HUDAH 91~95
⭐⭐HUDAH⭐⭐
Na
Feedoh & Meesha Lurv
9⃣1⃣~9⃣5⃣
Alh yakoma gida ranshi, bace yace safiya nagode da abinda kikaiman, saboda nasan wanan hadin duk kekika yishi, amma bakomai bazance maki komai ba, kuma bazan yiwa dana bakiba, amma kuje duniya zata bidaku, kuka fady keyi, tace daddy dan Allah kayi hakuri, yace bakomai farida, nariga dana sallama faruq yaje yanemi uba, yanxu kekadaice diyata Allah yamaki albarka tace amin daddy,
Haka rayuwana tacigaba cikin koshin lapia da kwanciyan hankali, saboda da daddy na kula dani sosai, haka kuma besty kullum tana kan hanyar gidanmu dan tadebeman kewa, saidai yawan ciwon zuciya daya matsaman duk idan yataso baiman da wasa, dan akwai sanda aka fidda rai dani,saigashi Allah yatashi kafaduna.
Haka samari suka dinga biyoni amma da anfara magana sai na nemesu na rasa sunkama gabansu, akwai wani salisu da muka dinga soyayya dashi har muka fara maganan aure, yaceman nafada gida iyayenshi zasuzo, nasami maaah nagaya Mata, tace badamuwa, idan sun sa rana sai nagayama dangin Abbu, nace toh, ranan nan ina zaune gida, saiga wani yaro yashigo da takarda yayi sallama yace hudah gashi inji wani, na amsa nace yana ina? Yace yatafi nace toh, saida nagama aikin dazanma maaah kana nadauki takardan nan na bude abinda nagani ciki yasani sakin wata kara tare da salati, maaah ce da gudu take tambayana lapaa? "Niko inbanda aikin kuka ba abinda nakeyi da kyar maaah ta lallasheni, tare da nasiha kana nayi shiru, tace hudah miye cikin takardanan haka datasaki razana?
Wani gauron numfashi na ja, nace maaah haka nikuma zan rayu kenan cikin kunci faruq ya cuceni yagama dani, yabataman suna, maaah tace miyafaru wai? "Nace maaah Salisu ne ya aikoman da wasika, wai gaskia nayi hakuri shikam bazai iya auran kingin waniba, saboda yayi bincike yagane inabin maza, shi kuma kamila yakeso,dan haka ya janye idan wani zai iya kwasa ya kwasa shikam bandashi, maaah kiga sharri minama mutane haka? Maaah ta shareman hawaye tace kiyi hakuri kinji iyakar abinda zance maki kenan,nace maaah insha Allah nagama soyayya na hakura da aure,inko zanyi aure toh ni dakaina zangayama mutum waceceni, maaah tace nayarda dake huda.
Numfasawa huda tayi tare da dago kai, tace ya naufal kaji labarin waceceni dakuma yanda rayuwata takasance, shiyasa lokacin dakake bina naki kulaka, hankicif ya dauko yamikama huda, ta amsa ta goge hawayen datakeyi gawani kamshi daya bigi hancinta saidata lumshe ido, "murmushi naufal yamata yace naji labarinki hudah,kuma in shaa Allah zan zamar maki gata a rayuwanki saina nuna maki so fiye da wanda fu'ad yama meera ( wata rayuwa) na lubabatu sani maitafsir haka zan maki gata, kuma dama nagayamaki ke rabo nace,"na hauwa Jabo, agogon hannunshi ya duba yace kai princess time yafaja, muje na rakaki gobe zan dawo, kar maaah tamaki fada, kanta ta gyada tatashi yarakata har kofar gida, yace princess kamar karmu rabu, plz say u Lurv mie, kona iya bacci, a kunyace tace I Lurv u, tana fada tayi cikin gida da gudu tana dariya,girgiza kai yakeyi yana murmushi....
Note:salam my beautiful people zakuji dijah shiru kwana biyu sainagama hudah kana zancigaba tnx ya 'all, feedoh luves u so much #muahhhhh
www.phirdauceejeebo.mywapblog.com
Written by
Firdausi Abd'Azeez (Feedoh) &
Ayeesha Musa (Meesha Lurv).
Comments
Post a Comment