DIJAH 156~160
🏵🏵DIJAH🏵🏵
Feedoh yanmata✍🏻
1⃣5⃣6⃣~1⃣6⃣0⃣
Akwana atashi ba wuya wajen Allah, yau ne randa hamza zaidawo daga tafiya. "Aiki sukeyi sosai na tarban d'an lelen Ammi, "daddy ne ya shigo kitchen ya samesu, yace lallai wanan shagalin duk nad'anki ne ko? Dariya Ammi tayi tace yoh eh mana, "affy tace ay daddynah sankai k'irik'i ake nunawa gidanan, lokacin danayi tafiya ba'a had'aman hakaba, saishi "Ammi tace zaki had'a kanki dashi ne? Affy tace ah ah waceni, dariya Ammi tayi, "daddy yace yauko kinasamun zuwa asibiti, Ammi tace nima tunanin danake kenan,gashi idan yaji bamujeba yadinga bak'in rai, "Affy tace kawai abari idan an d'aukoshi airport saimuje tare, daddy yace toh shikenan, Ammi tace daddy waye zai d'aukoshi ne? Daddy yace driver na tura dan yanzu gab suke da sauka.....
**************************
Tsaye take gaban window ta k'urama window ido, komai take tunani oho, ita kad'ai tasani, rungume yake da hannayenshi ya jingina jikin k'ofa kallonta yake yana murmushi, "dijah taji kamar k'amshin turaren hamza, juyowa tayi da sauri, kawai ta had'a ido da hamza, tana ganinshi, kawai tafara hawaye, "takowa yayi yazo kusa da ita, yace toh miye na kuka? Kobakiso nadawo ba? "Dasauri tace ah ah, yace toh miye na kuka dijatunah, tace bakomai, hankicif yazaro aljihunshi ya goge mata hawayenta, tagaidashi ya amsa, tace tun yaushe kazo nan? Yace nakai minti goma tsaye "tace yana ganka kaikad'ai inasu Affy?, "murmushi yayi yace banamaki alk'awariba idan nadawo wajenki zanfara zuwa tace "Eh, yace toh nan nafara zuwa, murmushi tayi tace nagode, "hamza yace dijatunah, tace naam yace guess what? Binshi tayi da idanu yace ooopz yi hak'uri, "albishirinki tace goro, yace ina shigowa naga likita, yace dama ni yake kira nadawo, "kinsam me? Tace ah ah, yace ansallameki yanzu, murmushi dijah tayi tace nagodema Allah kuma kaima nagodema da taimakona, "nurse ce tashigo d'akin tana murmushi tace yau patient d'ina sai gida, " murmushi dijah tayi, nurse ta rungume dijah tace zanyi kewarki, dijah tace nima haka, 'kayansu nurse ta had'amasu ta d'auka, shiko gagan naku hannun dijah ya rik'e sukayi wajen mota, "suna isa wajen mota nurse tace tau dijah Allah yak'ara sauk'i kinji, sainazo ganinki har gida, dijah tace nagode sosai, "kyauta mai tsoka Hamzariee yama nurse, itako sai godia take, hamza yaja mota sai gida.....
Suna isa gida, horn yama maigadi ya bud'e masu gate, suna shiga, ko ida tsayawa baiyiba, Affy tafito da gudu tayi wurinshi, fad'awa tayi jikinshi tana murna, "shiko dariya yakeyi, da kyar yasamu ta d'ahashi, "hamza yace baki ganin kowa saini ko? , affy tace toh kaidawaye, yace kalli can, gefen da yanuna mata ta kalla, sakin baki tayi, saikuma ta saka ihu, tana dijah oyoyo, hamza yace karki fasa mata kunne, shine yau bakije kinganota ba, amanar kenan,affy tace sowee bruh dama bari mukayi saikadawo, yace aygata ita tazo, dariya sukayi, suka d'unguma sukayi gida, "Ammi najin ihun affy tasan hamza ne yadawo, tare suka sakko Ammi da daddy, sakin baki sukayi da sukaga dijah,"daddy yace nasan ba aikin kowa baneba nakane, murmushi yayi yace toh ay anyi discharging natane, "daddy yace toh madallah, "duk'awa dijah tayi har k'asa tagaidasu Ammi amsawa sukayi fuska sake, da tambayan jikinta, tace dasauk'i
Daddy yace shikenan ya hutar damu muje muci abinci, daining area suka had'u sunacin abinci suna fira, itadai dijah takasa sakewa, bawanda ya kula da haka, "hamza ne kawai ya kula, suna gamacin abinci, daddy yace dijah, idan kinhuta gobe, zaki bamu labarinki, danmu maidama iyayenki ke, "jiki sanyaye dijah tace shikenan daddy, Ammi tace affy kikai dijah d'akin dake kusa da naki akwai komai na buk'ata, dan har d'inkuna nasa ammata, dijah tace Ammi nagode banida abin sakamaku sai adua, Ammi tace bakomai kema d'iyarmu ce, "Affy taja hannun dijah takaita d'aki, sakin baki dijah tayi tana kallon d'akin, cikin ranta tace saikace gidan shugaban k'asa, affy duk ta nuna muta abubuwa da yanda zatayi amfani dasu, "dan da alama bata saniba, Affy tace jekiyi wanka bari naje k'asa, dijah samun wuri tayi tazauna ta buga tagumi, d'akin taga anbud'e tana d'aga kai tayi karo da Hamzariee yana mata murmushi, ga plate d'in abinci, zama yayi yace shine kikak'i cin abinci ko? Dijah tace nafaci, hamza yace baki ciba, saboda naganki, dan haka yanzu zakici, inba hakaba inmaki d'ura, bayanda dijah tayi, haka tazauna hamza yana bata abinci, ita kanta tayi mamakin yanda taci abincin, yanagamawa yabata ruwa, yace toh bari nabarki kihuta kinji dijatunah, d'aga kanta tayi alamar to, kuncinta ya Shafa yace saikin fito gimbiya, dariya tayi, shima dariya yayi, yafita......
www.phirdauceejeebo.com
IG:yar_ficika
Written by
Feedoh Deedoh✍🏻✍🏻
Comments
Post a Comment