ZAMAN GIDA 36~40
🤔🤔 *ZAMAN* *GIDA* 🤔🤔
*_Feedoh_* *_yanmata_*✍🏻
*_page_* 3⃣6⃣ *_to_*4⃣0⃣
Numfasawa feedoh tayi tace toh yanzu yazamuyi ni wlhi tsoron masifan Kakus nakeyi, bare taji ance zariya kuma, "shiru sukayi saican Rookiey Kaxs tace Ina da idea duk sukace munajinki, tace why not muce queen ce tayi accident zamuje ganota, Marafa tace ah ah baza'ayi hakaba, kawai muce bikin queen akeyi zamuje kunga dama gobe Saturday muce yinin biki kawai zamuje mata, zamuyi sammako kuma goben zamu dawo, "hady tace idan queen d'in kuma tazo suka ganta fa, Marafa tace kawai saimuce sun rabu, gaba d'aya sukace good idea had'a hannu sukayi suka tafa,,,,,,
********
"Haka kuwa akayi sun tsara iyayensu, kuma Allah ya taimakesu anbarsu, dan feedoh Kakus bata bata Marsala ba, saboda tasan queen, "k'arfe sha d'aya suna cikin zariya, mini jeep suka hau sukayi gidansu queen, sun a shiga queen ta taso da gudu ta taresu tana murna, Maman queen ma tamasu tarar kirki cz duk tasansu, saida sukaci sukayi k'at kana queen tace toh muwuce ko, queen taje tacema mamanta zasuje gidan k'awayensu, Maman queen tace toh ta d'auko 1k tabasu tace gana mini jeep godia sukayi suka kama hanyan neman sa'a,,,,,,
"Suna fita basu tsaya ko inaba sai gidan malam ilu dake tudun jukum, sallama sukayi suka shiga, suna shiga sukaga wata yar yarinya, queen tace malam na nan? Yarinyar tace eh, queen tace jekice yayi bak'i, jimkad'an yarinyar ta fito tace sushiga,,,,
"Sallama sukayi suka shiga d'akin malam, izinin wurin zama yamasu, saida suka gaidashi, kana yace yanmata mike tafe daku, hady tace malam munji labarinka ne shine mukace bari muzo, saboda gaskia dukanmu nan aure mukeso mungaji da *ZAMAN* *GIDA* duk k'annenmu sunyi aure amma mu muna gida, babu inda bamuje ba amma shiru, nanfa Hady ta kwashe komai tagaya mashi, tundaga randa suka fara zuwa wajen malamai haryanzu da sukazo wurinshi,,,,,,
"Tunda hady ke bayani malam ke kallonta saidata kai k'arshe kana ya numfasa, yace yanmata ya sunanku kuma daga Ina kuke, sunayesu suka fad'a kuma sukace daga kt suke, "kallonsu malam yak'arayi yace tsakaninku da Allah tunda kuke binyawon malaman nan iyayenku sunsani, nanfa idanuwa suka raina fata sukace ah ah, malam yace kuji tsoron Allah yanzu miye abin zuwa ga mushiriki? Kunsan illar shirka kuwa? Saboda bokaye shirka suke kuma mak'aryata ne saboda duk inda kukaje da abinda za'a gayamaku, shin yanzu baku tsoron Allah ya kamaku, tabbas kun isa aure amma baku tunanin sai lokacinku yayi zakuyi, shin idan kuka mutu cikin wannan halin kucema Allah mi, kunci amanar addininku kuma kunci amanar iyayenku, da kuke bin bokaye yan tsubbu, nanfa malam ya dingayi masu nasiha, gaba d'aya saida jikinsu yayi sanyi, malam yace nikam ban bada maganin miji amma zanbaku adu'o i wanda zaku dingayi kuma kudinga tashi cikin dare kuna kaima Allah kukanku, kuma Ku tuba da zuwa wajen mushirikai, malam ya d'auko adu'o i yabasu yace kuna iya tafiya, tashi sukayi jiki sake suka fito suna fitowa suka kalli juna,,,,,,,
*Dedicated* *to* *Sadiya* *Marafa* *nd* *Hadiza* *Ahmad*
*Feedoh* *Deedoh*✍🏻✍🏻
Comments
Post a Comment