JINSINAH 51~55

❄❄ *JINSINAH* ❄❄

*_Feedoh_* *_yanmata_* ✍🏻

*_Page_* 5⃣1⃣ *_to_* 5⃣5⃣

Kwance take kan k'irjinshi tanata zabga mashi shagwaba, shiko sai riritata yakeyi, "muhammad yace finah nagode kwarai dagaske tabbas kincika yar halak, Allah yabani ikon rik'e amanarki, finah tace Amin my moh,,,,

         "Suna nan kwance suka dingajin bugun k'ofa, finah ta kalli moh cikin rashin fahimta shiko yagane waye, dan yasan bamai mashi haka sai mahaifiyarshi,,,,

            "Bugun k'ofa yasa suka tashi ga ba d'aya moh ya kalli finah yace dear saka hijab karki fita haka, kallon jikinta tayi kana ta tuna Ashe daga ita sai wata yar vest, hijab ta koma ta d'auko, muhammad ne yaje ya bud'e kofan mamanshi yagani tsaye, dukawa yayi yace sannu Umma, tsaki tayi ta shige ciki,,,
                   ***
Umma ta dinga kwalama finah Kira tana ke tubabba kina ina, tubabba ko bakijina, fitowa finah tayi tana kyarma, duk'awa tayi tace Umma gani, kallonta tayi sama da k'asa ta watsa Mata harara, tace uban waye ummartaki? Ni angaya maki na hada *_JINSI_* da tubabbe ne ni kinganni nan nida zur'a ta kaf dinmu cikin musulunci muka tashi, bamu had'a iri da tubabbu ba sai yanzu da na Allah ya jawomuna jidali,,,

              "Shidai moh had'a kai yayi da k'ofa yana girgiza kanshi, dan gaskia daga jiya zuwa yau abinda Umma kema finarshi baiso dan dai bayanda zaiyi saboda mahaifiyarshi ce, amma da watace daya takamata burki,,,,,,

               "Umma tace ubanwa kika Bari yamaki girkin da gyaran gidan, fun ba'aje ko inaba kinfara iskanci ko? Finah tace kiyi hak'uri naga bamu dad'e da gama breakfast bane shiyasa banyi saurin d'ora na Rana ba, katseta Umma tayi tace to zabaya naji, kinata zuba, ubanwa yace maki mu haka mukeyi KO angaya maki irin arnayen iyayenki ne mu, da bazaki d'ora muna girki da wuri ba, toh munan komi yaji bamu harkan tsiya, dan haka wuce kitafi ki d'ora muna abinci dangin tsiya kawai dake, tana kaiwa nan ta fita fuuuuu, "duk abinnan moh na tsaye baice komai ba,,,,,,

             "Hanyar fita finah takama, tana zuwa zata wuce moh ya jawota, fadawa tayi jikinshi, "magana zaiyi "shhhhhhh tace mashi ta d'ora hannunta kan bakinshi, don't say anything plz my moh, girgiza kai yayi, sakin ta yayi, murnushi tayi ta rab'ashi ta wuce, tana fitowa ta kalli gidan, kwallan data mak'ale dan kar moh yagani suka gangaro, hannu tasaka ta goge,,,,,

             "Part din  Umma ta wuce sallama tayi, Shiga tayi dantasan baza'a amsa taba, parlor ta tardata dukawa tayi tace Umma miza'a dafa, tab'e baki tayi tace pride rice da couslow da kuma pepper chicken, saiki muna kwakwa juice, Allah daiyasa kin iya finah tace eh na iya, umma tace tashi kiban wuri, takai bakin kofa Umma tace ke tubabba tsayawa tayi dan gaskia ta tsani wannan sunan, "Umma tace kikuma gama da sauri dan ki gyaraman gidana, finah tace toh,,,,,,,

        
              "Kitchen ta nufa ta d'ora girki tana d'orawa tafara had'a couslow tana gamawa ta had'a juice takai fridge tasaka, " 1:30pm daidai finah tagama girkinta, gawani kamshi yana tashi, kamar ba da icce tayi girki ba, kafin kace mi gida ya d'auki k'amshin abincin finah, "lek'owar Umma ukku sai had'a miyautakeyi😂😂😂,,,

            "D'akin umma tawuce ba abinda yayi girgiza kai tayi ta kakkab'e ta share tayi mupping parlor ma abinda tamashi kenan, "turaren wuta tayi, d'aki ya d'auki kamshi, "abincinta ta d'auko ta jera mata kan daining table ta d'auko juice ta aje mata saidata tagama ajemata komai, kana taje tasameta duk'awa tayi tace Umma sannu da gida, ko kallonta batayiba, ta ce Umma nagama komai nakan daining, sai sannan umma tace naji dallah, nitashi daga gabana karnayi amai, tashi tayi tabar d'akin tana share kwallan dasuka zubo Mata,,,,,,

              "Abincin Fadilah ta d'auka takai mata da sallama tashiga parlor tsawa Fadilah tamata tace ubanwa yace kishigoman gida, "finah tace yi hak'uri Anty abincin nakawo maki "fadilah tace hey karki Kara ceman Anty dan ni kaf *_JINSINAH_* musulmai ne, ban hada komai dake tubabba ba dan haka karki k'ara ceman Anty, "finah tace kiyi hak'uri, aje abincin tayi ta wuce,,,,

               "Abincinsu ta d'auka tayi sashensu, sallama tayi tashiga, dubawa tayi bata ganshi ba waya ta d'auka ta Kira, yana d'agawa tace my moh wia re u? Moh yace my finah naje masallaci ne amma gani nan zuwa kinji my baby, finah tace olryt saikadawo my moh,,,,,

              "Tana gamawa kal din anty Aysha yashigo tana d'aga kal din tafashema Anty Aysha da kuka hankalin anty yatashi tace finah minene kiyi shiru ki gayaman, kuka taitayi da kyar tasamu tayi shiru, "finah takwashe komaj tagayama Anty Aysha tace Anty nagaji daga jiya zuwa yau idan kinganni bazaki ganeni ba, Anty aysha ta tasauyama finah kuma dama tasan haka saitafaru, "Anty Aysha tace banda abin cemaki saidai kiyi hak'uri shikawai zakiyi, kuma Ina nan zuwa kinji, kashe wayan tayi saboda kuka yaci karfinta,,,,,,

*_Allah_* *_sarki_* *_finah_* *_nikaina _* *_feedoh_* *_yanmata_* *_finah_* *_taban_* *_tausai*_😭😭😭😭

*_Note_* : salam my people kuyu hakuri kwana biyu kunjini shiru, sister na tahaihu, amma da anyi suna zakujinjikullum, Lurv u in to pieces my people❤

                                      *_urz_*
                    *_Feedoh_* *_yanmata*_


*_Dedicated_* *_to_* *_biebee_* *_isa_* ❤

IG: yar_ficika


© *_written_* *_by_*

                  *_Feedoh_* *_Deedoh_* ✍🏻✍🏻

Comments

Popular posts from this blog

HUDAH 01~25

RASHIN GATA 1-5

RASHIN GATA 176-180