HUDAH 76~80
⭐⭐HUDAH⭐⭐
Na
Feedoh & Meesha lurv
7⃣6⃣~8⃣0⃣
Alh na fita yayi gurin motarsa har zai shiga sai ya tuna maganinta da zai siyo, nan ya rufe motar yaje ya siyo maganin ya yadawo, da "sallama" ya shigo d'akin dukansu basuji bud'e k'ofar ba sai "sallarmasa" sukaji amsa Mashi sukayi shigowa yaye jikinsa duk, asanyaye Dan duk wata irin kuyarsa yakeji, yana ijeye maganin ya juya zai fita, maaah ce tayi Mashi magana cak ya tsaya amma, be jiyo ba zuwa tayi kusa dashi ta tsugunna, tace masa Dan Allah alh wata alfarma nake nema indan zan samu, jiyuwa yayi yana kallonta kujerar robar dake d'akin ya janyo, " yazauna a kanta" sannan yad'ago ya kalleta yace "alfarma tami kike nema Hadiza" maah tace kayiman alk'awari zakayiman alh Dan Allah.
Shiru yayi kamar bazai ansa taba can dai ya nisa yace " inajinki Hadixa" nayi maki, alk'awari inde befi k'arfina, ba anyimaki shi maaah tace nagode alh, dama bawani Abu bane illar in a so, Dan Allah alh kada kasake kayima faruq magana ko kace zakayimashi wani Abu har duniya taji.
Badan komai nace haka ba kuwa shine, idan har kayiwa faruq magana dole kowa, na gidan yaji indan kuwa kowa, kaga kenan kuwa zaisan miyafaru da "HUDAH" nikuwa bani k'aunar kowa yaji wannan maganar Dan Allah Alh.
D'agowa Alh yayi sannan yace, " yaza kiyiman haka Hadiza" idan ba'ad'aukar HUDAH matakiba aka k'watar mata hak'inta ba itafa aka cuta kiyi tunani Dan Allah kada ki hanani d'aukar, " mataki" maaah tace nasan da haka Alh nidai kayiman wannan alfarmar, Alh yace naji amma kuwa inde haka ne, toh yazama dole ya aureta SBD shi yab'ata mata, rayuwa maaah tace na yarda da hakan inde baza tafad'a ba.
Tashi Alh yayi sannan yakalli maah yace mata naje, gida nadawo nan ya fita ranshi abace, HUDAH tad'ago kanta a hankali takalli maaah tace " maaah miyasa kika yarda da sai faruq ya aure ni maah?" Kinsan fa duk duniya bawanda ya tsana irina indan har ya aureni to daga ranar nayi banwana da farin ciki, wasu hawaye masu zafin suka zubomin maaah tazo kusa dani tace HUDAH yaza ma dole, kiyi hak'uri " ki anshi k'ad'dararki hannu bibiyu kinji" akwai dalilin da yasa nace na yarda Dan haka ki kwantar da hankalinki har Allah yabaki lafiya kinji HUDAH ta d'aga kaina kawai nayi sannan najuya mata baya na kwanta nayi shiru, ina tunani.
Written by
Fiddausi Abdul'azez (Feedoh) & Ayeesha Musa ( Meesha lurv).
®NWA®
Comments
Post a Comment