DIJAH 226~230

🏵🏵DIJAH🏵🏵

Feedoh yanmata

2⃣2⃣6⃣~2⃣3⃣0⃣

Dijah ce ta sakko cikin shirinta na skul, unifoam d'in sunyi matuk'ar karb'anta, parlor tasamu iyayenta, gaidasu tayi, amsawa sukayi cikin sakin fuska, "baba yace dijah ga key d'in mota nan idan zaki tafi skul, sadda kanta k'asa tayi tace baba hamza ne yace zaizo yakaini, baba yace ayshikenan, "kice mijinki zaikaiki, tashi tayi da gudu, tace mama ina Inna, "mama tace tana d'akinta, dijah tace bari naje mugaisa, "d'akin tashiga da sallama, tarda Inna tayi tabuga tagumi, dijah tace Inna lapia? Inatace inafa lapia, tund'azu nakejin bayan gida narasa inda zanyishi, waiku dama yan burni baku bayan gida, "dariya dijah tayi sosai tace munayi mana Inna, "Inna tace toh ayna kukeyi, hannunta dijah taja, takaita toilet duk tanuna mata yanda zatayi komai, da yanda zatayi wanka, "kana tafito, d'akin tafara gyarawa, can saigata tafito, tace Inna kingama, tace eh yar albarka, "Inna tace nidama baki gyara gadon ba, dan ba bisashi na kwanaba, dijah tace bisami kika kwana, Inna tace k'asa mana, ina zan hau wannan gadon inmanta da tashi sallah, dijah dan dariya harda hawaye, "hamza ne ya shigo d'akin da sallama, amsawa sukayi, shigowa yayi ya duk'a yagaida Inna amsawa tayi tana shimai albarka, gaidashi dijah tayi ya amsa, "Hamzariee yace Inna batadai cikaki da surutu ba KO? Dariya Inna tayi tace ah ah, "dijah tace Inna zantafi skul sainadawo, Inna tace inane skut dariya dijah tayi tace makaranta Inna, Inna tace a dawo lapia, "suka sa kai suka fita, cikin mota dijah kegayama Hamzariee k'auyancin da Inna keyi yanata dariya, "Niko feedoh nace dijah harta manta sanda tayi natk'auyancin🤔, "suna fira harsuka iso premier suna shiga gate olrdy har anshiga exams hall, dasauri dijah ta bud'e mota, rik'o hannunta yayi, yace ina nan ina jiranki harki gama, dijah tace saifa 3pm zangama cz paper biyu ce, hamza yace karki damu my babe, zan tsaya d'aga mashi kai tayi tace shikenan, murmushi yayi tare da manna mata kiss a kunci, lumshe idanu tayi, "dasauri tashiga hall, tana zama aka bata questions paper da booklet,

*****************************
Hmmm soyayya gamon jini, Hamzariee yana nan, jiran dijah saidai sallah kawai dayaje yayi cikin skul d'insu, "ukku saura aka fara fitowa daga hall, can saiga dijah da k'awayenta sunfito, murna cike da fuska, pix d'in tarihi suka farayi, sunata selfiee daga bayanta taji yace kawo na d'aukeku, juyowa tayi tafad'a k'irjinshi, shiko ya rungumeta, kuka take sosai, skul mate sai ihu suke suna tafi, "dakyar yasamu tadaina kuka, pictures yadingayi masu harsaida dijah tace tagaji, "bankwana tama k'awayenta da alk'awarin kawo masu iv idan biki yatashi, hannunta yakama suka tafi wajen mota, besty d'inta ce Firdausi ta rakosu wajen mota, "dijah tace besty sai yaushe, Firdausi tace besty zadaimuyi waya kawai, "mota dijah tashiga tana d'agama Firdausi hannu, "dayake tun zuwanta premier Allah yahad'ata da Firdausi tasu kuma tazo d'aya saboda itama feedoh batada hayaniya, kamar dijah, mafarin k'awancensu kenan....

Suna tafiya suna fira, hamza yace Allah nifa yau zanma baba magana asaka bikinmu, ina dalilin ace saina jira wasu, "dariya dijah tayi tace toh miye danka jirasu, hamza yace aydama kinfad'i haka, "nidai kike k'in ba goyon baya KO? Haba yarinya aykinzo hannuna, naga tayanda Ammi d'in zata kwaceki, itadai dijah dariya tayi, "hanyar maitama taga yayi, itadai batace mai miyasa zasuje can ba, dantasan halin kayanta, "harsuka iso batacemai k'alaba, saida sukazo bakin gate ya juyo yace yanmata banji kince ya akayi mukazo man ba, dijah tace ni nayi magana ka juyata, dariya yayi yace aww juya magana nakeyi kenan, daidai ya cinna kan mota cikin gidansu, "kujeru tagani farfajiyan gidan anyi decorating wajen sosai, itadai asaninta tasan ba abinda yafaru, "juyowa tayi tace ya hamza mi halan naga anti decorating, tab'e baki yayi yace nimafa bansaniba, amma kina iya shiga ki tambaya Ammi d'inki, mayb taro takeyi, "itadai jinshi takeyi, saboda tasan yasan komai yadai k'i gayamata, "dijah tace shikenan, ta bud'e mota tafita, hanyar cikin gida tayi nan ma ta tarda mutane.......

www.Phirdauceejeebo.mywaoblog.com

IG: yar_ficika

Written by
           Feedoh Deedoh✍🏻✍🏻

Comments

Popular posts from this blog

HUDAH 01~25

RASHIN GATA 1-5

RASHIN GATA 176-180