DIJAH 81~85

🏵🏵DIJAH🏵🏵

Feedoh yanmata✍🏻

8⃣1⃣~8⃣5⃣

Dijah tace inna sannu da gida, Inna larai tace sannu da gidan uwarki, shegia sai yanzu zaki dawo, gidan ubanwa kika tsaya," dijah tace wlhi Inna babu inda na tsaya, "k'arya zanmaki kenan? Zonan, dijah ta girgixa kai tace bance k'arya kikeba, Inna kiyi hak'uri, tsawa ta mata tace zakizo nan kosaina tashi, hak'uri dijah keba inna amma kamar tana k'ara zugata, mik'ewa Inna larai tayi ta fizgo dijah, mari ta wanka mata saida dijah star star bugunta ta cigaba dayi, dijah kuwa saineman d'auki takeyi, saidata ga dijah bata iya numfashin kirki kana ta kyaleta, wani mak'otansu ne ya shigo dayaji ihun dijah yayi yawa, yana shigowa yaga dijah kwance bata iya numfashin kirki, salati yakamayi, ya juyo kan Inna yace larai kini tsoron Allah wlhi hakkin d'iyar nan saiya kamaki dana malam, saboda amanace wajenku, "amma yanzu kiga irin rik'on da kike mata, yanzu kalli yanda kika mata gashinan ko numfashin kirki bata iyawa, kisani wlhi yarinyar nan ta mutu kema sai ankasheki , "tsaki Inna larai taja tace aydama nasan kaima kana nemanta toh wlhi duk sainayi maganinku, girgixa kai yayi yafita, mota yasamo yasa matarshi ta kama dijah sai asibiti...

**************************
Likita ne tsaye kan dijah da k'yar yasamu numfashinta ya daidaita kana ya d'aura mata ruwa, "juyowa likita yayi yana kallon wanda yakawo dijah asibiti, fad'a ya dingayi mai sosai, akan sunbarta ciwo yamata yawa, likita yace haba malam yayanku fa amanace da Allah yabaku yanzu gashinan sakamakon sakaci irin naku ciwon zuciya yakamata gakuma ciwon yunwa (ulcer) dan Allah kudinga kula akan yaranku, "hukri yakeba likita girgiza kai likita yayi kana ya mik'a mashi takardan magani ya juya yafi,magunguna yaje ya siya, kana yakoma gidan Inna larai, sallama yayi batako kalleshi ba bare ya amsa, girgiza kai yayi, yace mata dama dijah ce tana asibiti, shine nazo nagayamaki saboda hakkinki ne, tsaki Inna tayi tabarshi nan tsaye, fita yayi yana Allawadaran da hali irin na larai, yana fita yacikaro da hanne saboda angaya mata, tararshi tayi tana tambaya wane asibiti ne, yace hanne k'araman asibiti ne, hanne na kuka tace idan can zaka muje naganta....

www.phirdauceejeebo.mywapblog.com

Written by
          Feedoh Deedoh✍🏻✍🏻

Comments

Popular posts from this blog

HUDAH 01~25

RASHIN GATA 1-5

RASHIN GATA 176-180