HUDAH 101~105

⭐⭐HUDAH⭐⭐

Na
    Feedoh & meesha lurv

1⃣0⃣1⃣~1⃣0⃣5⃣

Tana shiga gidan direct d'aki ta wuce maaah na tsakar gida taga wucewar ta d'akin tana farin ciki, murmushi maaah tayi sannan tad'aga hannunta sama tace, Allah na godema, da kasan farin ciki azuciyar HUDAH yau ka Kawo mana Wanda ya korar da bak'in cikin dake ranta Allah kaina abin godiya Allah ka k'ara kareman HUDAH duk inda take da sauran musulmi.

Mik'ewa tayi tashiga d'aki HUDAH ta tarar a kwance kan gado sai murmushi take, zaunawa tayi kusa da ita tadafa ta da sauri HUDAH tad'ago tana ganin maaah kawai sai tafad'a kanta tana dariya, murmushi maaah tayi sannan tace oh ni Hadiza yanzu HUDAH duk murnar ce tasa ko kunyata bakiji?.

Murmushi tasake sannan tak'ara sunne kanta jikin maaah tana mai cewa kai maaah ni har kinsa, naji kunya wlh maaah Hmm yau abun mamaki yaushe rabon danaga kina dariya irin haka har na manta yau nasan duk abinda yasaki dariya bak'aramin Abu bane don haka bani labari.

D'agowa tayi sannan tace kai maaah sai nafad'a maki nan maah tace iye kaji yar gidan, maaah zaki fara boyeman abune toh ae shikenan, bari natashi na tafi tunda baza afad'aman ba, ta yunkura zata tashi rik'o hannunta HUDAH tayi sannan tace.

Kai maaah nifa banufi na kenan bari na fad'a maki nan tazauna. Tace toh ina jinki nan HUDAH ta fad'awa maaah duk abinda ya faru murmushi maaah sannan tace Allah tabbatar mana da alkairi bari na tashi naje nak'arasa aikina HUDAH tace "maaah muje nataya ki kinji" maaah tace " kiyi zaman ki ae nakusa gamawa".

HUDAH tace " gaskiya maah nikam sai nataya ki" indan banyi maki ba wazanyiwa maaah tace muje, Yar rigima HUDAH tayi dariya tace "eh naji nidai komai zakice sai nayi" dariya tayi tayi waje HUDAH tabita abaya wani dad'i takeji aranta yadda taga HUDAH na cikin farin ciki kai wannan yaro Allah yayi ma albarka daka dawo man da farin cikin gidana Allah ubangiji yasa ka maka da alheri.

Aikin HUDAH taci gaba dayi Wanda sunayi suna hira sai dariya sukeyi SBD nishad'i dasukeji Wanda rabon su dashi tun kafin mutuwar Abbu bayan suga ma tagyara wajen sannan taje yayi wanka ta d'oro alwala banyan tayi sallah ta shimfid'a musu babbar tabarma a tsakar gidan tana jiran fitowar maah Dan suyi hira.

Fitowa maaah tayi tace "ah HUDAH Naufal kece nan zaune, "zumb'uro baki tayi tace ni hudan maaah ce, dariya maaah tayi tace ay yanzu naufal ya kwaceman fada, "dariya hudah tayi tace ina maaah ay daban take a zuciyana, "rungumota maaah tayi tace hakane Auta na,"HUDAH tace lah maaah ina zuwa, tashi tayi ta d'auko mata kayan da naufal yakawomata, ta juyesu gaban maaah, turarukane masu kyau sai abaya suma masu kyau sai takalmi da bags duk designer's,"rike baki maaah tayi tace wannan d'awainiya haka, Allah yasakamai da alkairi, Amin hudah tace,"wayanta tayi kara tana hanun maaah, mik'o mata maaah tayi, tashi tashi tayi tanufa d'aki tana murmushi, murmushi maaah tayi tanajin wani sanyi aranta, gaskia zuwan naufal rayuwarsu gatane da Allah yamasu...

Amsa wayan tayi ta kara a kunnenta, sallama tayi saida naufal yanemi natsuwarshi ya rasa, shiru taji yayi yawa "ya naufal kayi shiru kaki amsa sallama, sannan yadawo hayyacinshi, yace princess kina lapia tace lapia lau, naufal yace my princess wlhi nayi mssn enki alot,"dariya tayi tace ya naufal bakafa dade da tafiya ba, gaskia princess nidai bansan ya naufal enan ki canjaman suna, dariya tayi tace toh zan dinga cema AD,"naufal yace meaning?" Hudah tace Arab design, yace wow gaskia yayi dadi, kokefa princess, haka suka dinga fira kamar karsu rabu, sallama sukayi akan da safe zaizo dan yakusa komawa wajen aiki, kuma yanasan yaga maaah, dan gaskia yanasan asan dashi kafin yatafi......

Www.phirdauceejeebo.mywapblog.com

Written by
              Fiddausi Abdul'azez (Feedoh) & Ayeesha Musa (meesha lurv).

®NWA®

Comments

Popular posts from this blog

HUDAH 01~25

RASHIN GATA 1-5

RASHIN GATA 176-180