DIJAH 116~120
🏵🏵DIJAH🏵🏵
Feedoh yanmata✍🏻
1⃣1⃣6⃣~1⃣2⃣0⃣
Hakadai sukaga jimami, itako afrah sarkin kuka da k'yar hamza yasamu tayi shiru, "Ammi ce takira daddy tamashi bayanin da hamza yamata, daddy yace ayshikenan tunda yataho da ita, Allah kuma yabata lapia, "Ammi tace Amin, "Ammi tace daddynsu hamza wai yaushe zakadawo ne? Daddy yace kina mssn d'inane, murmushi Ammi tayi tace sosaima, "dariya yayi yace karki damu nan da kwana ukku in shaa Allah ina cikin iyalina, "da fara'anta tace Allah yakaimu lapia, can't wait 2 c you, "daddy yace same my wife, hakadai suka dinga fira cikin so da k'aunar juna,daga k'arshe sukayi sallama "nidai feedoh sakin baki nayi ina kallon su, nace dama tsofaffi na soyayya haka, toh nima Allah yakaini wannan fagen nida....... Basai na ida ba saboda su sadiya Marafa da babby labo yan gulma🤔
**************************
K'arfe hud'u su Ammi suka isa DIFF hospital, "straight d'akin dijah suka nufa koda sukaje suntarda nurse na gyarata, amma haryanzu tana nan kwance kamar gawa, "gaisawa su Ammi sukayi da nurse tare da tambayarta yamai jiki? " nurse tace da sauk'i kana tafita, " Ammi ce ta isa gaban gadon dijah, ganin halin da dijah take ciki saida ya firgitata, "tayi wani irin fari, " Ammi tace sannu baiwar Allah, "Allah yabaki lapia yakuma tashi kafad'unki hamza yace Amin Ammi Nah, " Afrah kuwa ganin yanda taga dijah kwance kamar matatta sai k'arafunan da aka d'aura mata, yasata kuka, " da kyar suka samu tayi shiru, " Ammi ta kalli hamza tace Hamzariee yarinyar nan naji ta shiga raina zanso inji daga ina take, "Afrah tace Allah nima Ammin ya hamza , "Allah dai yabata lapia Ammi da hamza sukace Amin, " nan suka dinga fira har 6pm tayi sukabar asibiti suka wuce gida.......
WAYE HAMZA?
Alh Abubakar shine mahaifin hamza, yanada mata d'aya mai suna Hajia nafisa, Alh Sbubakar d'an siyasane, "yaransu biyu duniya hamza ne babba sai Afrah, "sunasan yaransu sosa, " saidai duk sanda suke masu bai hana sun basu tarbiya ba, dan dukansu saida suka sauke Alkur'ani, " yanzu haka Afrah na ss2 a Nigerian Turkish abuja, " shikuma hamza ya k'are masterx d'inshi a Cairo yanada 24yrz yanzu haka 25yrx gareshi, "sunyi mugun shak'uwa shida Afrah saboda sunasan juna, "kuma duk da haka baisa ta rainashiba,sai dai anraba saboda daddy yace afrah ce babynshi ita kuma Ammi tace Hamzariee ne nata, shiyasa afrah ke cewa Ammin ya hamza shikuma hamza yace daddyn afrah " Hamza dogo ne gashi chocolate, "hamza yanada d'an jiki amma basosai ba, ga dimples dake d'aukar hankalin mata,"saidai shi asalima tsoron mata yake, "Abotarsu shida nafeeu tasamo asaline tun a skul, "saboda halayansu tazo d'aya basa kula mata, "shiyasa tasu tazo d'aya, "saidai shi nafeeu tun randa yaga Afrah yaji duniya tamashi kuma aurenta yakesanyi, " bai b'oyema hamza ba yagayamashi, "hamza kuma ya amince Amma da sharad'in baxai mata maganan soyayya ba harsai tagama skul, "Nafeeu ya Amince, "koda hamza yajema Afrah da maganan bata musaba dan itama Nafeeu yamata, " wannan kenan...
Hanyarsu ta komawa gida bamai magana saboda gaskia halin da suka iske dijah tabasu tausai,"hardai hamza dan yak'are mata kallo tayi mugun ramewa amma duk da haka tanada kyau, " ga gashinta daya yamutse saboda wahala, "ahaka har suka iso gida ana magrib, " masallaci hamza yawuce yayi sallah baibar masallaci baba saida yayi isha,"adu'o'i yayima dijah tare dafatan tasamun lapia, " koda yadawo gida draining area yatarda su Ammi, "suna jiranshi suci abinci, "yana zuwa yagaida Ammi ta amsa mashi, "Afrah ta gaidashi ya amsa, "serving d'insu afrah tayi, suna cin abinci, "sab'anin afrah dataketa juya spoon "Ammi ce ta lura tace baba afran daddy kici abinci mana, "yamutse fuska tayi tace Ammin ya hamza Allah nakasa mantawa halin da naga baiwar Allah nan, "murmushi hamza yayi, yace babyn daddy ay adu'a zamu dinga mata, saboda k'addaranta ne haka kinji ko? "D'aga kai tayi dak'yar suka samu afrah taci abinci....
www.phirdauceejeebo.mywapblog.com
Written by
Feedoh Deedoh✍🏻✍🏻
Comments
Post a Comment