DIJAH 181~185
🏵🏵DIJAH🏵🏵
Feedoh yanmata✍🏻
1⃣8⃣1⃣~1⃣8⃣5⃣
Wuri tasamu bisa gado Ammi tazauna, "fuska d'aure tacema hamza naji duk abinda kuke ciki, kuma da sanadiyar canjawarka, "yanzu Hamzariee kayimana adalci kenan? "Karasa wadda zakaso sai wanda bamusan wacece itaba, ita kanta batasan waye itaba, ita kakeso muhad'a zuri'a da ita? Sanin kanka ne yanda na kwallafa raina akanka miyasa bazaka samo yar asali ba, duk matan dake garinnan, amma ka rasa wadda zakaso sai tsintacciyar mage, sakkowa hamza yayi k'asa yace Ammi kiyi hak'uri ki gafarceni, wlhi bansan ya akayi nafara santaba, "da soyayya tayi shawara dani kafin ta shigeni, danace tayi hak'uri saboda insamama dijah farin ciki, "saboda farin cikinta shine nawa, kuma Ammi koda ba musan dangin dijah ba ayzaman da mukayi da ita yakamata muga irin kyawawan halayenta, "kuma koda ita shegia yace ayba laifinta baneba, kuma wlhi inaji ajikina dijah nada iyaye kamar kowa, "kuma yanzu idan wani yazo neman aurenta baniba shikenan bazaki bashiba saboda bamusan asalinta ba? Kanshi ya d'ora bisa cibyarta yace Ammi kiyi hak'uri karki rabani da dijah, wlhi dijah tazama wani b'angare na jikina, dan wlhi rabuwa da dijah d'aya yake da rabuwata da duniya, kuka yafashe mata dashi, tabbas tasan duk abinda yafad'a gaskia ne, kuma harda sakacinta, saboda yakamata ace tasaka idanuwa akan shak'uwarsu, amma tayi sakaci, shafa kanshi tayi tace shikenan Hamzariee naji, bankuma isa nahana abinda Allah yayiba, saidai kasani nibazan yanke hukunci nikad'ai ba, saida sanin mahaifinku, rungumeta hamza yayi yace nagode Ammi, Allah ubangiji yaja da rayuwarki, tace Amin.....
Daddy na dawowa Ammi takwashe abinda yafaru tagaya mashi, shiru yayi yace ikon Allah, wata jarabawa ce kuma ta samemu, "Ammi tace nibanma san yazanyiba, "daddy yace Ammi adua zamucigaba kuma ni koke bamu isa muhana abinda Allah ya k'addara ba, dan haka mucigaba da adua kawai, yanzu abinda za'ayi ki kiramansu Ammi tace toh, tatashi, d'akin hamza ta shiga fitowarshi daga wanka kenan, tace idan kagama daddyn affy na kiranku, hamza yace toh, "dakin dijah ta wuce tana nan kwance tunda d'azu data shigo d'akin idanuwanta sunyi kumburi saboda kuka, sallama Ammi tayi, saida gabanta yafad'i, a sanyaye ta amsa, "wuri tasamu Ammi tazauna, tace yanzu dijah kin kyauta kenan, ace duk yau baki fitoba, har affy na aiko kiranki amma kika k'i zuwa, kalli idanuwanki, kowa yaganki yasan kinyi kuka, "shikenan tunda haka kika zab'arma kanki, idan kingama kukan kitashi daddynku yana Kira, bata jira ansawarta ba tawuce abinta...
*****************************
Koda taje parlor daddy ta iske su Hamzariee, kusa da affy tazauna, shiko tunda tashigo yake kallonta, yau kad'ai tarame, duk saiyaji haushin kanshi, tunda gani yake shiyaja mata, "gyaran murya daddy yayi, yace hamza naji halin da kuke ciki kaida dijah saboda Amminku tagayaman komai, "kumani bazan hanaka dijah ba wai dan saboda bansan iyayentaba, "koda bansan iyayenta ba, nasan tasamu tarbiyan kwarai wajen wanda suka rik'eta, "kuma bazanyi jayayya da abinda Allah ya hukunta ba, amma ina rok'onku dakuban d'an lokaci, "kuma dijah karkisa damuwa a ranki, kicigaba da d'aukarmu kamar iyaye, "hamza kayi hak'uri kaban lokaci, idan lokaci yayi, zantambayi dijah idan har tanasanka in shaa Allah zanbaka ita, "hamza yace daddy nagode, kallon Ammi yayi, yace Amminah bakice komai ba, murmushi tayi tace karkadamu yaro Nah, ay daddy yagama magana, "kuma in shaa Allah za'abaka farin cikinka, rungume Ammi yayi yana dariya, itadai dijah kanta na k'asa, Affy kuwa sai tsokanarsu takeyi, "daddy yace dijah kinyi shiru, murmushi tayi tatashi da gudu, dukansu dariya sukayi, affy tace walle bruh kayi dacen mata mai kyau fa, Ammi tace masha Allah dai, kar acinyeman d'iya, dariya sukayi...
Fad'awa tayi bisa gado, tabbas itama tasan takamu da san hamza amma batasan tun yaushe ba, "kuma tasan bazata iya daina sanshi ba, "d'akin taga anshigo amma takasa d'aga ido saboda kunyarshi datakeyi yanzu, kusa da ita yazauna yace yanmata bakiji ina sallama ba, batace komai ba, "murmushi yayi yace Khadijah amsawa tayi, saboda tasan duk sanda yakirata,da Khadijah maganace mai muhimmanci, hamza yace tashi zaune magana zamuyi, tashi tayi, hamza yace karkiji komai kigayaman gaskia idan kinasona, kuma wlhi idan bakisona karkiji kunyar gayaman, ammafa saikin gayaman miyasa bakisona, a hankali tace ya hamza kabari sainayi shawara, hamza yace waye abonkin shawaran inacewa nine? Toh wlhi yau zakigayaman kuma yanzu, shiru tayi, "yace wlhi idan zamu kwana nan, saikin fad'aman tasan halinshi, "cikin jin kunya tace ya hamza inasanka, san da bansan yaushe nafaraba, ya hamza yanda nakeji yanzu wlhi my life iz not complete without u, tana kaiwa nan tabar d'akin da gudu, ihu yayi, yace ashe itama tanasona Allah nagode maka, dakaban kamilar yarinya, Allah yasa tazama matata, "nikuwa deedoh nace Amin......
www.phirdauceejeebo.mywapblog.com
IG: yar_ficika
Written by
Feedoh Deedoh✍🏻✍🏻
Comments
Post a Comment