HUDAH 26~55
[4/8, 15:32] Feedoh: ⭐⭐HUDAH⭐⭐
Na
Feedoh & Meesha lurv
2⃣6⃣~3⃣0⃣
Wazan gani, ya Farukh ne nayi karo dashi ya fincikoni, ya dakaman tsawa, saida Meesha tasaki fitsari niko Feedoh bansan sanda nayi waje da gudu ba, yaceman ke dabba inace dabaki tafiya a hankali,nace ya Farukh kayi hakuri bangani ba, ban ankara ba ya wanka man marin dasai da nakusa sakin fitsari, yace uban waye yayan naki, diyar matsiyata dake, shin wai bama na hanaki zuwa gidannan ba, cikin kuka nace kayi hakuri dama Abbu ne yaban tsaraba yace na kawowa fady
Yace koma dashi kice ba,aso, ko ance tana buk'atar Tsiyarku, ya hanka d'ani waje daidai farida nazuwa, tasaki wata k'ara tana kirana niko ko juyowa banyiba, ya dakama fady harara yace koma gida kona karyaki, fady takoma gida tana hawaye.
Niko koda na fad'a gida ban tsaya ko inaba sai daki, ina kuka saiga Maaah ta shigo tace Huda lapia? Na kwashe yanda mukayi da farukh nagaya mata, Maaah ta dafani tana murmushi tace HUDA kiyi hakuri duk abinda hajia da farukh suke maki watarana sai labari, nace Maaah miyasa suka tsaneni Maaah tace huda ba tsanarki sukayi ba, kidaiyi hak'uri, kinga tashi ki wanke fuskarki kar Abbu enki yadawo ya tardaki haka bazaiji dadi ba, nace toh maaah, Maaah tace yawwa hudan Abbu Allah ya maki Albarka na amsa da Ameen Ina murmushi.
Daga tsakar gida mukaji sallamar fady, tana kwalaman Kira, Maaah tafita tsakar gida tana murmushi tace toh yar gidan huda shiga tana d'aki, farida tagaida Umma , kana tashigo daki, na kalleta nayi dariya, ta harareni, nace besty minayi, tace bansaniba nace plz tace shine kinaji ina magana kika taho kika kyaleni, nadafa fady nace besty kiyi hakuri, nima bada san raina bane, ya Farukh ne yace na fita, fady tace shine zaki biyemai Allah saina hadashi da daddy, na b'atarai ne farida kika fadama daddy abinda yaya Farukh yaman bani bake, fady tace yanzu dan zanfada ma daddy abinda yamaki shine zakice haka?nace "Eh" na batarai fady ta dafani tace shikenan besty nafasa fadan nace yawwa besty thanks, haka muka cigaba da labari da zata tafi gida na d'auko tsarabanta na bata ta amsa tana murna narakata har bakin gate ensu....
Haka rayuwa taita tafiya, muna kara girma kyau nak'ara fito mani, ina k'ara zama budurwa gawani boyayyen kyau da Allah yabani, bawata doguwa baceba kuma banda k'iba amma nafi babylabo😜 yanzu haka muna ss2 nida fady, ranan muna skul munfito break na dingajin gabana na faduwa, nace fady Aminiya nikam gabana ke fad'uwa taceman cigaba DA innalillahi wa Inna ilaihir raji'un haka nacigaba da maimaitawa, amma maimakon yadaina saima ya karu, ranan trueout nakasa cin komai haka fady duk tadamu itama takicin komai, a haka dai har akatashi, akazo daukarmu nidai gabana sai faduwa yakeyi mun karyo kwana gabana ya tsananta fad'uwa bansan sanda nafashe da kuka ba, duk suka juyo suna kallo na....
Lurv u Meesha
Written by
Fiddausi Abdul'azeez (Feedoh) &
Ayeesha Musa (Meesha lurv).
[4/8, 15:32] Feedoh: ⭐⭐HUDAH⭐⭐
Na
Feedoh & meesha lurv
3⃣1⃣~3⃣5⃣
Hakuri fady ke vani taja hannuna mukayiwa sauran yan class d'inmu sallama duk ransu ba dadi sukaci gaba da bani hakuri ahaka muka rabu, muka karaso k'ofar gida, nan fady tayiman sallama tace anjima zata shigo nak'ara hak'uri ba'abinda zai faru dani sai Alkairi nidai jinta kawai nakeyi danni kad'an nasan yadda nakeji nan muka rabu na shiga gida, da guntun hawayena inashiga nayi sallama.
Maaah nazaune tsakar gida da sauri tad'ago kai takalleni jin yanayin muryata ya chanza sallamar ta ansa sannan ta taso ta tareni tana mai cewa lafiya HUDAH naganki haka, ko wani Abu ya faru dake kuka nak'ara fashewa dashi, na rugume maaah saida nayi mai isata maaah bataceman komai ba saida ta barni nayi mai ista sannan ta lallasheni har nayi shiru sai ta tambayeni meyasani kuka nan nafad'a mata duk abinda yafaru dani d'agowa maah tayi tana kallona Ashe itama tun safe takejin fad'uwar gaba dakewa kawai takeyi nan tad'aure ta k'ara lallashina, tace bakomai idan naji haka nayi ta addu'a nan tajani zuwa d'aki na cire kayana nayi alwala nayi sallah bayan na idar da sallah nad'anyi azkar sannan na fito parlour.
Nan maaah tad'aukoman abinci tace naci nace nikam maaah nakoshi banji yunwa dataga dagaskenake, sai tasa hannu ta ce nasa muci tanayiman hirar abin dariya tuni na ware ina uwar dariya kance mi har naci abinci sosai.
Muna cikin hira kawai sai mukaji sallama, kirar sallah la'asar naufal nakalla nace, lokacin sallah yayi yakamata kaje kayi sai muci gaba murmushi naufal yayi sannan yace d'aukon ruwa nayi alwala, nace toh natashi nashiga gida nad'aukomai ruwa nakawo masa bayan yayi alwala yatafi masallaci niko gida nashiga Dan gabatar datawa farilla ina shiga nayi alwala nayi sallah bayan na idar nan muka fara hira da maaah suna cikin hirar akayi sallama yaro ne yashigo yace ana sallamah da HUDAH nan tace tana zuwa, nan ta d'au hijabinta ta fita niko meesha Dana bitta waige waige na kafa idan zan hango feeedoh can na hangota wajen wani yaro da wara a hannusa tana so yabata shiko yayi mirsisi, da masifa nayi wajenta nace to uwar kwadayi ko ina sai anuna hali idan kingama kwadayi sai kiboyeni kar HUDAH tawucemu har tafito juyuwa tayi tana cewa toh naji muje amma Allah ya is a kihanani na'ansa, nace kyaji dashi kwad'ayayya nayi gaba nawuce wajen HUDAH.
Lurv u Feedoh
Written by
Fiddausi Abdul'azeez(Feedoh)&
Ayeesha Musa (meesha lurv)
®NWA®.
[4/8, 15:32] Feedoh: ⭐⭐HUDAH⭐⭐
Na
Feedoh & Meesha lurv
3⃣6⃣~4⃣0⃣
Huda tafito tasami naufal inda suke zaune, tamai sallama ya amsa yana murmushi, Huda tace ya naufal kamar kagaji ko? Ko mubari sai gobe muk'arasa, naufal yace ah ah gaskia my princess nak'i wayon nidai zauna ki k'ara saman, huda tayi murnushin karfin hali tace toh shikenan
Muna zaune da maaah mukaji sallama, Maaah ta kalleni na kalleta muka kasa amsa sallamar can mukaji ankara, Maaah ce tayi k'arfin hali ta amsa sallamar, ta kalleni tace autar abbu jekiga wake sallama, nace toh natashi jiki sake na fita, nace ma mutumin aykuwa abbu bayanan, yace dama wajen mamanki nazo tana kusa? Na kalleshi sosai dan dai ni gaskia bansanshiba, nayi karfin hali nace "Eh tana ciki yace to ce tayi bako, nakoma gida nace ma Maaah dake ake sallama tace nikuma? nace haka dai yace, tace bani hijab ena, na daukoma ma hijab tafita, suka gaisa, tace malam bangane kaba yace gaskia baki sanni ba, kece matar malam Abdallah Maaah tace "Eh, yace dama bawani abu baneba illa..... bai ida ba saiga Alh Umar yafito yace maaah lapia kike tsaye nan? Maaah tace sallama yayi danine Alh Umar yace malam lapia kake sallama da ita, mutumin yace lapia amma ba lau ba, amma tunda gaka namiji Alhamdulillah muje kaji sakon, Alh umar ya gyada Kai yace to, Maaah koma gida gani nan shigowa maaaah tace toh ta juya jiki ba kwari..
Yace Alh dama ba wani abu baneba mai gidannan daine yayi accident kuma shine yabamu addrst en gidan, Alh Umar in banda innalillahi wa Inna ilaihir raji'un ba abinda yake fada duk ya rude yace bawan Allah yanzu yana wane asibiti? yace yana federal medical centre yace toh muje kawai Allah sarki alh duk ya rude ya manta ma yashiga gidan yama Maaah bayani, makwabcin arziki kenan, suna isa hsptl en ba inda suka nufa sai emergency, koda suka shiga, Ina rai yayi halin shi Allah ya dauki ran bawansa, alh kuwa ya rude inbanda kwalla ba abinda yakeyi da kyar aka shawo kan alh, akayi abinda za'ayi akabashi gawar makwabcinshi suka taho, koda suka shigo Layinmu saiga mutane kamar anfada masu ganin alh da gawa kowa yayo kanshi suna alh lapia? Nan yafada masu abinda yafaru, mutane nata salati suna fadan kyawawan Alh Abdallah..
Mu maaah na zaune tsakar gida muka ga anshigo da gawa, Maaah ta tashi tace dama nasani, wlhi naji ajikina akwai abinda zai samemi Ashe babban rashi zanyi, bangon da muka jingina nida 'yata yafadi nidai huda nakasa fahimtar zancen Maaah kawai Ina binta da kallo ne, natako nazo gaban alh, nace daddy lapia? daddy ya saukar da kanshi k'asa saboda wani kuka dayaji yataho mai, yadago ida nuwanshi da suka rine suka canja Kala, yadafani yace diyata kiyi hakuri kinji, kisama ranki dangana yanzu ba abinda abbu ke bukata wajenki sai adua nace daddy banfa fahimce ka ba, yajani muka zauna yace HUDA nace naam yace man kiyi hakuri Allah yayima abbu rasuwa, yanda naji maganar kamar dirar mashi,nace daddy wace irin rasuwa kuma? yaufa da safe saida yaman nasiha kafin natafi makaranta, daddy yadafani yace hakuri zakuyi abbu yarasu, nace innalillahi wa Inna ilaihir rajiun na bude fuskar abbu naganshi kamar namai magana ya amsa, narushe da kuka nace abbu katashi dan Allah wlhi kaine gatanmu bamuda sauran gata yanzu, ji nayi andafani
na dago muka hada ido da fady, tafado jikina ta rungumeni muka dinga kuka, nace farida kinga abinda zai sameni ko? Shiyasa gabana keta faduwa, farida kings nayi rashi ko, yanzu banda sauran gata, banida Wanda zangani nakira da sunan abbu shikenan nida abbu Maaah ta dagoni ta rungume muka cigaba da kuka..
Haka aka shirya abbu gabana aka dauke shi za'a kaishi gidan gaskia, nace Maaah kina gani zasu tafi dashi, fady ta rikeni tana hawaye Maaah naman nasiha, da in dauki dangana,Ana fita da abbu na yanke jiki nafadi....
Lurv u Meesha
Written by
Fiddausi Abdul'azeez (Feedoh) &
Ayeesha Musa (Meesha lurv).
[4/8, 22:00] Feedoh: ⭐⭐HUDAH⭐⭐
Na
Feedoh & Meesha lurv
4⃣1⃣~4⃣5⃣
Idona nafara bud'ewa ahankali dishi dishi nafara gani, hoton abinda yafaru ya fara dawoman kuka na fashe dashi da k'arfi, da sauri maaah ta matso kusa dani tana cewa, "HUDAH har kin farka fareedah maza jeki ki kira likita kinji" da sauri fady ta fita HUDAH tace maaah dagaske Abbu ya mutu maaah mafarki nake ko maah?nidaman nasan mafarki ne ba gaske ba nasan dama karya suke da su kace Abbu ya mutu, maaah kuka take sosai ta ga gari magana.
HUDAH ta girgiza maaah tace maaah kiyi magana kice karya ne Amma, tagaza cewa komai nak'are cewa maaah baza kiyi mgn ba, doctor ne ya shigo nan yak'ara dubani sannan yace "alhmdllh komai ya zama normal dama firgince datasamu yasa ta suma Amma yazo komai yayi sauki" zaku iya tafiya yanzu bari abaku sallama nan ya fita maaah tacewa fady ta had' a kayan nan tahau had'awa niko in banda kuka babu abinda nake ina kallon maaah lokaci lokaci tana share hawaye haka doctor yazo ya bamu sallama Sannan yace nasha maganina akai akai.
Nan mukayi sallama da gadon kusa damu muka fito daddy muka ci Karo dashi a haraba asibiti, nan yace yadai Hadiza ko abaku sallama ne, nan maaah tace wlh alhaji yanzu suka sallame mu, yace to kuzo mukoma gida nan nida fady muka gaishe shi nan ya'ansa da fara'arsa, nan yace HUDAH jiki yayi sauk'i ko? Nace masa eh daddy yace toh Allah k'ara afuwa yasa zakkar jikine nida fady muka'ansa da amin.
Daukar mu yayi direct gida muka wuce jama'ar dana gani k'ofar gida shi ya tabbatarmin dagaske, Abbu ya rasu wasu zafafan hawaye masu zafi sun zubomin dakyar na iya Jan k'afata nashiga gida, nan natarar da jama'a sosai nayi kuka bakad'an ba kullum maaah da daddy nayi man nasiha "sosai na rame tazama wata shiru shiru duk yadda nake da jama'a da hayaniyata duk ta tafi," nazama bana magana sosai ko yaushe shiru nake har Abbu yayi sati biyu da rasuwa komai Nagida da Ka sani toh daddy keyimana shi kullum ya fita da abinda ke kawoman yazo yanayiman hirar abin dariya har sai na sake yake tafiya, wani abin mamaki tun rasuwar Abbu ya faruq yake sakeman kullum sai ya shigo gidan yakawoman abubuwa da daddy ya fita shi Kuma sai ya shigo su zauna da maaah suna hira har taya maaah aiki yake yi tun abin na bani mamaki har na dawo na daina wasa wasa nafara sakewa dashi, haka zai fita damu nida fady yayi mana siyayya yazaga damu gari sosai, duk dadi yakamamu gani, Ya faruq yafara sake mana wata rana ina zaune tsakar gida maaah na d'aki ya faruq ya shigo yana zuwa na gaishe shi nan yake ceman anjima zai dawo akwai maganar da zamuyi nan nace masa toh sai yazo nan yajuya yafita.
Luv u beeboh
Written by
Fiddausi Abdul'azeez(feedoh) &
Ayeesha musa (meesha lurv).
®NWA®
[4/10, 19:10] Feedoh: ⭐⭐HUDAH⭐⭐
Na
Feedoh & Meesha lurv
4⃣6⃣~5⃣0⃣
Bayan ya faruq ya fita, nayi shiru ina tunanin maganar mi zamuyi dashi, haka dai na karasa tunani na narasa amsa, Ina nan zaune naji andafani nad'ago naga Maaah naman murmushi tace, wai bana hanaki tunani ba? nace maaah bafa tunani nakeba, kawai dai nayi shiru ne, Maaah ta girgiza kanta dan bata yarda ba, tace toh naji, ni zanje gidan hajiya sadiya amma baxan dade ba, nace toh Maaah ena saikin dawo, Maaah tace Allah yasa, tasakai ta fita
Ina nan zaune inda maaah tabarni, naji anyi sallama na na amsa sallamar tare da d'aga kaina, tsaye yake yaharde hannuwanshi bisa k'irjinshi yasakarman wani murmushi, bansan sanda na sadda kaina k'asa ba, yatako yazo gab dani ya tsugguna gabana, ina jin numfashinshi, ya dafaman kafada yace Huda baby, yaukuma kunyar bro akeyi, dayake dama tunda muka shirya huda baby yake ceman, nakasa d'ago kaina yace man bby dake fa nake magana kinyi shiru, a hankali na dago kaina nace ya faruq ina wuni, yaceman nabaroshi gida, bansan sanda nasaki murmushi ba, yace man yawwa kokefa my darlin sis, yace dama namaki alkawarin zandawo cz ina da maganan da zanyi dake, na gyada kaina..
Yaja hannuna muka shiga parlour na zauna yadawo gabana ya zauna ya kuraman ido harsaida na tsargu, na huramai ido nace bro kayi shiru, ya maida wani numfashi tare da wani malalacin murmushi, yace Huda kinsan dalilin dayasa nace inasan magana dake? Na girgiza kaina nace ah ah bro
Yace HUDAH tun bayan rasuwar malam Allah ya jarabceni da wani, abu nakasa yarda da zuciyana saboda gani nake kamar ba gaskia baneba, saida ga baya nagane yaudaran kaina nakeyi, dole na gasganta abinda zuciyana ke fadaman, nidai huda nabi ya faruq da Ido, saboda gaskia bansan ina ya nufa ba, cikin wata murya naji yakira sunana saida tsikar jikina ta tashi.
Yace Hudah Hudah bazan iya boye maki ba, saboda zan cutu da yawa, nace ya faruq Allah bansan ina wanan maganganun naka suka nufa ba, plz ka fito kagayaman yanda zangane, ya faruq yaja wani gwauron numfashi, tare da riko hannuna yace HUDAH ina sanki, kuma ba san wasa ba bansan tun sanda nakamu da sanki ba, nad'ago idanuwa da suka juye nace ya faruk nikuma kakeso? Kamance wacece ni, nifa ba kowa baceba d'iyar matsiyata ce dan Allah kadaina wannan maganan, ya faruk yace Huda bazan takuraki ba da kisoni, amma one things da yakamata kisani nidai faruk ina sanki, kuma ashirye nake da karban duk hukuncin da zakiman na wulakantaki baya da nayi, nafisge hannuna zan gudu, da sauri ya fizgoni nafada jikinshi, yamatseni bansan sanda nafara kuka ba ina ya faruq plz kasakeni, yayi murmushi kana ya sakeni yace na barki kije kiyi tunani komi kenan lemme knw kinji bbynah, ya mike yana murmushi yabar gidan...
HMl my Bestiee Maryam Muhammad Tsamiya May Allah bless ur marriage, walle am gonna mssn 😭😭😭
Written by
Fiddausi Abdul'Azeez (Feedoh) &
Ayeesha Musa (Meesha lurv).
[4/11, 19:46] Feedoh: ⭐⭐HUDAH⭐⭐
Na
Feedoh & meesha lurv
5⃣1⃣~5⃣5⃣
Mutuwar zaune tayi Dan ya faruq yayi masifar bata mamaki, bata tab'a tunanin zaizo mata da irin wannan zance sai gashi yazo mata dashi, anya kuwa ya faruq bai fara shan wani abuba? Tayi kanta wannan tambaya SBD tasan duk duniya babu Wanda ya tsana sama da ita,amma yanzu zaizo mata da wannan zance gsky da sake baza ta tab'a yadda dashi ba, tana cikin tunanin taji maah tayi sallama nan tayi firgigit ta'ansa maaah murmushi tayi tace HUDAH baza ki daina ba ko?.
Murmushi HUDAH tayi sannan tace maaah wlh nad'aina maaah tace Hmmm Allah sa, nan tace " maaah har kindawo? Maaah tace wlh nadawo na isketane zasuji wajen bikin k'awar mijinta keyiwa d'iyarta biki shiyasa nata ho," nan ta wuce d'aki tabar HUDAH tsak'ar gida bayan maaah tashiga d'akin nan HUDAH ta tashi ta k'arasa sauran aikace aikacen gidan bayan tagama, nan tad'ora girkin d'are bayan nagama girki nashifid'a tabarma a tsak'ar gidan, nayi alwala sallah magrip ana k'iran sallah nashiga d'aki nayi.
Nan itama maaah ta fito tayi ba'ita ta fito ba sai bayan sallah isha'i bayan tasyi shafa'i da wituri, nan nazubo mana abinci munaci muna hira maaah nabani labarin abinda dariya inata kyalkyala dariya, " ya faruq ne yayi sallama ya shigo cikin gidan nan suka gaisa da maaah bak'ar Leda ya ijiyemata dama kullum sai ya rikon mata wani Abu idan zai shigo," nan maaah ta tashi tashiga d'aki ta barni dagani sai faruq shiru nayi nakyaleshi yanata surutu ba'abinda nake cemasa daga umh sai a'a dayagaji yayi man sallama yatafi, haka faruq yayi ta damuna Niko baya gabana kullum da kalan abinda nakemasa haka ya hak'ura yad'aure toh bana sakewa dashi k'arshe nad'awo INA sakewa dashi wata shak'uwa mai k'arfi tashiga tsakanina dashi.
Written by
Fiddausi Abdul'azeez (Feedoh)
&
Ayeesha Musa (meesha lurv).
®NWA®
Comments
Post a Comment