JINSINAH 116~120

❄❄ *JINSINAH*❄❄

*_Feedoh_*  *_yanmata_*✍🏻

*_page_* 1⃣1⃣6⃣ *_to_*1⃣2⃣0⃣

Shiru Amir yayi yarasa mike mai dad'i, amir yace mushiga daga ciki, maigaidai shigar da kayanta ciki, da sauri maigadi ya amsa ya d'auki kayanta, amir ne yaba mai napep 3k amsa yayi yana godia, saida safe yamasu yaja mini jeep d'inshi yayi gaba,,,,,,

              "Anty na zaune parlor taga anshigo da kaya, tambayan maigadi tayi tace waye, maigadi yace Hajia bansanta ba, "kafin ta sakemashi tambaya su finah sunshigo, sallamar finah yasa ta d'ago, ganin finah datayi yasa tamik'e zumbur, tana lafiya? Shiru babu Wanda yace da ita komi, 'zuwa Anty tayi wajen finah tace fad'aman miyafaru, kuka tafashe dashi tace Anty sakina yayi, wani irin razana Anty tayi tace wane irin Saki, ya akayi ya sakeku, miya had'aku, kuka yaci k'arfin finah, amir yace Aysha bari tazauna saiki Mata tambayoyin, janta tayi ta zaunar da ita amsar arif tayi dayake ta bacci d'aki takaishi ta kwantar dashi kana tadawo parlor, "saida finah tayi kuka mai isarta kana tace bawani abu ya had'amu ba asalima shikanshi bada niya yasakeni ba...... Takwashe komai tagaya masu, "zaro takardan tayi cikin hand bag d'inta ta mik'ama amir, karb'a yayi ya bud'a ya karanta ga abinda ke ciki,,,,,

      "Ni Muhammad na saki matata nafisa saki d'aya, batare da wani laifi ba mahaifiya tace ta matsaman, "amma in shaa Allah sai nafisa tadawo gida na inaji ajikina nafisa itace rayuwata,,, "nyt tace ayko ko shine autan maza kingama aurenshi "kallonta  amir yayi yace badai zaki fasa halinki ba, mata nasan mijinta zaki fad'i haka, kudai muyita adua, "Anty tace tashi kitafi ki kwanta,,,,,,,
                  ********

           "Tunda finah tashiga d'aki take kuka, "tashi tayi ta d'oro Alwallah tazo ta kabbara sallah, tana gama sallah tafara jero adu'on neman sauk'i cikin ikon Allah taji zuciyanta tafara samun natsuwa, "bata kwanta ba saida tayi sallan asuba, nan fa bacci mai k'arfi ya d'auketa, arif yatashi yanata kuka amma tana ta bacci, Anty ce tashigo jin kukan arif, ganinshi tayi yana kuka, itako finah nata bacci, d'aukanshi tayi suka fita, wanka tamashi, tabashi madara yana gamasha ta goyashi, tana goyashi Yakoma bacci, amir ne ya shigo yace ah ah su Anty goyo akayi, dariya tayi tace bacci takeyi, shikuma yatashi yana kuka, amir yace baccin gajiya ne da b'acin rai,,,,,,,,

           "Firgigit ta tashi saboda wani mummunan mafarki datayi, "salati tayi, "agogon dake gefenta ta kallah d'aya saura tagani, a hanzarce ta tashi tashiga toilet tayi wanka, tana gama wanka ta d'auro alwalla fitowa tayi, tana fitowa Anty tagani zaune, murmushi Anty ta Mata, tace harkin tashi tace eh natashi, gaidata tayi Anty ta amsa, "mik'a mata arif tayi tace bashi ya sha, amsarshi tayi tabashi nono ayko kamar jira yake Yakama, "kallonta Anty tayi da kyau tace finah kina cikin damuwa kiyi hak'uri, ki d'auka k'addaranki ce haka, finah tace wlhi Anty yawuce mummunan mafarki nayi shiyasa kika ganni haka, anty tace mafarkinmi? Finah  tace mafarki nayi wai mahaifita ta ta haukace ta ruga ta fad'a daji, dafata Anty tayi tace in shaa Allah ba abinda zaisameta, kibari idan akwana biyu saikije ki dubata, d'aga kanta finah tayi kawai, arif nagama shan nono Anty ta amsheshi tafita,,,,,


         "Bari mulek'a gidan moh muga wainar da ake toyawa,,,,,,,,,

Moh ne zaune gaban umma, Umma tace yakamata kasamo masu aiki dandai kasan Fadilah bata iya komai ba, Moh yace shikenan Umma kibada cigiya, "tashi yayi yace bari naje office Umma tace adawo lafiya,,,,,,


             "Fadilah ko tunda abinnan yafaru take cikin wani irin annashuwa, "habiba ce tashigo da sallama, rungume juna sukayi, suna murna, habiba tace ya akayi, fadilah tabata labarin komai, ihu habiba tayi tace alhamdulillah mungama wannan saura mataki na k'arshe, kallonta Fadilah tayi, habiba tace kwarai matakin k'arshe,,,,

Wajen malam zamu koma yabaki maganin da za'a janye hankalin Muhammad akan finah saboda idan ba janye hankalinshi akayi ba yana iya shawo kan mahaifiyarsh ta yarda yamaidota, amma kinga idan yana hannunki sai yanda kikace ke amallake makishi ko uwarshi bata isaba bare finah, kings idan akayi haka shikenan yazama naki, rungumeta Fadilah tayi tace wlhi shiyasa nake sanki, akwai hangen nesa, yanzu yaushe zamu habiba tace inma kin shirya gobe saimuje, Fadilah tace a shirye nake,,,,,

*_Dedicated_* *_to_* *_biebee_* *_isa_* ❤

IG: yar_ficika

© *_written_*  *_by_*
              *_Feedoh_* *_Deedoh_*✍🏻✍🏻

Comments

Popular posts from this blog

HUDAH 01~25

RASHIN GATA 1-5

RASHIN GATA 176-180