JINSINAH 111~115
❄❄ *JINSINAH* ❄❄
*_Feedoh_* *_yanmata_*✍🏻
*_page_* 1⃣1⃣1⃣ *_to_*1⃣1⃣5⃣
Anyi taron an gama lafiya kowa yakoma gidanshi, "Anty aka bari saidata gyarama maijego gida, "kana ta d'auki suhaila suka tafi, "zaune take tana cirema Arif pamperz, yanata kuka, nono tabashi yana kamawa yayi shiru, "sallama akayi muryan datajine yasa gabanta fad'uwa, saboda tunda aka sallamosu asibiti basu had'uba,,,,,,,,,,
"Fadilah ce tashigo da habiba, guri suka samu suka zauna, gaidasu finah tayi suka amsa cikin sakin fuska, "habiba tace maijego abamu yaron mugani, mik'amasu yaron rayi, karb'a habiba tayi tace Masha Allah, yaron mai kyau dashi, "mik'ama Fadilah tayi, amsa tayi tace Allah yarayaka, itadai finah batace komai ba, "habiba ce tace finah kamar baki sake damuba kiyi hak'uri abinda yafaru ya riga da yafaru, plz kiyi hak'uri komai yawuce, "finah tace nidama ban ruk'e kukba, Allah ya yafemuna baki d'aya Fadilah tace amin, "fira suka d'anyi, kana Fadilah tamik'a mata arif tace bari mukoma, saikama na k'ara shigowa, finah tace nagode,,,,,,,,
********
Suna fita fadilah takalli habiba tayi wani shu'umammen murmushi,,,,
"Part d'in Hajia suka nufa suna zuwa kafin sushiga parlor Fadilah tabuga wani irin ihu, Wanda nikaina *Yar* *ficika* mai d'auko maku rahoto saida na zura aguje, ihu takeyi tana nashiga ukku na lalace, Umma ce tafito da gudu hartana tuntube, "kama Fadilah tayi tana tambaya lafiya itakuma Fadilah sai ihu takeyi, habiba nabata hak'uri, "hajiya takalli habiba tace miyafaru, "habiba tace dama d'azu ne da nazo nacema Fadilah mushiga muyima finah barka, hartace bazatajeba, nace ta daure mutafi aybakomi, "muna zuwa mukayi sallama ba'a amsa ba, mukashiga, muna shiga muka tarda su parlor itada wannan shegiyar antyn tata, zama mukayi ba wanda yakallemu, Fadilah tace dama finah ganin baby mukazo, "bud'an bakin finah tace toh saimi idan ganin baby kukazo, kina tunanin zanbaki d'anane wlhi ban iyaba juya d'ana wadda batasan darajan nak'uda ba bare haihuwa Allah ya tsareni daba juya d'ana, habiba tafashe da kuka, tace Umma ta zazzagemu ta had'a dake ta zage duka, waikema munafukace, wani salati Umma tayi, tace ayko yau zankawo k'arshen iskancin tubabbar nan,,,,,,,,
"Afusace Umma tayi part d'in finah, fadila takalli habiba sukayi dariya tace dama nagaya maki kedai tafi gida sai gobe idan nazo, habiba tace shikenan hajiya nah sai goben,,,,,,
"Kutsa kanta tayi cikin parlor bako sallama, kamar daga sama finah taji ance ke tubabba, d'agowa tayi ta kalli Umma, ganin Umma yasa gabanta nadakan ukku ukku, Fadilah ce tashigo part d'in tana sharan kwallan muna funci, "Umma tace naji sak'onki duka da wanda kikaman da kuma gorin da kikama Fadilah amma yau zanyi maganinki, "binsu finah tayi da kallo dan batama gane mesuke nufi ba, "moh ne yashigo da sallama ganin Umma da Fadilah yasan yau akwai tashin hankali gidan, "Umma tace Alhamdulillah dama ko baka dawoba yanzu zan kiraka a waya,,,,,,
**********
"Jiki sanyaye moh yace Umma lafiya mike faruwa, kawai Umma saita fashe da kuka, hankalin Moh yatashi yace Umma kima girman Allah kidaina kuka, "Umma tace ay kuka bazai k'are ba harsai dangin arna tabarman gidannan idan ba hakaba ni Zan barmata, moh hankalinshi yatashi yace Umma mike faruwa, ummah tace wai kamarni wannan shegiyar tubbabbar zata zaga kuma tayima Fadilah gorin haihuwa hartana kiranta da juya, "moh yace Umma waya gayamaki, Umma tace Fadilah da k'awarta kuma nasan bazasu mata sharri ba, "dan haka abinda nakeso dakai shine ka saki finah arazane moh yakalli Umma tace kwarai idan ba hakaba wlhi ni zanbarma gidan,,,,,,
Duk'awa moh yayi Yakama k'afan Umma yana bata hak'uri amma Ina saima k'ok'arin fizgewa datakeyi tabar mashi gidan, itako finah gaskia ma tamata yawa tarasa abinyi, "finah ce ta tako tazo gaban moh ta kalleshi tana hawaye tace my moh trust me sharri Fadilah keman, amma inasan kabi umurnin mahaifiyarka daka sakeni k'ila nima nasamu yanci gaba, "hawaye moh keyi yace finah bakida wani miji sai ni kima daina wannan maganan, finah tace Kama Allah kasakeni Nima na huta da azaba tunda nazo gidanna shekara guda kenan amma bansamu farin cikiba dan haka ka sakeni dan Allah,,,,,,,
"Kuka yaci k'arfinta juyawa tayi ta nufa d'aki Umma tamik'a mashi biro da paper tace yi abinda nasaka ka wlhi kona barma gidan, "amsa yayi, yayi rubutu ciki ya kanannad'e paper moh yace ummaa kiman alfarma kinga dare yayi sosai kibari da safe tatafi, Umma tace na rantse saitabar gidan yau d'innan,,,
"Finah tafito da trolley d'inta tazo gaban moh ta tsaya mik'a mata paper yayi amsa tayi tana kuka, shima kuka yakeyi, juyawa tayi tawuce takai k'ofa kenan Umma tace toh tubabba da kinyaye yaro zamu amshi kayanmu dan karya koyi wani addini da ba nashiba, "dawowa finah tayi tace Umma ko bakiceba zan maidoshi, kuma moh ne gashinan kizauna dashi Umma yamaki abinda yakeman, kinji ko idan har baki auri Muhammad ba baki cika mai kishinshi ba, "kekuma Fadilah da izinin Allah saikin girbi abinda kika shuka da hannunki, indai duniyace ta isheku daga ke har umman, kuma koda kuke kirana tubabba kowa yasan nafiku saboda kuda kuke ikirarin anhaifeku cikin musuluncin bakusan komai ba, "niko tubabba nasan abinda baku saniba, tana kaiwa nan tasaka kai tafita, ba Fadilah ba ko Umma tayi mamakin maganganun finah saboda ko kallonta bata yi, amma yau itace tsaye gabanta tana gaya mata bak'ak'en maganganu haryana cewa ta auri Muhammad,,,,,
"Koda tafito layin shiru saboda 10:30pm gashi unguwan ba mutane, tafiya takeyi ta rasa ina zata dosa, cikin ikon Allah saiga wani mai Napep yazo wucewa tsaidashi tayi yakuma tsaya, cemashi tayi rinjin sambo mai Napep yace 1k finah tace sutafi, tafiya suke gabanta yana dakan ukku ukku saboda yanda zata k'are da iyayenta, amma indai sun yards zasu k'arb'eta zatabar musulunci takoma addininta,,,,,,,,
************
"Suna isowa rinjin sambo tafara mshi kwatance harya kawota k'ofar gidansu, yana ajeta tazaro 1k d'inshi tabashi amsa yayi yana mata godia, kayanta ta d'auka ta nufa gidan gabanta sai fad'i yake, knocking tafaryi muryan babanta taji yana cewa waye shiru tayi, bud'ewa yayi ganin finah tsaye ya had'a rai yace Maman Claire fito kigani, fitowa tayi ta ga finah tsaye, babanta yace miyakawoki gidana, finah tace daddy he divorce me daddy yace so wetin concern mi? Aydama mungaya maki indai musulmai ne kije gaki gasunan, kuma kima amince dan haka, yanzuma bamu sankiba kiwuce kikoma inda kika fito, d'ukawa finah tayi tana basu hak'uri amma ina hankad'ata mummy tayi suka maida gida suka rufe,,,,,,,,,,
"Duk abinnan gaban mai Napep akayishi takowa yayi yazo gabanta ya d'uka yana bata hak'uri share hawaye tayi tace bakomai, mai Napep yace inbazaki damu ba nakaiki wajen mahaifiyata, girgiza kai tayi tace karkadamu kaidai kataimakeni ka kaini gidan yan uwana, mai Napep yace wace unguwa ce tagaya mashi, kayanta ya d'auka yasaka cikin napep d'in shiga tayi suka wuce bai tsaya ko inaba sai unguwar su amir, " suna zuwa sun kulle knocking tayi gate man ne ya lek'o ganin mace da goyo yasa yafito, cz shi new ne fitowa yayi yace Hajia lafiya, finah tace ciki zanshiga, yace wurinwa finah tace wajen masu gidan, maigadi yace baisan wannan ba, nanfa rigima taso ta kaure mai napep da gate man, "hayaniya amir yaji yafito, yana fitowa tambaya yayi lafiya, gateman yace wai wannan ce tace zata shiga gidansu ne nikuma bansanka da d'iya babba hakaba, amir yace dallah yoman shirk gidansu ne mana, finah lafiya cikin darennan haka , fashewa tayi da kuka tace Umma tasaka ya sakeni, amir yace saki, finah tace eh saki,,,,,,,,,,,,,,,,
*_Dedicated_* *_to_* *_biebee_* *_isa_* ❤
IG: yar_ficika
© *_written_* *_by_*
*_Feedoh_* *_Deedoh_*✍🏻✍🏻
Comments
Post a Comment