JINSINAH 36~40
❄❄ *JINSINAH* ❄❄
*_Feedoh_* *_yanmata_*✍🏻
*_page_* 3⃣6⃣ *_to_* 4⃣0⃣
*_BAYAN_* *_WATA_* *_UKKU_*
Abubuwa sunfaru cikin wata ukku, ciki harda saka ranan auren muhammad da nafisa, wanda yanzu saura sati ukku bikin,
Zaune take parlor ta kunna kirar sudais tana binta, cikin zazzakar muryanta, yakai minti goma tsaye yana kallonta, amma batasan yashigo ba, "takowa yayi a hankali, yazo tabaya ya runtse mata Ido, cikin yar siririyan muryata tace innalillahi wa Inna ilaihir raji'un, sakinta yayi d'aga idonta tayi taganshi yanata mata dariya, zumb'ure baki tayi tace haba dear kasanfa ba kyau tsorata musulmi, kama kunnenshi yayi yace afuwan *_FINAH_* murmushi tayi tace is *_OK_*,,,,,
**************************
Zagayowa yayi yazauna tareda d'aukan remote ya rage volume, gaidashi tayi ya amsa yana tsokananta, amarya ba kya laifi kokin kashe d'anmasu gida, dariya tayi tace kardaina kashen dan zanyi katon laifi, dariya sukayi su duka, muhammad yace ina mash gidan, nafisah tace sunje unguwa, amma nasan yanzu gab suke da dawowa, muhammad yace Allah yamaidosu lapia,,,
Muhammed yace nafisa biki nata matsowa amma banji kince zaki komaiba, nafisah tace ayba abinda zanyi walima kawai zanyi dan bansan party gaskia ko d'aya albarkan aure nake Nima, muhammad yace gaskia ne, kinyi tunani amma bari Anty dinki tadawo, naji nawa zanbada na gyaran amarya dakuma na waliman,,,,,
"Fira sukeyi sosai, su Aysha sunshigo sunata sallama amma firan soyayya tayi dad'i basuji, saida suka shigo parlon kana nafisah tace Anty banji sallamarku ba, amir yace yaushe zakiji parrot yasakaki gaba, dariya sukayi, muhammad yace kafa rainani, Amir yace surukinka fa nake yanzu Allah zanfasa muhammad yace afuwan papa bazan karaba, dariya sukayi suduka, nafisah ce tamasu sannu da gida, takawo masu lemo, bayan sungama sha sun d'anyi fira su amir suka fita, hannun nafisah Aysha taja tace muje kiga kayak kitchen d'inki, idan akwai abinda baiyi ba saimuje ki canja, "wani store suka nufa cike yake da kayan kitchen dubawa nafisah tayi tace anty komi sunyi Aysha tace kintabbata, d'aga kai tayi, tana hawayee tace Anty nagode banda bakin daxanmaku godia saidai fatan keda mijinki Allah yabaku aljannah Firdausi Allah kuma yasaukeki lapia, Aysha tace amin, karki damu mamanah kincancanci muyi maki fiye da haka, dan yanzu jinki nake kamar kanwata,,,,,,,,
"Bari mu leka wajen Fadilah muga yatake ciki,,
"Kwance take saman gado tayi rigingine, ta d'aga kanta sama gawata uban rama datayi, sallama akeyi amma takasa amsawa shigowa matar dake sallama tayi tab'ata tayi kana tadawo firgigit tace haba Fadilah miye na dogon tunanin nan jibi yanda kika rame, ajiyan zuciya Fadilah tayi tace bari kedai habeebah abunne na dagaman hankali, duk inda mukaje sai aceman aurennan ba fashi kuma kece shaida tunda tare muke zuwa dake, "habiba tace dagangan kike tada hankalinki kincefa uwar mijin baso takeyiba saboda ma auren zata dawo gidannan toh kibari ta shigo gidan idan malamai sunkasa zamuyi amfani da kissarmu ta mata kuma muhadata da uwar mijin dole tabar gidan, washe baki Fadilah tayi suka tafa tace gud idea shiyasa nakesanki wlhi, "nidai *_Feedoh_* *_yanmata_* d'akin nabaro inamai aduan ka Allah yabasu sa'a kan wannan mugun k'udiri nasu,,,,,
"Rana bata k'arya saidai uwar d'iya taji kunya ayau aka d'aura auren muhammad da nafisa akan sadaki dubu Hamsin, inda dubban mutane suka shaida d'aurin auren gaskia aure yatara mutane da dama, inda Amir yazama waliyin amarya, "bayan angama d'aurin aure kana aka fara reception,,,
"Marece nayi naje gidan amir dannaga mike faruwa tardawa nayi ankakkafa tempol ga kujeru ga mutane zaune gefe guda ga Malama Maryam Ladan Shuni tana bada lacca uwar amarya na hango tayi kyau cikin d'anyen lace gaskia Anty aysha tayi kyau, ware idanuwa nakeyi inga inda zanga amarya, can na hangota cikin shigar alfarma ga alkyabba Tasha gaskia tayi kyau ban iya kawo maku irin kyan datayi mai karatu nabarka ka kyasta da kanka irin kyan da amarya tayi,,,, marece lik'is aka tashi data wa'azi inda aka sallami kowa da soveniers,,,,,
"Anagama isha yan d'aukan amarya sukazo Aysha ne takama hannun nafisah takaita gun amir, Amir yace Aysha kiyi biyayya ga mijinki da iyayenshi hakurin danasanki dashi ki cigaba kiyi hakuri da irin abinda zakigani kidage kuma da adua Allah natare dake kije Allah yabaku zaman lapia yatashi yabar wurin kuka takeyi sosai, itaa kanta Anty aysha saidatayi kuka,,,,,
"Gidan ango dake arkillah aka nufa da amarya gaskia gidan amarya yayi kuma su Anty Aysha sunmata kara "bedroom ukku suka Mata sai parlor biyu ko kitchen dinta abin kalllo ne gaskia gidan amarya yayi kyau sosai,,,,
"Yan kawo amarya sun watse anbar Anty Aysha ita kadai saboda sai amir yazo d'aukanta zaune sukeyi tana Kara kwatanta Mata yanda zaman aure yake,, "kofa sukaga abbanko, basuba nikaina saida gabana yafadi, uwar mijin sukagani tsaye, dayake Anty Aysha tasanta gaidata sukayi amsawa tayi a dak'ile,,,,,,
" nuna nafisah tayi tace ke tubabba ki saurareni sosai kiji abinda zangaya maki, kinnace dole saidakika auri d'ana dankinga Allah yarufama shi asiri, toh barikiji ba zaman aure kikazoyiba zaman bauta, saboda na sallami masu aikin gidannan gaba d'aya komai kezakiyi tundaga kan shara wanke wanke wanki, girki kezakiyi kuma girki da icce zakiyi, dama amfanin tubabbe kenan kuma gyaran d'akina sau ukku arana, kuma aikinki zaifara daga gobe tana kaiwa nan tajuya tafita,,,,,,
" *_Turk'ash_*🤔🤔🤔🤔
*_Dedicated_* *_to_* *_biebee_* *_isa_*❤
IG: yar_ficika
© *_written_* *_by_*
*_Feedoh_* *_Deedoh_*✍🏻✍🏻
Comments
Post a Comment