JINSINAH 121~125
❄❄ *JINSINAH* ❄❄
*_Feedoh_* *_yanmata_*✍🏻
*_page_* 1⃣2⃣1⃣ *_to_*1⃣2⃣5⃣
Fadilah ce gaban boka ita da habiba, habiba ta gyara zama tace Allah gafarta boka, wannan da kake gani, k'awata ce sosai, toh matsala gareta shine nace bari na kawota wajenka, saboda duk matsalan da mutum yazo da ita kana biyamashi buk'atarshi, boka yace wannan gaskia ne, "Hajia mike tafe dake.... "Fadilah ta kwashe komai tagayama boka, tace boka sonake ka d'auke hankalishi akanta, yamanta da ita arayuwanshi, sai abinda nace yayi ko mahaifiyarshi sonake yadaina kulata duk sudawo k'ark'ashin ikona, "dariya boka yayi yace wannan aykin naki ay mai sauk'ine, d'aga hannunshi sama yayi aka jefomai wani Abu, mik'a mata yayi hannunta na rawa ta karb'a, boka yace ki tabbatar da kin sakamashi k'ark'ashin pillow d'inshi, idan harya kwanta, toh aikinki yaci zaimance da ita da abinda ta haifa komai saike ko mahaifiyarshi bazaiji magananta ba saitaki "wannan kuma k'ofar d'akin mahaifiyarshi zaki saka data tsallaka toh saiyanda kikayi da ita,,,,
"Godia Fadilah tayi sosai, ta ajema boka rapper d'in dubu d'aya, sallama suka mashi sukata tashi sukatafi cikin murna, "saboda gani suke burinsu yakusa cika, "Allah karabamu da mugayen k'awaye, dan tabbas muguwar k'awa ita ta halakar da Fadilah, dan haka yan uwa mukula da irin k'awayen da zamuyi tarayya dasu,,
*********
Gida ta sauke habiba, kana ta d'auki hanyar gidanta, tana shiga gaten taci karo da Umma, "Umma tace fadila lafiya ina kikaje baki ko gayaman ba, "d'aga mata hannu fadilah tayi tace dakata Malama, aybake ke aure na ba dazakice duk inda zani saina gayamaki, sakin baki Umma tayi tace Fadilah nikike gayama haka? Fadilah tace nagaya maki niba finah baceba da kike takawa, wlhi kiman sainamaki, "tsohuwa saisaka ido nida gidan mijina kinzo kin takurani kin hanani sak'at toh wlhi baki isa ba sainayi maganinki, juyawa tayi taita fiyarta, sakin baki Umma tayi tana kallon sarautan Allah, juyawa tayi takoma cikin gida,,,,,,
"Moh ne gaban Anty Aysha yana kuka, yace Anty wlhi ba da san raina nasaketa ba, dole tasani, kuma nasan k'azafi aka Mata, amma ba yanda zanyi, biyayya nayi, Anty rok'onki nakesan kiyi koda finah ragama idda karki bari ta auri wani wlhi finah itace rayuwata, "gyara zama Anty tayi tace Moh nasan kanasan finah amma k'addara ta rabaku, shin idan zamanku tak'are yazakayi, ni ko kai bamu isa musaka ka maidata ba, kaidai kacigaba da adua, idan kuna da sauran zama Allah ya ganar da mahaifiyarka gaskia, moh yace amin, "arif ya amsa dake hannun Anty, Moh yace Anty ina finah Anty tace tana d'aki, yace zan iya ganinta Anty tace why not? Kaje ka ganta,,
"Tashi yayi ya nufa d'akin finah yana sab'e da arif, sallama yayi, amsa mashi tayi, moh yace anban izini inshigo, finah tace kashigo, "shiga yayi yasamu kusa da ita yazauna, kallon juna sukayi, moh yace shine kika taho kika barni? Finah tace dole na taho zamana yak'are gidanka, moh yace waya gaya maki, ay yanzu muka fara zama, "yak'e finah tayi tace nida gidanka harsai randa mahaifiyarka ta daina tsanata, tadaina kirana tubabba, "moh ya kalleta yace finah baki tausaina, bakisan halin dazan shigaba sakamakon rashinki, saikawai yafashe da kuka, itama kukan tayi, kuka sukayi mai isarsu, moh ne ya koma lallashin finah da kyar yasamu tayi shiru,,,
"D'agota moh yayi yace kallanni, kallonshi tayi, yace taimako nakeso kiman, finah tace nami, yace dan Allah duk runtsi karki auri wani, ninasan nikad'aike dake, kuma in shaa Allah zaki koma gidana matsayin mata mai yanci, "hawaye finah takeyi tace moh bazan iya yima alk'awari ba mayb zamanmu yak'are, tsawa yamata harsaida arif ya firgita, moh yace wlhi kika auri wani baniba saina kasheshi, yana fad'in haka ya aje mata arif da kud'i masu yawa yayi gaba, kiranshi takeyi amma bai saurareta ba, fashewa tayi da kuka takama arif ta rungume tana kuka,,,,,
"Anty ce tashigo d'akin taganta tanata kuka, dafa ta Anty tayi tace minene, fad'awa kan Anty tayi tace fushi yayi, daga..... Tagayama anty komai d'agota Anty tayi tace yi hak'uri zai sakko kinji, share hawayenki, d'aukar arif Anty tayi ta fita,,,,,
*_Dedicated_* *_to_* *_biebee_* *_isa_*❤
IG: yar_ficika
© *_written_* *_by_*
*_Feedoh_* *_Deedoh_*✍🏻✍🏻
Comments
Post a Comment