm* d'in muga waye "da sauri aysaah ta d'ago tace ammi kin amince naganshi kenan? Eh mana my babe kiganshi kuma ki shirya mashi delicous d'in da kika saba had'ama yayanki kinjinko? shikenan ammi nah zanyi yanda kikeso ur wish is my command ammi tace gud gal Allah yamaki albarka amarya, tashi tayi da sauri tafita d'akin tana dariya.....

Waya ta d'auka ta kira mummyn haneefa kan tabar haneefa tazo ta mata weekend ba wata gardama dayake mummyn haneefa tasan yan gidansu aysaah har zumunci sukeyi, "ba'a jima ba haneefa ta k'araso da gudu aysaah taje ta tarota rungume juna sukayi suna murna, "d'aki suka wuce aysaah ta gayama haneefa komai murmushi haneefa tayi dan ita kanta tasan bak'on bai wuce salman...

Kitchen suka shiga suka fara aiki suna aiki tana murmushi d'aka mata duka haneefa tayi tace murmushin mi kike? ita kanta ta rasa fara'an miye yau takeyi fried d'in couscous sukayi wanda yaji kayan had'i sannan su kayi coslow pepper meat sukayi, coconute drink suka had' ta saka a fridge bakwai daidai suka gama komai mai aikinsu ta kwalama kira tana zuwa tace gani uwar d'akina aysaah tace zanyi bak'o k'arfe takwas da yazo kikaimai abincinnan kafin nazo kinji, angama uwar d'akina he wishing is me kwamad dariya aysaah tayi sosai itako haneefa har fad'uwa takeyi saboda dariya, tace haba biebee wai yaushe zaki waye ne? Waya gaya maki haka ake cewa b'ata fuska biebee tayi tace toh ay saiku gyaraman toh naji cewa akeyi ur wish is my command yawwa, dariya aysaah keyi harta bar kitchen d'in......
          ★★★★★★★★★★★
Tana shiga d'akinta ta fad'a kewaye wanka tayo tazo ta tsaya gaban madubi da yake tana fashin sallah "tsintar kanta tayi da yin makeup "light makeup tayi kana ta feshe jikinta da turaruka gaban wadrobe d'inta taje wata riga red wadda ammi ta siyo mata ta d'auko ta saka kana ta feshe ta da turare rolling tayi da scarves kallon kanta tayi a madubi masha Allah nikaina *feedoh yanmata ta burgeni nasan da rookiey kaxs ce ta iya gayu haka bazata k'ara yimuna magana ba lolz* itadai haneefa ido ta sakama aysaah saboda abun na bata mamaki, "takwas daidai sms ya shigo wayanta ```ina parlorn bak'i``` abinda aka rubuta kenan murmushi tayi tace lallai wannan yacika ji dakai baima iya kirana.....

"sauka tayi ta nufa parlorn bak'i tana isa bakin k'ofa gabanta yafara dukan uku uku sallama tayi ta shiga "tsaye yake ya juya baya shiru akayi ba amsa saida ta k'ara sallama kana ya amsa cikin husky voice d'inshi "juyowa yayi ya kalleta kanta k'asa yake batama san ya juyo ba "takowa yayi yazo gabanta kamar daga sama taji yace baby doll d'agowa tayi da sauri tabbas ba mafarki takeba salman ne gabanta dama salman ne ya mata sms? "Hannunta yaja ya zaunar da ita kallonta yayi yace miye na dogon tunani nine gabanki salman ne ur lurvly broda, saboda tsaban rud'ewa aysaah ta kasa cewa komai.....

Idonta ya hura da sauri ta lumshesu peck ya mata a kunci "kiran sunanta yayi yace aysaah amsawa tayi a hankali da naam "tashi yayi yace aysaah nasan zaki mamakin ganina ko? Toh karkiyi mamaki ba abinda ya gagari Allah zuwa yayi ya duk'a kusa da ita hannunta yakamo yace aysaah yau ga salman gabanki da k'ok'on baranshi kuma sai yanda kikayi dashi  aysaah ina sanki kuma inasan kizama mother to my unborn child "hawayene suka gangaro mata saboda ko amafarki batayi tsammanin salman zaiso ta ba amma yau shine gabanta yana neman ta soshi, "share mata hawaye yayi yace yanzu ba tym d'in kuka baneba aysaah...

Kitaimaki d'an uwanki ki soshi na maki alk'awarin zansaki farin ciki har k'arshen rayuwata "d'agowa tayi ta kalleshi kashe mata ido yayi da sauri tayi k'asa da ido "ya salman naji amma kabari zanyi tunani komi kenan l'll let u knw "

Ah ah aysaah ba tunani tsakanin mu just tell me nasamu shiga koko? Tashi tayi ta kalleshi tace ya salman aysaah ta mallakama zuciyanta sai yanda kayi da ita tana kaiwa nan ta ruga da gudu, lumshe ido yayi yace masha Allah gaskia am lucky guy "zama yayi yaci abinci yayi k'at kana ya nufa d'akinshi.......



Phirdauceejeebo.blogspot.com

*IG: yar_ficika*


© *Feedoh Deedoh*✍🏻✍🏻

Comments

Popular posts from this blog

RASHIN GATA 176-180

RASHIN GATA 1-5

DIJAH 241~245