JINSINAH 16~20

❄❄ *JINSINAH* ❄❄

*Feedoh* *yanmata* ✍🏻

*page* 1⃣6⃣ *to* 2⃣0⃣

Iyayenta tagani zaune parlor, rab'asu tayi zata wuce wata tsawa da baban yamata saidata kusa sakin fitsari, "claire daga ina kike? Shiru tayi takasa magana sai jikinta ke kyarma, mummy tace baba dear miye na tsaya tambayarta bayan nagaya maka, naga fitanta, kuma saida nabita baya naga wajen wanda taje, daddy yace sonake naji daga bakinta, koba tambayarki nakeba? Daga ina kike, claire tace dama dama, dama mi?

         "Toh tunda kinzab'i zama da musulmi kikoma can wajenshi, mukam bazamu, zauna dakeba, kije na fitar dake daga cikin *jinsinah* "duk'awa claire tayi tana rok'on uyayenta, amma haka Mummy ta tashi tashiga d'aki tadinga watsoma claire kaya, har waje take watsa mata, "Maman tace Claire lemme warn u koda mafarki kada kiyi tunanin kinsanmu bare kidawo garemu, kije gaki ga hausawa nan, "kuka Claire keyi tana rok'on iyayenta amma sunk'i sauraronta, tsawa daddy yamata Claire get out ov my house, "kuka takeyi sosai janta mummy tayi har bakin kofa ta hankad'ata waje,,,

Had'a kayanta claire keyi tana kuka, tabar k'ofan gidansu tana waiwayen gidan, nikaina yar ficika saida taban tausayi, "hanya ta d'auka tana tafiya batasan ina ta nufa ba, "tunawa tayi da muhammad wayanta d'auko cikin handbag tayi dialing number enshi, ringing biyu, yad'auka yana d'auka claire tafashe da kuka, bansan miyace ba, ajiyan zuciya naga tayi, tace kazo yanzu ina wajen ibro hotel, "banji miyaceba, claire tace saikaxo,,

            "Minti sha biyar saiga muhammad yak'araso wajen, fitowa yayi ya d'auki akwatinta yasaka matashi mota, "bud'e motan tayi tashiga, shima shiga yayi yama motan key, yad'auki hanya, babu wanda kema wani magana, kusan minti goma, wuri yasamu inda bawasu mutane yayi parking, "muhammad yace claire miyafaru, claire takwashe komai tagaya mashi, "shiru muhammad yayi, yace kiyi hak'uri Claire duk nina jamaki, amma I'm shha Allahu bazakiyi kuka dani ba, zanmaki gata bazan butulce makiba, d'aga kai claire tayi, "wayanshi ya d'auko yayi dialing number Ana d'auka Muhammad yace helo Amir kana gida? Amir yace eh, muhammad yace gani nan xuwa nida Claire, Amir yace saikunzo, "ajiye wayan yayi ya kalli Claire yace bari nakaiki gidan Frnd Dina, matarshi nada kirki, kizauna wajensu, kafin musan abinyi, "claire tace to,,,

     "Gidan Amir dake unguwan rogo suka nufa, suna isa parlor suka tarda masu gidan, muhammad na sallama Aysha matar Amir nata tsokanarsu, dayake sun san labarin Claire, "saida suka d'anyi barkwanci, kana muhammad ya kwashe komai yagaya masu, yak'ara dacewa Amir taimako nake nema wajenku kaida Aysha dan Allah inasan Claire tazauna wajenku, nawani d'an lokaci, nazab'e kune sanin halinku kuduka bakuda Matsala, numfasawa Amir yayi yace wlhi abokina bakomai aykaima nan gidanka ne, tazauna damu, Allah yabamu ikon rik'eta Amana, "muhammad yace nagode, madam kefa banji kince komai ba, "dariya Aysha tayi tace wlhi ba komai nidama zaman kad'aici ya isheni, godia muhammad yayi masu,,,

     "Juyowa kan claire yayi yace madam, kinga inda zaki zauna sanin basuda matsala nace kizauna wajensu, toh inasan kema kixauna dasu gaskia da amana, d'aga kai claire tayi, muhammad yace bari naje gida zan shigo anjima, toh claire tace, yatashi amir yarakashj yataf, "Aysha takama hannun claire tace muje na nuna maki d'akinki, binta tayi,,,

    "Gidan mahaifiyarshi dake hubbare yanufa, yana zuwa ya isketa tsakar gida tana shara, "tsintsiyar ya amsa yana ida share Mata, yace Umma karime batazo baneba kike aiki da kanki, Umma tace karime batajin dad'i na Allah, muhammad yace Allah shibata lafiya, Umma tace Amin, saida yagama tattara mata gidan , "dukawa yayi ya gaidata, amsawa tayi tana shimai albarka,,,

Shiru yad'an gifta tsakaninsu, umma tace na Allah bakinka akwai magana, muhammad yace gaskia ne Umma, "tace toh inajinka, shiru yayi, kana yace Umma aure nakeson nak'ara, Umma tace aure na Allah, muhammad yace eh, Umma tace toh na Allah bazan hanaka ba, tunda dama Allah ya halarta maka ka k'ara aure idan zaka iya adalci, toh tinda kace zaka k'ara ayshikenan, Allah yasa alkairi, yace Amin, "Umma tace yasunan sirikar tawa kuma waye iyayenta, Allah yasa yar babban gida ce, saida gaban muhammad yafad'i,,,,,

        "Daurewa yayi yace sunanta claire, Umma tace miye kuma wannan, saikace d'iyar arna, muhammad yace Umma ayba musulma baceba, "bai k'arasaba Umma tahau salati, tace na Allah kodai kaima kafara shaye shayen zamani ne, shidai baice komai ba, Umma tace to ban yardaba duk matan dake garinnan karasa wacce zaka aura sai arniya, gaskia bakaima *jinsinka* adalciba, "Muhammad yace Umma tanafa da hankali ba irin sauran matanan baneba, iyayenta korarta sukayi sabodani, "Umma tace toh kaji iyayenta dake batattu ma sun koreta saboda kai ba *jinsinta* baneba, saikai, toh magana ta tak'arshe shine idan harni na haifeka to ban yarda ba, bakuma da miyau naba, idan kuma kace saikayi toh ga hanya amma kada kakara lissafani cikin mahaifanka.....

*turkashi*
  Ana wata ga wata, "Anya auren claire da muhammad zaiyu kuwa? Kudai biyoni *Yar* *ficika* danjin yanda abin yake....

*Dedicated* *to* *biebee* *isa* ❤

IG: yar_ficika

*written* *by*
     *Feedoh* *Deedoh*✍🏻✍🏻

Comments

Popular posts from this blog

HUDAH 01~25

RASHIN GATA 1-5

RASHIN GATA 176-180