JINSINAH 151~155

❄❄ *JINSINAH* ❄❄

*_Feedoh_* *_yanmata_* ✍🏻

*_page_* 1⃣5⃣1⃣ *_to_* 1⃣5⃣5⃣

Koda moh ya shiga d'akin Fadilah ya tarda bata nan, dandama yanxu fita takeyi,bawai dole saita tambayeshi ba, "wuri yasamu ya kwanta, yanata tunane tunane amma yakasa tuna komai, shikanshi yasan akwai abinda ya manta,amma yakasa tuna miye wannan abun, "da kyar yasamu yayi isha, tunda yayi sallah ya kwanta bacci mai nauyi ya d'aukeshi, "cikin baccin ne yayi mafarkin wata mata da d'anta sunxo mashi, matar tace moh miyasa zakaman haka, bancancanci kaman haka ba, arif baikamata yatashi ba uba ba, plz moh kadawo garemu muna buk'atarka, cikin tsawa yacema matar bansanki ba, kuma ni banda d'a plz kifita harkana, stay out of my life, yana kaiwa nan ya bar gurin itako matar kuka takeyu tana kiranshi amma bai juyoba, "firgigit yayi ya tashi zaune, tagumi yayi yana tunanin wacece wnnan tazo mai, daya ga baiya tuna komai kawai saiyayi adua ya kwanta,,,,,

        "Tunda ya dawo sallan asuba bai koma ba, yakumaji dad'in Fadilah da ba d'akinshi ta kwana ba, 7:am  ya jawo trolley ya shirya kayanshi, yana gamawa tashiga wanka, yana fitowa ya shirya cikin geznah yayi mugun kyau kamar sabon ango lolzz, "lallab'awa yayi ya jawo trolley d'inshi ya maida d'akinshi ya rufe, kodayaje part d'in Umma ya tarda itama ta shirya, gaidata yayi, abin mamaki tabata dan rabon da yagaidata tunda finah tabar gidannan, "amsawa Umma tayi yace idan kinshirya mutafi, Umma tace toh, amma kalaci fa Moh yace munyi kan hanya bansan Fadilah ta tashi muna cikin gidannan dasauri Umma ta d'auki akwatinta, "Moh ta amsa suka nufa parking space, "suna shiga mota horn yayi maigadi ya taso da gudu ya bud'e masu gate, Moh yace mashi zamuje argungun bazamu dawo ba sai nan da sati d'aya ka kula da gida, maigadi yace toh Alh Allah ya kiyaye ya maidoku lafiya, "da gudu Moh yaja mota yabar unguwar saikace Wanda akace mashi ga fadila nan,,,,,

"12:00pm fadilah ta tashi daga bacci, wanka ta shiga bayan tafito ta shirya, d'akin Moh ta wuce ganin d'akin kulle yabata mamaki, komawa tayi ta d'auko wayanta, kiranshi tayi amma saitaji switch off abun ba karamin tada mata hankali yayi ba, part d'in Umma ta nufa cikin k'unan rai dan duk zatonta yanacan, tana zuwa taga wurin rufe, juyawa tayi tanufa parking space, zarginta ya tabbata moh fita yayi bata saniba, "maigadi tashiga kwalama Kira, da gudu ya k'araso, duk'awa yayi yace hajiya gani, Fadilah tace kaga Umma itada was suka fita, maigadj yace da yallab'ai hajiya, razana Fadilah tayi, tace sungayama inda zasu, maigadi yace eh sunje argugun kuma sai sunyi sati, Fadilah tace sati cikin tsawa saida maigadi yakusa fitsari, yana kad'a kai yace eh hajiya, "juyawa tayi tanufa cikin gida, "tana shiga ta d'auki waya takira, habiba, habiba na d'auka tace hajiya gani nan kusa da gidanki, Fadilah takashe wayan,,,,

               "Habiba ce tashigo taga Fadilah nata zagayen d'aki, da sauri habiba tace lafiya? Fadilah tace inafa lafiya, takwashe komai tagaya Mata, "numfasawa habiba tayi tace miye abinyi, murmushin mugunta Fadilah tayi tace zanyi maganin umma hauka zansa tayi, tunda naga asirin dane yafara karyewa amma yanzu zanyi wani, shikuma muhammad ko k'ofar gida yagama fita, saida izinina, habiba tace Ina bayanki, amma kibari tunda ance sati d'aya zasuyi Ana gobe zasu dawo saimu koma wajen malam, yanda maganin zaiyi aiki, Fadilah tace hakane,,,,,,,

"Moh da Umma d'akin malam Ana gaisawa dakuma ya hanya, "gyara zama malam yayi yace na Allah jiya kayi mafarki ko? Moh yace eh, malam yace Masha Allah amma zaka iya tuna matar da kayi mafarki, moh yace ah ah, malam ya gyara zama ya dubi Umma yace asiri Fadilah tamaku, shi, na Allah anmashi asiri ya manta da matarshi da kuma d'anshi a k'ark'ashin pillow d'inshi aka samadhi maganin, "kekuma tsallakawa kikayi shiyasa sai yanda tayi Daku, da inaso da saina maida Mata abinta amma bazanyi hakaba duniya zata Mata hankali,"amma ke hak'k'in baiwar Allah nan ce da kika zalunta, damma Allah nasanki da Rahma, fashe Umma tayi da kuka tace tabbas nasan Alhakin nafisa ne, shidai moh binsu yayi da kallo, dan baigane Ina suka dosa ba, "malam yace karki damu ni zan karya asirin shiyasa nace kuzo nan , saboda aikinku zaiyi kwana bakwai daga randa kukayi kwana bakwai zamuga sarautan Allah kuma in shaa Allah komai zaiyi daidai, godia Umma tayi banda moh da yazama hoto, wani galan malam ya d'auko ya zuba maganin dake ciki a cup ya mik'ama moh ba musu ya karb'a yasha, wasu ya d'auko ya fesa mashi, haka itama Umma anbata nata tasha , yakuma basu na wanka,,,,,

"Finah ce zaune tayi tagumi ga hawaye na Binta, mummy ce tashigo ganin tana kuka, yasa ta zauna, jawota tayi jikinta tace wai bana hanaki kukannan baneba, "finah tace wlhi mummy bansan yana zuwa ba, yanzu mummy ya za'ayi na iya zaman aure da mijin Anty kuma babban abokin moh, wlhi mummy banma moh adalciba, duk randa yadawo hayyacinshi zai tsanemu, saita fashe da kuka, ita kanta mummy tasan yar ta gaskia ta fad'a d'agota tayi tashare mata hawaye, tace nafisa ba yanda zamuyi da k'addara ki rungumi k'addaranki, kekuma haka taki k'addaran tazo, kiyi hak'uri, kuma shi moh bazaiga laifinki ba, tunda yasan kinmashi adalci tsawon shekara da watanni kina jiranshi amma shiru, aykinga ba kowace mace zata iya hakaba, kiyi hak'auri kinji my baby in shaa Allah everything  will be fine, goge hawayenta finah tayi, mummy tace data my girl kokefa tashi muje kitchen, antynki taman waya tace gasunan zuwa tunda ke kink'i komawa, murmushi finah tayi ta tashi suka tafi kitchen,,,,,,,


*_Dedicated_* *_to_* *_biebee_* *_isa_*❤

IG: yar_ficika


© *_written_* *_by_*
          *_Feedoh_* *_Deedoh_*✍🏻✍🏻

Comments

Popular posts from this blog

HUDAH 01~25

RASHIN GATA 1-5

RASHIN GATA 176-180