DIJAH 186~190

🏵🏵DIJAH🏵🏵

Feedoh yanmata✍🏻

1⃣8⃣6⃣~1⃣9⃣0⃣

Shekaru sunja, soyayya mai k'arfi ta shiga tsakanin dijah da Hamzariee kullum suna mak'ale da waya, "dan yanzu haka dijah na zana waec, itakuma affy tana final year d'inta inda takarana English, "Ammi ce zaune parlor da daddy, "daddy yace Ammin Hamzariee baban Nafeeu yakirani, yace sunasan su aiko tunda final year take, Ammi tace toh daddyn affy su aiko mana, "numfashi daddy yaja, yace toh Ammy sonake a had'a dana su hamza, shiru Ammi tayi, batace komai ba, daddy yadawo kusa da ita, yace nafisa kiyi hak'uri da duk hukuncin da Allah ya k'addara, duk da nasan dijah batada asali amma idan Allah yanufa matar shice ba yanda zamuyi, shin sokike rabo ya kashemu? Ammi tace ah ah, daddy yace toh kiyi hak'uri kicigaba da adua, in shaa Allah komai zai warware, "kuma yanda baki canjama yarinyar nan ba, dan Allah karki canja mata, saboda nasan ke macece kamila kiyi hak'uri kisama auran hamza da dijah Albarka, tunda kinga haka, mayb akwai b'oyayyen al'amari, "tabbas jikin Ammi yayi sanyi takuma yarda da maganganun daddy, tace shikenan daddy Allah yasa haka yafi zama alkairi Allah kuma ya albarkacesu baki d'aya, dad'i Yakama daddy, rungumo matarshi yayi yana Samata abarka...

*****************************
Dijah ce keta faman danna horn, maigadi yazo da gudu ya bud'e yana wangale baki, murmushi tayi tace baba maigadi sannu da gida, yace yawwa uwar d'akina, "tana shiga parlor ta yarda jikkan hanunta, Ammi ce kad'ai parlor, duk'awa tayi tace Ammi sannu da gida, murmushi Ammi tayi tace yawwa dijatunah ya exams? Dijah tace Alhamdulillah, amma wlhi Ammi nagaji, dariya Ammi tayi tace raguwa aykin kusa gamawa, dijah tace Ammi afyy fa? Ammi tace batadawo ba, dijah tace Ammi nifa yunwa nakeji, Ammi tace ay angama abinci, daining tawuce saida tayi k'at kana tawuce sama, "d'akin Ammi ta shiga tagyarashi ta wanke toilet tana turaren wuta ne Ammi tashigo, salati Ammi tayi, tace dijah yanzu daga dawowarki saiki fara aiki, sallan wanan marar kunyar yazo yace nabarki kina aiki, dariya dijah tayi tace Ammi  d'akin mahaifiyata tafa na gyara, rungumota Ammi tayi tace khadija Allah yamaki albarka, dijah tace Amin Amminmu....

Dijah nafitowa d'akin Ammi toilet tafad'a tayi wanka, tafito ta shirya cikin wata maroon abaya, tayi matuk'ar kyau, "jitayi anrufe mata idanuwa, murmushi tayi dantasan waye, tace ya hamza naganeka, "dariya yayi tare da bud'e mata Ido, juyo da ita yayi gabanshi, yace wow my baby kinyi kyau, tace nagode charming, yace shine kika dawo koki nemeni, dijah tace eyyah hubby wlhi na d'auka ka fita, kumatunta yaja yace yazan fita batare danaga beautiful face d'innan nakiba, "dariya tayi tace toh sowee aygani, hannunta yaja suka sauka parlor, fira suke cikin so da k'auna, harsun manta inda suke, "affy ce tashigo gida a gajiye, tana shigowa parlor tagansu, tab'e baki tayi, harta wuce tadawo, tace sannunku Romeo nd julliet dariya sukayi Hamzariee yace yawwa fa sarkin saka ido, dijah tace ko ina ruwan mutum damu, affy tace eyyeh dijeh abin harda gori, hamza yace look yanmata adaina b'atama matata suna, sunanta dijah nt dijeh, affy tace toh naji tabtabara sarkin aure, "dariya sukayi, affy tace dijah anjima zaki rakani, sahad store, dijah tace aysaikin nemi izinin mijinah, affy ta tab'e baki tace toh mai miji, idan nahad'aki da daddy Nah dole kirakani, tajuya tatafi, dariya suka bita da ita.....

Su dijah ne zaune parlor suna kallo, itadai kwata kwata jinta takeyi sukuku, "dijah tace charming, hamza yace naam, tace charming wlhi yau tunda natashi gabana ke fad'uwa, Hamzariee yace yasalam, miyasa baki fad'aman ba, shiru tayi, tasowa yayi yadawo kusa da ita, kanta yadafa yace my baby karki damu kita innalillahi wa'inna ilaihir rani'un in shaa Allah akairi ne, d'aga kai tayi tace shikenan, affy tashigo parlor tace sis Ammi na kira, tashi tayi tanufa wajen Ammi, Ammi tace d'iyata yanaganki haka? Murmushi dijah ta kwakwalo tace bakomai, Ammi tace shikenan d'auki lemo da ruwa kikai parlorn daddynku, dijah tace toh, fridge tanufa tahad'a tray ta wuce jitayi gabanta yaci gaba da fad'uwa, karo sukaci da affy, dijah tace sis dan Allah taimakarni kikai wannan parlorn daddy, "affy tace wlhi ban kaiwa kikaima mijinki yakai, jiya ay k'iri k'iri yahana kirakani, tawuce tana dariya, dantaji dad'i tarama, "parlorn daddy dijah tanufa jikinta sai rawa yakeyi, dakyar ta isa parlon da sallama, amsawa akayi akabata izinin shiga, "tana shiga kanta k'asa ta aje tray tareda gaidasu, amma bata d'ago ba, kuma gabanta baidaina fad'uwa ba, "tashi tayi zata fita suka had'a ido, zumbur yayi ya mik'e tare da nunata da yatsa.......

www.phirdauceejeebo.mywapblog.com

IG: yar_ficika

Written by
           Feedoh Deedoh✍🏻✍🏻

Comments

Popular posts from this blog

HUDAH 01~25

RASHIN GATA 1-5

RASHIN GATA 176-180