HUDAH 111~115

⭐⭐HUDAH⭐⭐

Na
     Feedoh & meesha lurv

1⃣1⃣1⃣~1⃣1⃣5⃣

Bayan ya tafi gida ta dawo, tana shiga ta iske maaah, zaune kusa da ita ta zo ta zauna tace wash maaah, wlh duk nagaji maaah tayi murmushi tace "Hmm kya fad'i gsky babu wata gajiya kawai bakisan rabuws ne da naufal" murmushi HUDAH tayi ta sadda kanta k'asa tace "kullum maaah sai kinsani kunya ankan naufal" maaah tace ae gsky na fad'a tun zuwan naufal ya kwace man ke komai sai kice naufal ni andaina ambatar maaah HUDAH wayyo maaah "Dan Allah kidaina fad'a" maaah tayi dariya tace bazan daina ba sai nafad'i gsky HUDAH tace shikenan bari natashi nashiga d'aki tunda baza ki bari ba, maah tace gashi kuwa zaki tafi d'aki Dan nayi maki magana da kafin naufal yazo ae komai zanyi baki tafiya, da gudu ta fita tabar wajen maaah tayi d'aki murmushi maaah tayi tana mai k'ara godewa Allah dayakawo masu farin ciki da annashuwa.

******************
Fady ce zaune da HUDAH suna hirar yadda shagalin bikin nasu zai kasance dayake naufal iyayensa har sun zo, anyi maganar auren daddy ne ya anshi komai na bikin HUDAH shida yan uwan Abbu daya musu waya sukazo asa biki wata uku masu  zuwa ba haka naufal yaso ba yaso asa bikin sati biyu Dan ya matsu yaga HUDAH tazama mallakinsa wani sonta sai k'ara tsirgashi yake had'e da tausayin ta Dan yana mugun tausayin ta akan cutar da faruq yayi mata kullum yayi sallah sai, ya rok'i Allah yasaka ma HUDAH akan abinda faruq yayi mata yanaso yaga k'arshensa tun a duniya kafin aje lahira, maaah kwarai takeson naufal saboda nutsuwar sa uwa uba rik'o da addinsa duk dayasan miyafaru da HUDAH kwata kwata be kyamaceta ba sai kara sonta dayayi.

Shiyasa tayi murna Dan tasan HUDAH tayi sa'ar miki Allah yadubi halin datake ciki yakawo mata mijin marainiya, yadubi maraicinta yakawo mata miji mai nagarta shiyasa kullum tayi sallah sai ta rok'i Allah da yabasu zaman lfy yasa naufal alk'ari ne gareta, in kuma sharri ne Allah ya Kawo mata mafi alkairi Allah ya anshi addu'arta kuwa shiyasa kullum cikin k'ara godewa Allah takeyi da zuwan naufal garesu, daddy yaji dad'i zabin HUDAH Dan mutane ne masu karamci da hangen nesa Mamy fady dataga irin kud'in da aka bar zuwa maganar aurenta tasan ba kananan mutanene ba taji bak'in ciki sosai bataso HUDAH taaamu cigaba ba tason yadda ta tsanesu suk'are a taulaci datasan yadda zatayi da tuni tacanza naufal yadawo gurin d'iyarta fady amma tasan yadda  zatayi auren ya waste tayi k'wafa ta tashi daga inda take.

Fady tace gsky HUDAH dole ayi shagali bana wasa ba Dan inajin sai munyi perty wajen kala biyar HUDAH tace bakinku d'aya da AD shima haka yace wai dole achashe, bikin autan papa da mammy ace za'ayi shi shiru ae bazai yiwu ba har k'ara fad'i yake Dan kar nace wani Abu, dariya fady tayi sannan tace ae tasan halin ustazanciki, HUDAH tace lalle fady sharri zakiyiman fady tace bawani sharri gaskiya na fad'a suna cikin  hirar taji wayar tayi k'ara dubawar dazatayi taga AD ne yakirata da murmushi ta d'aga tace hello cikin farin, ciki yace princess wlh nayi kewar da yawa yakasa d'aurewa weekend yayi tace haba AD na yaufa laraba, sauran kwana biyu fa, yace haba yanmatan AD wlh bazan iya ba, yanzu haka INA hanya nakusa shiga, kt tace dagaske kake? Yace wlh da gaske dahaka kuyiman girki mai dad'i Dan agidan maaah zanci abinci tace Mashi toh sun, tab'a Yar hira sannan takashe wayar tafad'awa fady komai, tace tashi muje ki tayi had'a masa abinda zaici.

Www.phirdauceejeebo.mywapblog.com

Written by
               Fiddausi Abdul'azez (Feedoh)  & Ayeesha Musa (meesha lurv).

®NWA®

Comments

Popular posts from this blog

HUDAH 01~25

RASHIN GATA 1-5

RASHIN GATA 176-180