DIJAH 121~125
🏵🏵DIJAH🏵🏵
Feedoh yanmata✍🏻
1⃣2⃣1⃣~1⃣2⃣5⃣
Kwanan dijah ukku a asibiti amma jiya I yau, "saboda tana nan kwance kamar gawa, kuma kullum hamza dasu Ammi sai sunje dubata"yau ne daddynsu hamza zai dawo gari, "hamza ne cikin d'aki yana shiri saboda yanasan yaje hospital kafin, "daddy ya iso, "wayan hamza tafara ruri alamar ana Kira, baibi takan wayan ba harta tsinke dayake yana sauri yagama shiri, "yanasa botir d'in hannun riganshi ne, wayan tafara k'ara, "tsaki yayi yaje inda wayantake, "sunan daya gani kan screen ne, yasashi murmushi, "d'auka yayi yace hello naf, "d'ayan b'angaren naf ya amsa, "hamza yace naf har yanzu bakaji wani labari ba? "Nafeeu yace hamzaree bawani labari har wajen na k'ara zuwa amma duk wanda na tambaya sai suce basu santa ba, "hamza yace naf al'amarin nan yana d'aure man kai, "Nafeeu yace hamza sai hak'uri mucigaba da adua har Allah ya tashi kafad'unta, "hamza yace toh Amin, sukayi sallama...
Yana gama shiri asibiti ya wuce, "yana zuwa asibiti d'akin da dijah take kwance ya nufa, "saboda yanzu asibiti tazama wajen zamanshi, "tun sanda yakawo dijah asibiti ya tare nan bacci kawai ke maidashi gida, "nurse d'in dake kula da dijah ce ta shigo, "tana ganin hamza ta washe baki, saboda kyautar dayake mata, "gaisheshi tayi ya amsa fuska sake da tambayarta mai jiki? "Tace mai jiki da sauk'i hamza yace toh Allah yak'ara lapia, "nurse tace Amin, "hamza yace doctor na nan? Dan inasan ganinshi, "nurse tace eh yana office saboda yanzu ma yabar nan, "tashi yayi yanufa office d'in doctor, "sallama yayi, "amsa sallama doctor yayi tare da mai izinin shiga, 'gaisawa sukayi tare da d'an barkwanci dayake sun san juna, "hamza yace doctor ya jikin patient d'ina? Doctor yace toh da sauk'i, "hamza yace doctor akwai ko cigaba, shiru doctor yayi, "yace toh munasamun cigaba kam, "kuma in shaa Allah nan bada jumawa ba zatasamu sauk'i, "hamza yace toh Allah yabata lapia doctor yace Amin, "hamza yace bari na koma na gode kwarai, doctor yace bakomai hamza, "Allah dai yabata lapia, "amma dagani kanaji da patient d'innan taka, "murmushi hamza yace nidai kaga tafiya, dariya doctor yayi, "yace sai munyi waya......
*****************************
D'akin dijah yakoma dama kullum nan ne wajen firanshi, shigayayi d'akin da sallama, "yana zuwa yaja kujera ya zauna gabanta ya k'ura mata Ido, "tunani kala kala yayishi kan ta, "sallama aka dangayi amma ina hamza ya lula kogin tunani, "dafashi akayi firgigit yayi yadawo hayyacinshi, "yana d'aga ido wazai gani, daddy ne, "da murnanshi ya mik'e ya rungume daddy, yace daddyn affy oyoyo, "daddy yace ayni nayi fushi dakai, hamza yace am sowee daddy afrah, "nasan ban kyauta ba, wlhi ban d'auka time yaja haka ba, "murmushi daddy yayi yace ina zakasani tinda ba Ammy d'inka baceba tayi tafiya, "inda itace aykai zaka d'aukota airport , "sai sannan Ammi tayi magana tace toh yanzu ba afrah taje d'auko kaba, "ninatab'a tafiya afrah taje sun d'aukoni, "hamza yace a toh kaji dai daddyn affy, "dariya su duka sukayi, "daddy amma aygashi baki bari na hutaba kikace mutaho asibiti, "Ammi tace toh bagara kazo kaga patient d'inmu ba , "yace aigani nazo, "daddy yace hamzarien Ammi ya marar lapian taka da jiki? Baki yatab'e yace toh gatanan, "daddy yace wani irin gatanan dasauk'i zakace "hamza yace inafa sauk'i daddyn afrah mutum kwance kamar gawa ba abinda me aiki jikinshi, "daddy yace Authubillahi hamza musulmi fa kake kuma kace basauk'i, "koyane ay ana samun rahaman ubangiji, "Ammi tace gaskia ne, "daddy yak'arasa gaban gadon dijah k'uramata ido yayi yana kallonta, kamar yanasan yatuno wani Abu, "amma kuma ya kasa, kuma yakasa daina kallonta, "har Ammi ta Lura zuwa tayi ta dafashi tace daddy lapia kuwa, "murmushi yayi yace bakomai Ammi, "kad'a kai tayi, "adu'o'in Neman sauk'i daddy yama dijah, yajuyo da murmushi yace Hamzariee Allah yabata lapia, "hamza yace Amin daddy, "sun d'an dad'e kana sukawuce gida, "koda zasu wuce saida daddy yakoma wajen gadon dijah, "yana tunani amma yakasa tuno komai, "ahaka dai sukabar asibitin.....
www.phirdauceejeebo.mywapblog.com
Written by
Feedoh Deedoh✍🏻✍🏻
Comments
Post a Comment