ZAMAN GIDA 11~15

🤔🤔 *ZAMAN* *GIDA* 🤔🤔

*_Feedoh_* *_yanmata_* ✍🏻

*_page_* 1⃣1⃣ *_to_* 1⃣5⃣

Kallon juna sukayi, cike da mamaki, malam yace amma karku damu, ga wanan kuyi wanka dashi kwana ukku, hadiza ce ta amsa, godia sukayi suka fito, "suna fitowa suka samu mai amalanke yana, jiransu, suna zuwa suka hau amalanke, sunfara tafiya kenan, sadiya tace amma wannan malamin anyi d'an iska wlhi, ji shege wai mijinmu baizo duniya ba, hadiza tace ayni narasa bakin magana, ji wannan shegen maganin da yabamu, wlhi yarda shi zanyi, tillar da maganin sukayi, shidai mai amalanke yana jinsu, dariya ta kufcemai, ran sadiya yak'ara b'aci tace malam lafiya kake muna dariya? Saikace kaga mahaukata, mai amalanke yace ba daku nakeba, tsaki sukayi daga nan basu sake cewa komai ba,,,,,

         "Suna isowa tasha sukaci sa'a saura mutum biyu, Shiga sukayi suka biya kud'in mota, mota ta d'aga sai katsina, "cikin minti k'alilan suka iso katsina, sadiyace tace muwuce gidansu feedoh, hadiza tace bari na kirata, karmuje tana skul, waya hadiza ta d'auko takira feedoh ringing ukku ta d'auka, hadiza tace in kina gida muna nan, zuwa feedoh tace ina nan saikunzo,,,,,

        "Suna sauka Tasha suka hau mini jeep (Napep) sai gidansu feedoh, "suna zuwa suka iske kakar feedoh batanan, hamdalah hady tayi ta kalli marafa tace azababbar tsohuwar nan batanan, dariya sukayi baki d'aya, daga d'aki feedoh tace sannuku da gulman Kakus d'ina dariya sukayi suka sakai cikin d'aki,,,

"Suna shiga feedoh tace yana ganku haka kamar korarru, hady tace bamu abinci dai yanzu muci akwai hot story, tashi tayi takawo masu abinci, saida sukaci sukayi k'at, sukayi sallah kana Marafa tace karkad'e kunnenki kisha labari,,,,,,

Suka zayyanema feedoh komai, wata irin dariya tayi harsaida sukaji haushi saidatayi mai isarta, ta kallesu tace yanzu mijinku ashe baizo duniya ba, d'aka mata duka hady tayi tace inji la'anne ba, "gyara zama feedoh tayi tace kunsan me? Sukace ah ah, tace wani malami aka had'ani dashi chan cikin k'auyen charanchi yake ance maganinshi na aiki, yakuka gani zaku? Danni dai zanje, Marafa tace wlhi nidai nagaji, Hady tace waya gaya maki ana gajiya, *ZAMAN* *GIDA* ya ishemu, feedoh tace tell her dai, yanzu kawai Ku shirya gobe muje, da zafi zafi akan bugi k'arfe, sukace Allah yakaimu goben,,,,

*Taufa* *yanzu* *kuma* *charanchi* *aka* *nufa* *toh* *can* *komi* *za'a* *gaya* *masu*, *kudai* *biyo* *Yar_ficika* 😂😂

*Dedicated* *to* *sadiya* *Marafa* *nd* *hadiza* *Ahmad*

*Feedoh* *Deedoh*✍🏻✍🏻

Comments

Popular posts from this blog

HUDAH 01~25

RASHIN GATA 1-5

RASHIN GATA 176-180