DIJAH 241~245

🏵🏵DIJAH🏵🏵

Feedoh yanmata✍🏻

2⃣4⃣1⃣~2⃣4⃣5⃣

Biki akayi sosai inda akayi event har ukku, yau Friday yau ake dinner, amare sunsha kyau har sungaji, cute makeover tama amare kwalliya, gaskiya amare sunsha kyau harsun gaji, mawak'a aka d'auko  sosai karode bello shiya masu wak'a, saboda dijah nasan karode, gaskia dinner tatsaru "niko feedoh na chashe yanda Yakamata,  "rana bata k'arya saidai uwar d'iya taji kunya,  yau asabar aka d'aura auren dijah da hamzariee afrah da nafeeu inda dubban mutane suka halarci d'aurin auren ciki Harda shugaban k'asar nageria, "bayan and'aura aure akayi reception, anagama reception aka kawo affy wajensu daddy suyi Mata fad'a daddy yace kiyima mijinki biyayya inayi bari na bari, Baba ma nasihar daya Mata kenan, sannan, yabata key d'in mota, akatafi da afrah kaduna, affy da dijah sunyi kuka, kamar zasu cire ransu, Allah sarki afrah Allah yabaku zaman lapia...

Dare nayi aka kawo dijah gabansu Baba, shida daddy suyi Mata fad'a daddy yace Toh dijah yanxu Kintashi daga hannunmu kima mijinki biyayya, Karki saki kibari mijinki yakawo k'ararki, daddy yace Baba yamata fad'a Baba na hawaye yace aykagama Mata fad'a kije khadijah Allah yamaki albarka,kema ga key d'in motarki,  kuka dijah kayi sosai, wajensu Ammi aka tafi da ita ammi kasa Mata fad'a tayi saidai kuka, mamace tadaure tace kiyi biyayya ga mijinki, tarbiyan da kikasamu hannun malan da mamarki kiyi Amfani da ita kike Allah yamaki albarka, "da kyar aka fidda dijah da gidan, aka wuce da ita gidan hamzariee , "yan kawo amare sun watse daga feedoh sai hanne suka rage, "dijah ce kwance bisa hanne sai ajiyar xuciya takeyi, "dijah tace Allah sarki Baba da mama ba rabon suga wannan ranar Allah na rok'e ka daka gafarta masu, hanne da feedoh sukace Amin, "anguna ne suka shigo sallama sukayi, wuri suka samu suka sauna tare da tsokanar Amare, anyi wasa da dariya, kana aka bud'e taro da adua tare da yima amarya da ango nasiha, anyi siyan bakin amarya hundred thousand, "anguna sukace su hanne sutashi sutafi dasu, nanfa sabon kuka yatashi, dakyar aka b'anb'are dijah jikinsu, ango yatafi yarakasu, "dawowa yayi yatarda dijah na kuka, d'agota yayi tare da yaye Mata lifaya d'inta rungumeta yayi yace haba my babe miye na wannan kukan gidanafa aka kawoki, dakyar yasamu tayi shiru, "Alwalla sukayi suka gabatar da nafila wadda manzonmu ya umurce duk wasu sabbin aure suyi, "bayan sungama yamata tambayoyi kuma tabashi amsa, "kitchen yatafi ya d'auko plate da cups, zubamasu kaza yayi, yadinga ba dijah harsai data k'oshi "d'aukarta yayi kamar yarinya ya kaita kan gado, wasa yafarayi da ita dijah kuka yakeyi tana rok'onshi Amma ina hamzariee yayi nisa nanfa labari aysha banban, nidai feedoh fitowa nayi na barsu....

**********************************
Asubar fari nakoma gidan dijah, da taimakon hamzariee dijah  tatashi yaje toilet Wanka tayi tayi sallah, tana gama sallah takoma bacci, baiwar Allah bata tashi ba sai 12 tana tashi toilet ta nufa tayi Wanka, shiryawa tayi cikin pink super Riga  da skrt sunyi matuk'ar karb'anta tana cikin d'aura d'ankwali Hamzariee ya shigo rungumota yayi ta baya sunne kanta tayi, tacemai ina kwana yace lapia lau dijah na nagode kwarai dagaske, kincika yar  halak nagode da rik'eman mutuncin kanki da kikayi Allah yamaki albarka, dijah tace amin hannunta yaja sukaje parlor abinci yadinga bata harsaida ta k'oshi, "Alhamdulillah farin ciki ya bayyana wajen dijah lokacin data cire ransamunshi, saboda Hamzariee bai rageta da komai ba, kullum cikin kulawa yake da ita, gashi tafara skul d'inta a nail university inda take karantan medicine...

BAYAN SHEKARA SHIDDA
Bayan shekara shidda dijah ce ta fito cikin asibitinta Alheri hospital, gakuma wasu twinse mace da namiji na binta masu kyau, dasu dijah tace haneef ina zamuje haneef yace wajensu grandma dijah tace haneefa kefa tace mammy Nina can, dijah tace toh mutafi, "asokoro sukawuce dijah na parking mota suka fito da gudu suka nufi cikin gida suna kwalama Inna larai Kira, parlor suka had'u da ita fad'awa sukayi kan  k'afanta suna tsokanarta inna tace ni ku d'agani mai sunan malam karku karyani dariya sukayi, inna tace lubabatu kuda suwa kukazo haneefa tace tare da mammy, dijah ce tashigo da sallama tace haneefa Ku d'agaman uwa karku karyata, haneef yace haba Ammi duka nawa muke, "hannefa tace Inna ina grandma? Inna tace miye shi, haneefa tace ooopz sori baki fa saniba, kaka kenan, tab'e baki inna tayi tace kuma ankoya maku yaren arna, tana sama tashi sukayi suna dariya suka haye sama, sai dare kana suka wuce gida...

Dijah ce zaune tana duba wani littafi ga twinse d'inta gabanta harsunyi bacci, hamza ne ya shigo da sallama tashi tayi ta tareshi, rungumeta yayi, yace sannu da gida my babe, dijah tace yawwa, hamza yace inasu princess dijah tace sunyi bacci, "dijah ce kwance saman cinyar hamza tace ya hamza samun irinka a dunia sai anshirya, yau gani nazama babbar likita, kakuma bud'eman asibiti,  kuma kasama yaranka sunayen mutanen da bazan iya mantawa dasu ba, ya hamza banda bakin cewa komai, saidai Allah yabani burin yimaka biyayya, "Hamzariee yace karki damu my babe komi namki kin cancanci sama dashi, nidai fatana kicigaba da yiman biyayya, dijah tace angama my man, cikinta yashafa yace gaskia yau sai anma su haneefa k'ane aysun shak'ata hakanan, baijira cewartaba ya sungumeta sukayi d'aki...., nidai feedoh nan zan aje biro Nah...

Godia ta tabbata ga Allah subahanahu wata'alah daya bani ikon gama wannan littafin kura kuran danayi Allah kayafemani...

Nasadaukar da wanann littafin ga Antynah nafisa Sani yashe, Allah yabaki lapia albarkacin wanan watan mai alfarma... Amin

Special tnx 2 my people nagode maku sosai da bibiyan wanann littafin nawa, bazan iya lissafakuba saboda kuna da yawa, nagode kwarai dagaske❤

Godia ta musamman ga
Feedoh & biebee💕novels
Dandalin karatu
Rookee sadau❤novels
Meesha❤ fans
Hausa novel
Muyi zumunci dan Allah
Novels only
Khadijah candy novel
Modern hausa writers
Da dukkan Groups d'inda banfad'a ba nagode kwarai Allah yasaka da alkairi

Saikunji bayan sallah cikin sabbin litattafaina in shaa Allah, "ayi azumi lapia

For any comment or correction here my digit 08037791855

Ni feedoh nake maku fatan alkairi❤

Written by
           Feedoh Deedoh✍🏻✍🏻

Comments

Popular posts from this blog

RASHIN GATA 176-180

RASHIN GATA 1-5