JINSINAH 76~80

❄❄ *JINSINAH* ❄❄

*_Feedoh_* *_yanmata_*✍🏻

*_page_* 7⃣6⃣ *_to_* 8⃣0⃣

Kwance take tanata juya magani a hannunta tarasa yanda zatayi tasakama finah a abinci, tsaki tayi tajawo wayanta ta kira, ringing biyu habiba ta d'auka cikin shewa tace Hajia tun randa nakawo maki nake jiran wayarki, sai yau kika saka kenan, cikin ya zube KO, danna san yanzu tana hannun likitoci saikuma tasake fashewa da dariya,,,,,,

      "Fadilah tace habiba banfa saka Mata maganin ba haryau, cikin k'araji habiba tace what mikike nufi yau kwana biyar da kawomaki magani, kokuma kincanja ra'ayi ne? Haba Fadilah miyasa zakibari tubabba tayi tasiri akanki gidanki fane? Wlhi kika bari tahaihu saidai wata amma bakeba, "fadilah tace wlhi ba wai nacanja ra'ayi baneba, ah ah saidai bansamu dama ba, Dan antyn nan tata kullum take zuwa shiyasa bansamu damar sakamata shiba, tsaki habiba tayi tace toh yanzu minene mafita, Fadilah tace wlhi bansaniba, "cankuma tace amma bari na duba dan duk yau banji motarta ba Allah yasama batada lafiya dan tsohon ciki gareta, "habiba tace yawwa tashi duba idan kinga bakowa kawai ki aiwatar da abun, ki tabbata kinjata ajiki harki bata maganin, Fadilah tace zanyi duk yanda zanyi Tasha,,,,,
               ***********

Part din finah tanufa tana shiga parlor taji shiru ranta yamata fari, "parlor n tabi da kallo gaskia yamata kyau, sosai, yaune ranan farko data shigo sashen finah, tsaki tayi tace yanda bazan haihuba kema bazaki haihuba, "sallama tadingayi, "amma shiru, kuryan d'akin finah ta nuna inda dama takesa ran shine d'akinta, tana zuwa tayi sallama tareda knocking, daidai finaj tafito daga toilet, k'ofan tanufa tana amsa sallama, bud'ewa tayi ganin wadda bata tsammani ce yasa taja baya, "murmushi Fadilah tayi tace miye na tsorata kamar kinga cici, nifa yar uwarki ce, kidaina tsorata dani, d'aga kanta finah tayi saboda haryanzu batadaina mamakn ganin Fadilah ba, ahankali tace shigo Anty, shiga Fadilah tayi cikin d'akin,,,,,,,


       "Wuri tasamu bakin gado ta zauna, itama finah zamatayi, Fadilah tace haryanzu bakidaina mamakiba, KO?  "Karki damu Allah ne ya shiryeni, sakamakon wani wa'azi danaji, shine nazo nabaki hak'uri, murmushi Finah tayi tace wlhi Anty damani ban rik'ekiba ko sau d'aya kuma na yafemaki, Fadilah tace nagode, "yakuma k'arfin jikinki, finah tace dasauki, Fadilah tace ya upcoming babynmu kuma, dariya finah tayi ta d'ukar da kanta k'asa,,,,,,
             **********

        "Jan finah da fira fadilah tadingayi, harsaida taga tasaki jiki da ita, Fadilah tace yar kanwata nacikaki da surutu KO? Bari nakawo maki lemu, finah tace ah ah wlhi Anty dama kinbarshi, "b'atarai Fadilah tayi tace danmi, dole kisha Abu mai d'an sanyi kinyi surutu dayawa kedai Ina zuwa, juya kai tayi tafita, "mamakin sauyawar halin fadilah tadingayi, murmushi tayi tace Allah kenan mai yanda yazo, yanda naga canjin halayen Fadilah Allah ya nunaman na uwar mijina haka,,,,,,

      
  "Jim kad'an saiga fadilah ta dawo da cup tana dariya, mik'ama finah tayi tace gashi kisha, amsa tayi tare da godiya, bakinta takai kan cup d'in "ganin haka yasa Fadilah murna da farin ciki marar  misaltuwa, "jitayi ance finah karki sha wannan lemun da k'arfi, juyawa Fadilah tayi cikin razana taga waye "itakuma finah sakin cup d'in tayi tareda maido nabakinta k'asa, "bakowa baneba Anty Aysha ce tayi magana, "takowa Anty tayi tazo gaban Fadilah, tace mitamaki? Kike Neman kasheta ki kashe abinda ke cikinta, "fadilah cikin tsiwa tace ni zakima sharri akanmi Zan kasheta, da can dana tsaneta ban kasheta ba, sai yanzu?, "murmushin takaici Anty tayi tace ayko yanzu basanta kikeba, tunda zaki kasheta, "waya tazaro ta kunna, "saiga fadilah lokacin datake zubama finah magani, kallonta Anty tayi tace koshima k'arya nakemaki, "fadilah tayi tsuru tsuru, anty tace bazan gwadama kowa ba, amma Zan ajeshi shaida Dan nan gaba komai yasamu finah da d'anta kece, dan haka bar d'akinnan, wucewa tayi sumi sumi,,,,

            "Juyowa anty tayi kan finah ta d'aure fuska tace Ashe bakida hankaki, mutumin dabai sanki haryakawo maki Abu kikarb'a harkina kokarin sha, "marairaicewa finah tayi tace wlhi Anty bansaniba, takwashe kaf yanda sukayi tagayamata, murmushi Anty tayi tace Allah yafita, kuma abinda takesan tayi kanku in shaa Allah bazata samu sa'a ba,,,,,


Finah tace wai Anty ya akayi kika ganta, kuma ya akayi kikazo keda kikace tunda na warke bazakizo yauba, "numfasawa Anty tayi tace wlhi finah Ina kwance saina dinga ganin abu zaifaru dake, kawai saina d'auka waya nakira Amir bako gida, nacemai zanzo shikanshi yayi mamaki, dan harya ceman lafiya nacemai bakomai, kawai inasan nazo nak'ara ganin jikinki, saiyaceman saina dawo,,,,


                "Ina shigowa parlornki zanyi sallama kenan, sainaji Ana waya, naji anacewa habiba nasamu sa'a yau gashinan zansaka Mata, dan ba kowa dan na tambayeta Anty dinta tace yau bata zuwa, "sai nayi sadaf sadaf naje wajen kitchen d'in "wazan gani fadilah, saina zaro wayana na dinga video gudun kartayi gardama, ina ganin zata juyo sainayi baya, "naduk'e wajen daining area d'inki, toh kinji yanda akayi, "fad'awa jikin Anty finah tayi tana kuka tace anti minamata take Neman kasheni da abinda ke cikina, anty tace kishi kedamunta, "amma Allah natare dake, kuma saikin kula kinsaka ido kuma kidage da adua, kuma karnasaki naji maganan nan bakin moh kinji "finah tace naji Anty,,,,,,


*_Dedicated_* *_to_* *_biebee_* *_isa_* ❤


IG: yar_ficika


*_Written_* *by_*

            *_Feedoh_* *_Deedoh_*✍🏻✍🏻

Comments

Popular posts from this blog

HUDAH 01~25

RASHIN GATA 1-5

RASHIN GATA 176-180