DIJAH 221~225
🏵🏵DIJAH🏵🏵
Feedoh yanmata✍🏻
2⃣2⃣1⃣~2⃣2⃣5⃣
Bud'e d'akin sukayi suka fito, badan sun k'are firan ba, tsakar gida sukaga Ammi da mama, Ammi tace toh saikizo mutafi, kayan abinci aka dinga shigowa dasu gidansu hanne, dijah taba hanne kayan data kwaso mata, takuma d'auko waya HTC one tace mata gashi namaki chargy nasa maki number ta, "kuka murna hanne ta dingayi, dijah ta lallasheta, Inna larai ce tashigo bankwana, sunyi bankwana suka d'un guma sukayi waje, "hanne tace dijah idan aurenki yatashi karki manta kigayamana fa, dafata dijah tayi tace karki damu yar uwata, in shaa Allah zangayamaku, "jikka ta bud'e ta bata kud'i masu yawa, shima Hamzariee yabata karb'a tayi tana godia ga hawaye, "haka su dijah suka shiga mota suka tafi hanne ta dinga d'aga masu hannu harsaida tadaina kallonsu, Allah sarki dijah saidatayi kuka, jitakeyi kamar tatafi da hanne, "minti talatin yakaisu cikin garin katsina, "gida babansu naf yabasu inda zasu kwana, tundaga bakin gate Inna larai ke zabga k'auyanci, affy ko sai dariya takeyi, suna shiga suka iske komai na abinci, sallah sukayi sukafara cin abinci, itadai Inna sai santi takeyi affy nata dariya kamar Maryam shuni🤔, haka sukagama cin abinci kowa yanufi makwancinshi amma banda su dijah saboda fira sukeyi, dijah da Hamzariee naf da affy, sunata fira har lokaci yaja basu saniba, saida Ammi tasauko takoresu, tace oh ni yaran zamani, toh kutashi kuwuce kuban wuri, su dijah aka mik'e sumi sumi aka tafi afyy kuwa saida akamata kwanya, Hamzariee tafiya yayi yana gunguni....
*****************************
K'arfe bakwai nasafe duk sungama shirinsu, saiga yan baban Nafeeu sungaisa cikin mutunci, sukamashi godia, "shima yamasu godia da alk'awari nan da kwana ukku zasuzo maganan aure, daddy yace bakomai saisunxo, haka suka fito zasu tafi Nafeeu da affy an tsaya bankwana, Hamzariee saida yamasu shaida Ammi ta fatattakesu, Hamzariee da dijah nata dariya, "Hamzariee yace kaga ni matata zan tusa gaba mutafi ina tuk'i muna firan soyayya, naf yace zanrama, suka tafa suna dariya, "bankwana sukayi suka wuce affy nata mssn habeebee d'inta, "tafiya sukayi mai nisa itadai Inna larai duk taji ta takura, Inna tace wai yayannan ina zaku kaini? Affy tace Inna saidaki fa zamuyi, "Inna ta d'ora hannu bisa Kai tafashe da kuka tace dan Allah kuyi hak'uri wlhi nayi nadama, dariya hamza da affy keyi, Hamzariee harda kwalla, dijah saida tayi dariyamai isarta kana tace affy bansan haka innartawa zakima haka, kyaleta Inna k'arya takeyi, "Inna tace nidai kuyi hak'uri kuma saukeni nan, "dakyar aka samu Inna tayarda ba saidata za'ayiba,
K'arfe d'aya da rabi suka iso suna isowa maitama suka wuce, nanma Inna Tasha kallo, saida dijah ta rik'o hannuta, saida sukaci abinci kana sukayi shirin tafiya gida, "sama dijah tahawo takwaso unifoam d'inta nanfa daru yatashi, waishi dijah bazataje KO ina ba tana nan, "mama tace toh tazauna ayduk d'ayane, saida yaga ran Ammi yab'aci kana ya kyalesu, affy kuwa sai dariyan k'eta takeyi, gidanma Hamzariee yabari, baba yayi dariya yace Hamzariee rigima, daddy yace ay d'iyata nada aiki, "sallama sukayi suka wuce asokoro, ita kanta dijah duk taji bataji dad'i ba dataga Hamzariee yayi fushi, "suna isa gidansu dijah, Inna larai harda kukanta, saboda kunya saida mama ta lallasheta, baba yace Inna ina zaki zauna k'asa ko sama, Inna tace ina wlhi ina k'asa bamai kaini k'ololuwa dariya sukayi ga ba d'aya, "dijah tace toh nidai Inna nayi d'aki saina sakko Inna tace toh yar albarka, "dijah na hawa sama Hamzariee ta kira saida takusa tsinkewa kana ya d'auka, yana d'auka tace bazan gaji da baka hak'uri ba charming, munfa kusa zama inuwa guda, kadaina fushi, kaima kasan kanka ina kewarka, da dad'in baki tasamu ya huce, sukacigaba da firan soyayya, "Hamzariee yace wane tym ne exams d'inki gobe tace 9am yace toh kijira zanzo nakaiki, tace ya hamza karka damu zanyi drivn, hamza yace nadaice zanzo, dijah tace yes boss, ur wish is my command,....
www.phirdauceejeebo.com
IG: yar_ficika
Written by
Feedoh Deedoh✍🏻✍🏻
Comments
Post a Comment