ZAMAN GIDA 06~10
🤔🤔 *ZAMAN* *GIDA*🤔🤔
*_Feedoh_* *_yanmata_*✍🏻
*_page_* 0⃣6⃣ *_to_*1⃣0⃣
Tun daga titin mani house, har goruba sukaje, k'asa suna tafiya suna yanga, "amma tun la'asar suka fita gashi har magrib, babu wanda ya kallesu, "haka dai sukaga bin titin bazai masu ba suka dawo gida, "tunda suka taho bamai ma wani magana kowane da abinda yake sak'awa aranshi, "saida suka kawo unguwarsu, hadiza ta kalli sadiya tace k'awa mukuma haka Allah yayi damu, sadiya tayi murmushin takaici, tace yazamuyi, kiduba kiga kaf layinnan babu sa'anmu amma mu haryanzu shiru, gaskia munshaida *ZAMAN* *GIDA* , "hadiza tace gobe akwai wajen wani malami da zamu safina ce ta had'ani dashi, ki shirya gobe muje, sadiya tace wlhi harna gaji, hadiza ta dafata tace ba'a gajiya da neman sa'a kedai kawai ki shirya, sadiya tace shikenan Allah yakaimu goben,,,,,,
*********
Shiga gida hadiza tayi bako sallama, Inna ta tarda tsakar gida, hararta Inna tayi tace gidan maguzawa ne da zakisho ba sallama, zub'ura baki hadiza tayi tace nafayi Inna, Inna tace gidan uwarwa kikayita, Allah dai ya shiryaku, yakawo randa zamu rabu daku duk unguwarnnan babu sa'anku inama amfanin nauyin k'afa gunguni tayi ta nufa d'aki,,,,,
" *WASHE* *GARI*
Tunda tatashi daga bacci taketa faman shiri, kallonta inna tayi tace saikuma ina? Ku baku gajiya da yawo, "hadiza tace makaranta fa zamu, Inna tace inacewa kunyi Hutu, hadiza tace result aka lik'a shine zamuje ganowa, inna tace shikenan Allah yamaidoku lafiya, d'ari biyar ta mik'a mata amsa tayi tana murna, tafito waje,,,,,,
"Tana fitowa taci Karo da sadiya, hadiza tace da gidanku zani, sadiya tace aynaga baki fito bane, shine nace bari na biyo, hadiza tace muwuce kawai, "tasha sukaje, suna zuwa sukace motar d'andume suke nema aka gwada masu sukayi sa'a kuwa saura mutum ukku suna shiga wani yazo, mota tatashi sai d'andume,,,,,,
"Suna isowa tasha, suka tambayi wani dan Allah gidan malam gobe da nisa mukesan zuwa, mutumin ya kallesu yace gaskia akwai nisa, saidai ku hau amalanke, zaro ido sadiya tayi tace amalanke, mutumin yace kwarai saboda ko mashin baibi hanyar, kallon juna sukayi, Hady tace yazamuyi dole muje, malam ina zamu hau amalanken, gwada masu yayi inda zasu hau,,,,,,
"Dakyar suka iya hawan amalanke, suna hawa mai amalanke yaja, yayi cikin daji dasu, "tafiya suke cikin daji wadda takai ta Rabin awa, sadiya harta fara nadamar shigowa dajinnan, "gaban wata bukka ya tsaya, mai amalanke yace ku sauko munzo, hadiza tace inane gidan, nuna masu bukka yayi, sadiyace tace malam dan Allah bari mugama ka maidamu,,,,,
"Bakin bukka suka tsaya, suna sallama, daga ciki sukaji anacewa wake muna sallama, nan ba'a sallama kushigo kawai, "shiga sukayi, wuri suka samu suka zauna, tare da gaida malam, "malam yace yanmata miya kawoku, hadiza ce tace malam bawani abu yakawomu ba illah aymuna taimako, aure mukeso muyi amma ko kare baizuwa wajenmu, d'aga mata hannu yayi yace ya isa,,,,
Wasu ruwa yajawo yayi surkullenshi, kallonsu yayi, yace yanmata saidai kuyi hak'uri bazakuyi aure ba, sadiya tace mi? Yace kwarai saboda kuduka biyun na duba nidai banga mijinku ba ma'ana mijinkuma baizo duniya ba,,,,,,,,
*_Dedicated_* *_to_* *_sadiya_* *_Marafa_* *_nd_* *_Hadiza_* *_Ahmad_*
*Feedoh* *Deedoh*✍🏻✍🏻
Comments
Post a Comment