HUDAH 106~110

⭐⭐HUDAH⭐⭐

Na
    Feedoh & Meesha Lurv

1⃣0⃣6⃣~1⃣1⃣0⃣

Hudah tace yez boss, dariya yayi yace Lurv u princess, tace Lurv u mre AD, "saurin kashe wayan tayi ta rungumeta tana dariya, "waje ta nufa wajen maaah,tana zuwa ta kwanta bisa cinyar maaaah, "maaah tace Auta minene? Naga bakinki kamar da magana, fuskarta hudah ta rufe, "murmushi ma tayi tace toh idan kingama rufe fuskan kingayaman, ni d'agani karki karyani, "Hudah face Allah sarki maaah duka kwara nawa nake da zan karyaki,"Maaah tace HUDAH tashi muyi magana kinji ko,tashi zaune hudah tayi, " Maaah tace hudah fad'aman abinda ke ranki, karkiji kunyata,kigayaman damuwarki, ki d'aukeni aminiyarki, kinjiko, d'aga kai huda tayi alamar toh,"Hudah tace maaah dama ba wani abubaneba, naufal ne yace zaizo gobe wajenki saboda yana buk'atar asan dashi kafin yakoma Kaduna, idan sansamu enshi mane a tsaida lokaci kafin yatafi,"maaah tace Masha Allah toh hudah miye na kunya, Allah yakaimu goben lapia, sai nashiga nagayama Alh umar saboda shizai shige gaba, hudah tace hakane maaah ena, maaah tace kullum dai bazan gaji da gayamaki ba Hudah kirike gaskia da amana kuma idan Allah yasa kin auri naufal kirike danginshi da iyayenshi tsakani da Allah ,ki kyautatama iyayenshi kamar yanda kikemana kinjiko, "Hudah tace In shaa Allah maaah, hakadai suka dinga fira.

Bayan naufal yayi wanna yafita parlour wajen iyayenshi, "zama yayi kusa da papa, papa yace my boy ya akayi ne? Yace papa fyn, mammy tace papa yakamata yaronan yakoma aikinshi hakanan,bansan wasa dayakeyi da aikinshi, pap yace hakane, my boy kaji abinda mammay tace, naufal cikin shagwab'a yace Allah daddy bazan koma kd ba harsai anje an nemoman auren hudah, "baki mammy ta Kama tace toh ba'a zuwa inyaso kaita zama, kanka kaimawa, naufal yace daddy kanajin matarka ko?, "daria papa yamasu yace naji naufal kyaleta in shaa Allah zamuje neman maka auren hudah,kaidai katabbatar da tana Sanka, "ihu yayi yama mammy gwalo, yace papa tana sona sosai, "papa yace shikenan duk yanda kuka tsara kaida ita saika gayamana, sai inma su kawunka waya sai muje, rungume papa yayi, yace papa nagode Allah yaja kwana, amin papa yace, "kana yaje wajen mammy yace mammy plz say something mana, murmushi tayi tace Allah yatabbatar da alkairi my boy, rungumeta yayi yace Amin mammy nd I Lurv u, "mammy tace Lurv u mre my boy, hakadai suka dinga fira har time en bacci yayi yamasu saida safe kana yatafi daki,"koda nayayi,  yakoma d'aki kasa bacci yayi, yanata juye juye, wayanshi ya jawo yafara SMS, "supreme don't u tink you should be mre concern about what I feel for you? Princess AD nata mssn enki, sndn yayi, "tana kwance ta runtse ido amma ba bacci takeba, wayanta taji tayi Kara, d'aukowa tayi ta duba, tana karanta text d'in tana murmushi, tana gamawa tayi kamar zatama reply saikuma tafasa, " kwance yake yana juyi yana jiran reply amma shiru, "har bacci b'arawo yayi gaba dashi, nima fitowa nayi na jawo mai kofan.

****************
Tun karfe ukku da naufal yatashi baikomaba sallah yakeyi, harsaida aka kira asuba, tashi yayi ya fito, yana futowa sukaci karo da papa, murmushi papa yayi yace my boy anfito kenan gaidashi yayi yace na fitoh papa, jerawa sukayi suka tafi masallaci,"bayan sundawo masllaci naufal ke bacci bai farkaba said 12pm a gurguje ya shirya, parlour ya fito nan yatarda iyayenshi zaune, gaidasu yayi, suka amsa fuska sake, b'ata fuska yayi, mammy tace my boy minene kuma?, zumb'uro baki yayi yace shine baki tadani da wuri ba dariya tayi tace, aybakace natadakaba, yanzu dai ci abinci katafi gidansu huda, dannasan can aka nufa, dariya yayi tace ofcourse mammy...

Parking yayi kofar gidansu, kiranta yayi a waya yace gashi yaxo, daga d'ayan b'angaren naji hudah tace ya shigo, nok'e kai yayi kamar tana ganinshi yace kizo kishiga dani,"Hudah tace shikenan bazaka shigoba kenan tunda dama ba wajena kazoba,murmushi yayi yace zakizo hannu yarinya, "sallama yayi maaah ce ta amsa mashi, shigowa yayi ya duk'a har kasa yagaida maaah, amsawa tayi cikin fara'a, maaah tace tashi ka zauna kan kujera mana, noke kai yayi, yace maaah ban ma yayi, "murmushi maaah tayi tace hudah tagayaman sak'on ka, nikam ta b'angarena bakomai na baka hudah duniya da lahira, saidai ka riketa amana dan marainiyace, kuma bazan yanke hukunci nikadai ba, saida dangin mahaifanta, dan haka kafinnan...... Bata k'arasa ba sukaji sallamar daddy, amsa mai maaah tayi kana tace ya shigo," da fara'anshi ya shigo yace ina sirikin nawa, sunne kai naufal yayi, yagaidashi a girmame, amsawa daddy yayi, yace naufal Maman hudah tagayaman komai kuma nayi murna, saboda nasan mahsifinka mutumin kirkine, kuma nasan zuri'anshi zasuyi halin kwarai, dan haka kagayama iyayenka duk sanda kuka shirya kuzo, nikuma in shaa Allah zan shigema gaba wajen iyayen huda,"godia naufal ya shigayi kamar Wanda akace an daurama aure lolxzz😃😃"rafan hundred ya aje yatashi ya fita maaah na magana amma yak'i juyowa, murmushi maaah tayi tace angode, yana fita yakira hudah a waya..

Takowa take kamar wadda kwai ya fashemawa a ciki, shidai sakin baki yayi yana kallonta, fari tamai da ido data k'araso, murguda baki yayi yace ayna b'ata dake, ido tazaro ta marairaice tace AD mikuma nayi, yace bakinga SMS enaba amma ko reply, HUDAH tace eyyah AD kayi hak'uri, yace na hak'ura my wyf, dariya tayi, yace tafiya fa zanyi cz inada wajen da zani, zumb'uro baki tayi tace ina zaka? Yace wajen budurwata zani, "hararanshi tayi ta juya zata tafi, hannunta ya rik'o yace wasafa nake maki, dariya tayi tace toh nayarda,"Hudah tace Allah yatsareman kai AD, yace Amin, princess, sai munyi waya kinji, tace tohm...

www.phirdauceejeebo.mywapblog.com

Written by
                 Fiddausi Abdul'azeez (Feedoh) &
                 Ayeesha Musa (Meesha Lurv).

Comments

Popular posts from this blog

HUDAH 01~25

RASHIN GATA 1-5

RASHIN GATA 176-180