HUDAH 56~60

⭐⭐HUDA⭐⭐

Na
    Feedoh & Meesha Lurv

5⃣6⃣~6⃣0⃣

Nayi shiru cz banda amsar da zan gayam maaah, tak'ara ceman huda dake nake magana kinyi shiru, nad'ago a hankali na kwashe kaf yadda mukayi da ya faruq na gayama maaah, SBD ban iya yimata karya, maaah takirani jiki sanyaye, tace huda bazan hana kiso faruq ba saidai zanja hankalinki kisan waye faruq, saboda shine mutumin da yafara dora maki karan tsana shida mahaifiyarshi, kinatsu kisan waye shi, ke yanzu ba yarinya baceba, duk zunubin da kikasan zan dauka kema shi zaki dauka,ki kama mutuncin kanki, kitsare mutuncinki da kuma namu mu iyayenki, domain yanzu muna cikin wata rayuwa na(Lubabatu Maitafsir) rayuwar da sabon Allah yayi yawa cikinta, ina rokonki huda da kikama mutuncinki wajen kowama bawai faruq kad'aiba haka dai Maaah ta dingayiman nasiha, tagama nace in shaa Allah maaah zaki sameni mail time mutunci na da naku baki daya, maaah tace yawwa Auta tashi kitafi Allah yamaki albarka, na amsa da Amin.

Haka rayuwa ta cigaba, soyayya nakara karuwa tsakaninmu, saidai duk abinnan da ake yan gidansu ya faruq basu saniba, saboda yaceman baisan mummy tasani cz zatana iya hanashi, shikuma yanzu yanda yakeji he can't do without mie, da wannan dadin bakin na ya faruq na yarda dashi, kuma nakasa gayama fady tsakanina dashi saboda karta gayama mummmy.

Saidai abinda na Lura da ya faruq shine yanasan ya dinga tabani nikuma kullum zan nuna mai ah ah domin ina tuna nasihar abbu da maaah da sukeman, rannan muna tad'i dashi sai yaceman huda can I ask u sometin nace mai go ahead, bud'an bakinshi sai ceman yayi miyasa bakisan na dinga tabaki ne wai? Nace mai ya nawaf saboda kafikowa sanin ba kyau, wani shu'umin murmushi yayi yace gaskiarki ne bae,nidai yanzu abinda nakeso dake shiga gida kicema Maaah zamuje shopping nace toh, nashiga gida nasamu maaah na gyara alayyahu, nace maaah sannu da aiki tace yawwa, nace dama ya faruq ne yace nace maki zamuje wai shopping, maaah tayi shiru tace toh sai kundawo, ki kula da kanki kinji nace in shaa Allah nafita yana nan inda nabarshi yace pretty maaah ta amince KO? Na ce "Eh" yace muje toh.

Tafiya mukeyi kamar zamu bar gari, harnakasa hakuri nace ya faruq ina zamu haka? Yayi dariya yace saidaki zanyi nima nayi dariya, naga munyi parking gaban wani gida nadago na kalleshi ya d'agaman gira, yace basai kince komai ba matsoraciya gidan friend dinane matarshi tadaman saina kawoki, na gyada kaina haka muka danna Kai cikin gidan...........

NOTE: kunjimu shiru kwana biyu walle 4ne ena tasamu matsala amma yanzu zaku dinga jinmu kullum, tnx ya'all

Written by
                Fiddausi Abdul'azeez (Feedoh) &
                Ayeesha Musa (Meesh Lurv).

®NWA®

Comments

Popular posts from this blog

HUDAH 01~25

RASHIN GATA 1-5

RASHIN GATA 176-180